An yanke wa mutum biyar zaman gidan yari na wata shida saboda rikicin kwallon ƙafa

Asalin hoton, VLN NIEWS/ANP/AFP
Wata Kotu a Netherland ta yanke wa wasu mutum biyar hukunci saboda hannu da suke da shi a tashin hankalin da ya faru gabani da kuma bayan wani wasan ƙwallo tsakanin Maccabi Tel Aviv da Ajax Amsterdam a watan da ya gabata.
Hukuncin da aka yanke masu ya haɗa da zaman wata shida a gidan yari da kuma aikin taimakon al'umma na tsawon sa'a ɗari.
Wasu ƙarin waɗanda ake zargi za su bayyana gaban kotu cikin kwanaki masu zuwa.
Harin da aka kai wa ƴan Isra'ila magoya bayan ƙwallon ƙafa ya janyo zarge-zargen nuna wa Yahudawa ƙyama.
Sai dai mai gabatar da ƙara ya ce bai kamata a danganta lamarin ga nuna ƙyama ga Yahudawa ba.
Rikicin da aka yi daidai lokacin da ake fuskantar zaman ɗarɗar kan yaƙin Isra'ila a Gaza, ya faru bayan da wasu magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Maccabi suka riƙa rera waƙoƙin adawa da Larabawa tare da ƙona tutar Falasɗinawa.



















