Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibarhim Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye. Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Ba a fara raba kayan agaji a Gaza ba - MDD

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Har zuwa yanzu ba a fara raba kayan agaji Zirin Gaza ba, kamar yadda kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya, Stephane Dujarric ya bayyana.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake murnar fara shigar da kayan agaji yankin na Falasɗinu ta ɓangaren Kerem Shalon, wanda yanki da ke tsakanin kudancin Gaza da Isra'ila.

    "A yau daga cikin wakilanmu sun jira na sa'o'i sosai domin samun lasisin shigar da kayan agaji ta yankin Kerem Shalon domin karɓo abinci masu gina jiki. Amma abin takaicin shi ne ba su kawo mana kayan abincin ba," in ji Dujarric a ganawar Majalisar Ɗinkin Duniya da manema labarai.

    Ya ƙara da cewa, "an shiga da kayan agaji Gaza," amma ya ƙara da cewa wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya sun jira, "amma ba su samu karɓar kayan ba a gidajen ajiyarsu da ma cibiyoyin rabo."

    Tun da farko, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Isra'ila ta amince a shigar da motoci 100 na kayan abinci zuwa Gaza bayan hanawa na mako 11.

  3. Kansar Biden ta jawo tambaya kan rashin lafiyar da ya sha fama a lokacin mulki

    Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Sanarwar Joe Biden cewa yana ɗauke da cutar ƙasan mafitsara ta jawo tambayoyi kan irin yanayin rashin lafiyar da ya sha a zamanin da yake shugabantar Amurka.

    A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ofishin Biden ya ce tsohon shugaban mai shekara 82 yana fama da cutar kansar, wadda ta bazu zuwa ƙasusuwarsa, kuma ba a gano ba a cikin lokaci.

    Wasu likitoci sun bayyana mamakinsu kan yadda cutar ta bazu zuwa ƙasusuwa, amma kuma ba iya a ganowa da wuri ba.

    Wasu kuma suka ce dama kansa tana ya iya bazuwa cikin sauri ba tare da nuna alama ba - sannan wasu suka ce maza da suka haura shekara 70 ba su cika zuwa gwaji ba.

    Shugaba Donald Trump ya ce ya kamata a ce wanda ya gada ya bayyana wa jama'a gaskiyar halin da yake ciki - inda yake nufin cewa an yi rufa-rufa ne game da cutar, duk da bai bayar da dalili ba.

  4. UAE ta ce ba ta alaƙa da harin da aka kai a Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta musanta cewa ta taka rawa a harin da aka kai a farkon wannan watan a garin Port Sudan wanda ta kasance hedikwatar gwamnatin Sudan tun bayan da yaƙi ya ɓarke a ƙasar sama da shekara biyu da suka gabata.

    A ranar Litinin jakadan Sudan a Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ikirarin cewa jiragen yaƙi ne da suka tashi daga sansanonin masarautar suka kai harin.

    Daga nan ne Sudan ta yanke hulɗar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, tana mai cewa masarautar na taimakawa abokan hamayyar sojojin ƙasar, wato dakarun Rapid Support Forces, da makamai na zamani.

  5. Gwamnatin Najeriya za ta sayar da gidaje 753 da aka ƙwato daga Emefiele

    CBN

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na sayar da gidaje guda 753 da ta ƙwato daga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, waɗanda suke cikin kadarorin da Hukumar EFCC ta ƙwato daga hannun masu almundahana da kuɗin ƙasar.

    Ministan gidaje na Najeriya ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata a lokacin da yake karɓar takardun gidajen daga hannun EFCC, kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito.

    A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ma'aikatar, Salisu Haiba ya fitar, ya ce, "ma'aikatar gidaje ta karɓa gidaje 753 da suke Abuja waɗanda Hukumar EFCC ta ƙwato daga tsohon babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele."

    Ministan ma'aikatar, Ahmed Dangiwa, ya yaba wa ƙoƙarin Hukumar EFCC ɗin wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

  6. Ba domin rikici da ɓangaren zartaswa aka zaɓe mu ba - Akpabio

    Godswill Akpabio

    Asalin hoton, Godswill Akpabio

    Shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya ce ba a zaɓe su - ƴan majalisa - ba domin su je su riƙa rigima da ɓangaren zartaswa, inda ya ce aikinsu shi ne yin dokokin da za su ciyar da ƙasar gaba.

    Akpabio ya bayyana haka ne a tsakuren bidiyon shiri na musamman da aka domin bikin cika shekara biyu na gwmanatin Bola Tinubu.

    Da yake magana game da amfanin haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu, ya ce, "idan ka lashe zaɓen majalisa, ko dai ta dattawa ko ta wakilai, waɗanda kake wakilta ba za su ba ka safar hannun dambe ba. Ba dambe muka zo yi ba, mun zo ne domin gudanar da ayyukan da za su ciyar da Najeriya gaba."

    Shugaban majalisar ta nanata cewa akwai alaƙa mai kyau da fahimta tsakanin majalisa da ɓangaren zartaswa a shekara biyu da suke gabata.

    "Idan ka ƙarar da lokacinka wajen rikici da ɓangaren zartaswa, waye zai yi wa Najeriya aikin?" in ji shi.

  7. Zelensky na zargin Rasha da "ƙoƙarin lalata" yarjejeniyar tsagaita wuta

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da "ƙoƙarin yin wasa da hankali domin ci gaba da yaƙin da take yi a Ukraine, kwana ɗaya bayan Donald Trump ya ce nasarar da ake samu dangane da tsagaita wuta ta samu ne sakamakon kiran waya da ya yi da shugaban Rasha Vladimir Putin.

    "Idan Rasha ta ci gaba da sanya sharuɗɗan da ba za a iya cika su ba sannan ta janyo koma baya to dole ne za a samu sakamakon hakan", kamar yadda shugaban Ukraine, Vlodomyr Zalensky ya wallafa a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya ƙara da cewa ƙasarsa a shirye take ta tattauna.

    Shugaba Trump na Amurka dai ya ce tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine za ta fara "cikin gaggawa" bayan magana a waya da ya yi da Zelensky da Putin.

    Putin ya ce a shirye yake ya yi aiki da ƙunshin yarjejeniyar domin cimma sulhu a gaba, sai dai kuma bai yi magana ba dangane da kiraye-kirayen tsagaita wuta na kwana 30.

  8. Isra'ila na rasa goyon bayan ƙasashen duniya sannu a hankali - Jeremy Bowen

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙwararren ɗan jaridar BBC mai rahotanni kan tsaro a faɗin duniya, Jeremy Bowen ya ce alamu na nunce cewa a yanzu ƙimar Isra'ila a idanun ƙawayenta ta zagwanye ko kuma a ce a idanun Faransa da Burtaniya da Canada.

    Sun bayyana kakkausan suka dangane da yaƙin da Isra'ilar ke yi a Gaza.

    Sun ce dole ne Isra'ila ta dakatar da sabon yaƙin da take yi a Gaza wanda firaiminista, Benjamin Netanyahu ya ce sai ya ga bayan Hamas da ceto ragowar mutanen da Hamas ke garkuwa da su sannan kuma ya mayar da ilahirin Gaza ƙrƙashin ikon Isra'ila.

    Sanarwar ƙasashen guda uku ta yi watsi da iƙrarin Netanyahu inda suka nemi a cimma tsagaita wuta. Ƙasashen sun kuma ce suna adawa da faɗaɗa yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, inda suka ƙara da cewa "irin girmar wahalar da ɗan adam ke ciki ba abu ne da za a iya jerewa ba".

    Sun kuma bayyana abin da Netanyahu ya kira amincewa da shigar da abinci kaɗan zuwa Gaza da wanda bai taka kara ya karya ba.

    Sai dai kuma Netanyahu ya mayar da martani inda ya ce "shugabanni a London da Ottawa da Paris na murna da harin da aka kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Okotoba har ma suna fatan a sake kai irin wannan hari."

    Ya kuma tsaya kai da fata cewa za a ƙare yaƙin ne kawai idan Hamas ta saki mutanen da take garkuwa da su, ta ajiye makamai sannan ta amince da shugabanninta sun bar ƙasar tare da tabbatar da cewa Gaza ba ta yin barazana." In ji Netanyahu.

  9. Birtaniya ta gayyaci jakadan Isra'ila don ya amsa tambayoyi

    House of Common

    Asalin hoton, David Lammy,House of Common

    Bayanan hoto, David Lammy, House of Common

    Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ya bayyana matakin jingine batun ciniki tsakanin Birtaniya da Isra'ila, ya kuma nemi jakadan Isra'ila a Birtaniya ya bayyana a gaban Ofishin Lamurran Cikin Gidan ƙasar domin ya amsa tambayoyi game da yaƙin da ƙasarsa ke ci gaba da gwabzawa a Gaza.

    Mista Lammy ya ce ministan da ke lura da lamurran da suka shafi gabas ta tsakiya na Birtaniya, Hamish Falconer, zai sanar da Hotovely cewa, "hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza har na tsawo makonni 11 mugunta ce kuma babu hujjar yin hakan" .

    A cewar sakataren wajen Birtaniyar, " gwamnatin Natanyahu na da manufar korar mazauna Gaza daga gidanjensu zuwa kudancin zirin na Gaza, tare da yanke musu adadin irin kayan agajin da suke buƙata ya kai gare su. " A yanzu muna ci gaba da shiga wani mummunan yanayi game da wannan yaƙi" in ji shi.

    Lammy ya ƙara da cewa yaƙin da ake yi a Gaza ya haifar da naƙasu ga alaƙar da ke tsakanin Birtaniya da Isra'ilan, sannan ya ce gwamnatin Birtaniya za ta sa takunkumi ga mutane uku 'yan Isra'ilan waɗanda ke da hannu wajen tayar da mazauna Gaza daga muhallansu.

    "Hana shiga da kayan agaji, da ci gaba da kai hare-hare a Gaza abubuwa ne da suka raunana alaƙarmu kuma, wajibi ne a dakatar da su da gaggawa," in ji shi.

  10. 'Matsin lamba daga waje ba zai sauya Isra'ila akan manufofinta ba' - Oren Marmorstein

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila, Oren Marmorstein ya mayar da martani akan matakin gwamnatin Birtaniya na dakatar tattaunawar ciniki tsakanin ta da Is'ra'ila.

    A wani bayani da Marmorstein ya wallafa a shafin X ya ce yarjejeniyar kasuwanci maras shinge "ba wani abu da gwamnatin Birtaniya ta tsinana game da shi" kafin sanarwar da David Lammy ya bayar a majalisar dokokin Birtaniya.

    Ya ce idan gwamnatin Birtaniya a neman haifar da koma baya ga tattalin arzikinta "a dalilin ƙin jinin ƙasar Isra'ila da siyasar cikin gida" to wannan ya rage nata idan tana son ta aiwatar da hakan.

    Dangane da bayanan akan takunkuman janye hulɗar kasuwanci da gwamnatin Birtaniya ta ce za ta saka, akan take haƙƙin ɗan adam da Isra'ila ke yi a gaɓar yamma da Kogin Jodan, mai magana da yawun ma'aikatar wajen isra'ilan ya ce babu wata takamaiman hujjar aikata laifin.

    Marmorstein ya kuma ce a yanzu Isra'ila na jimamin "wani mummunan ta'addanci daga Falsɗinu na kasheTzeela Gez lokacin da ta ke hanyar zuwa ɗakin haihuwa a asibiti, wadda daga bisani likitoci suka yi ƙoƙarin ceto jaririn da za ta haifa,"

    "A kan haka, duk wani matsi ba zai sa Isra'ila ta sauya daga hanyar da ta ɗauka domin kare kanta daga maƙiyanta da ke neman ganin sun kassara ta." in ji shi

  11. An ɗaure mutumin da ya shigar da fiye da mutum 3,000 Turai ta haramtacciyar hanya

    ...

    Asalin hoton, NCA

    An ɗaure mutumin ne har na tsawon shekaru 25, wanda masunci ne ɗan asalin ƙasar Masar da ya taimaka wajen yin safarar fiye da 'yan cirani 3,000 a wani ɓangare na yin haramtaccen ciniki da ya kai na dala miliyan 12 ta amfani da kwale-kwale wajen tsallakar da su zuwa Turai.

    A cewar Hukumar da ke Yaƙi da Manyan Laifuka ta Birtaniya (NCA), Ebid ɗan shekara 42 da ke da takardun izinin zama a ƙasar, ya shiga wannan sana'ar tsallaka baƙin haure da 'yan ci rani daga arewacin Afirka zuwa Italiya tsakanin wata Oktoban 2023 zuwa Yunin 2023, inda daga can su kan tsallaka zuwa Birtani.

    Ebid shi ne mutum na farko ɗan Birtaniya da aka yankewa irin wannan hukunci mai alaƙa da safara mutane ta hanyar tsallaka Tekun Miditireniya daga Afirka zuwa ƙasar Italiya.

    Ya isa Birtaniya cikin ɗan ƙaramin kwale-kwale a 2022 bayan ya kwashe shekaru biyar yana zaman kaso a Italiya saboda laifin yin safarar miyagun ƙwayoyi. Daga bisani ya nemi mafaka a Birtaniya duk bai samu karɓuwa ba; abin da ya nuna yana zaune ne ba bisa ƙa'ida ba, duk da ba a kore shi ba. Kuma akwai yuwar za a mayar da shi ƙasarsa ta asali muddin aka same shi da laifi.

    A yanzu haka iyalan Ebid da suka haɗa da matarsa da 'ya'yansa na rayuwa a Birtaniya, inda suke zaune a wani gida da ke yammacin birnin Landa wanda Ofishin da ke lura da lamurran cikin gidan Birtaniya ke ɗaukar nauyi.

    A lokacin da ake saurare ƙararsa da aka shiga a kotun Southwark Crown a ranar Talata, alƙalin kotun ya ce Ebid ya jefa ɗimbin jama'a cikin damuwa "bisa burinsa na na son yin kuɗi ta hanyar safarar bil'adama".

  12. Faɗa ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da RSF a birnin Omdurman

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Faɗa ta ɓarke tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai na RSF a birnin Omdurman da ke gaɓar Kogin Nile, da ke gaban babban birnin ƙasar, Khartoum.

    Rundunar sojin ta ce tana dab da korar dakarun RSF daga babban birnin, Khartoum.

    Tun farkon wannan yaƙi da ya ɗauki sama da shekaru biyu, yankin ya kasance cikin rikici mai tsanani.

    A makonnin baya-bayan nan dai dakarun RSF sun kai jerin hare-hare da jirage marasa matuƙa da dama kan yankunan da ba su ke da iko da su ba, ciki har da birnin Port Sudan, inda gwamnatin da sojoji ke marawa baya ke zaune.

  13. Yadda aka tsinci gawar wani yaro kwana 48 bayan sace shi a Sokoto

    Yaron

    Asalin hoton, Dr. Abubakar Hamza

    Mahaifan wani yaro ɗan kimanin shekaru biyar da aka sace, sannan aka kashe a birnin Sakoto sun yi kira ga hukumomin tsaro na tarayyar Najeriya ƙungiyoyin kare hakkin bil adama, su bi musu kaɗin jinin ɗansu.

    An dai sace yaron mai suna Ayman ne a daren ƙaramar sallah wato 29 da watan Maris a unguwarsu ta CBN Quarters Sokoto, sai bayan kwanaki 48 aka ga gawarsa cikin wani ramin ruwa wato Soakaway, a kusa da gidansu.

    Mahaifin yaron Dakta Abubakar Hamza ya shaida wa BBC cewa an sace yaron ne bayan dawowa daga sallar la'asar, daga suka yi ta nema, sai wani ƙaramin yaro ya ce ai ya gan shi wasu sun saka shi cikin mota sun tafi da shi.

    Ya ce bayan ƴan kwanaki sai wata mai suna Ummu ta ce masa ta son inda Ayman yake, wai an yi garkuwa da saurayin ƙawarta, wanda ya ce an tsare su tare da Ayman a yankin Kamba, ta kuma faɗa musu cewa za ta taimaka wajen dawo da yaron.

    ''To sai dai bayan da ta buƙaci kudi kuma muka ba ta sai maganar ta shirice, matar da riƙa yi mana gobe-gobe, har dai muka sanar wa hukumomi, suka kuma kamata, amma bayan bincike sun ce mana ƙarya take yi ba ta san inda Ayman yake ba'', in ji mahaifin yaron.

    ''Amma abin mamaki kwana biyu da suka wuce sai aka ganshi a cikin ramin ruwa (Soakaway)''.

    Mahaifin yaron ya yi kira ga hukumomi su taimaka wajen bi masa kadin jinin ɗansa.

  14. Shugaban Afirka ta Kudu ya isa Amurka domin ganawa da Trump

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya isa ƙasar Amurka inda zai gana da Shugaban kasar, Donald Trump, da nufin farfado da dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.

    Ramaphosa tare da wasu daga cikin ministocinsa sun isa birnin Washington a daren jiya, kuma ana sa ran za su gana da Shugaba Trump a fadar White House gobe.

    Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin tankiya tsakanin ƙasashen biyu, musamman bayan isar wata rukuni ta farko na fararen fata ‘yan Afrika ta Kudu da suka samu matsayin ’yan gudun hijira a Amurka makon da ya gabata.

  15. Kalli wurin yawon shaƙatawa da mutane ke tururuwan zuwa a arewacin Najeriya

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Mutane da dama kan taso daga garuruwansu domin zuwa Tulo-Tulo da ke jihar Yobe a arewacin Najeriya, tare da abokai ko iyali domin yawon buɗe ido da kuma shaƙatawa.

    Wuri ne mai faɗi kuma buɗaɗɗe, wanda hakan ya sa mutane ke sha'awar zuwa domin hutawa

  16. Rashin cika ƙa'ida ne ya sa aka kori masu neman aikin ɗansanda - Gwamnatin Katsina

    ...

    Asalin hoton, Katsina State Government

    Gwamnatin Jihar Katsina ta ce rashin cika ƙa'ida ne ya sa aka kori ƴan asalin jihar da suka je neman aikin ɗansanda.

    A kwanan ne dai aka samu labarin korar wasu matasa ƴan asalin jihar Katsina su 35 da ke neman aikin ɗansanda bayan kwashe watanni a makarantar horas da ƴansanda da ke Kaduna.

    To sai dai cikin wata sanarwa da sashen kula da ɗaukar ma'aikata da yi musu ƙarin girma ta Jihar ta fitar, ta ce rashin cika ƙa'idar aikin ne ya sa aka kori atasana.

    ''Akwai ƙa'idojin da ba su cika ba da suka haɗa da rashin kai tsayin da ake buƙata, da girman kirji da kuma wasu matsalolin lafiya'', in ji sanarwar.

    Sanarwar ta tabbatar da cewa mutum 126 ne aka sallama baki daya daga makarantar, amma waɗanda suka fito daga jihar Katsina ba su kai 35 ba.

    Sanarwar ta ƙara da cewa sallamar ta shafi ɗaukacin jihohin Najeriya ba wai jihar Katsina kawai ba, saɓanin yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.

  17. 'Har yanzu matatar Fatakwal ba ta fara fitar da man fetur ba'

    ...

    Asalin hoton, NNPC/X

    Masu hada-hadar man fetur a Najeriya na kokawa kan yadda suke samun matsala wajen samun fetur daga matatun gwamnati guda biyu da aka gyara kwanan nan—matatar Fatakwal da na Warri—shekara daya bayan da aka bayyana cewa sun fara aiki.

    Najeriya, wadda ta shafe shekaru tana fama da ƙarancin man fetur, ta kashe kimanin dala biliyan 2.4 tun daga shekara 2021 domin farfaɗo da waɗannan matatun da ke yankin Niger Delta, da nufin dakatar da dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje. Sai dai har yanzu, ba su fara fitar da man fetur ba.

    Kungiyar 'yan kasuwa masu gidajen mai ta Najeriya, PETROAN, ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sama da mambobinta 6,700 har yanzu na dogaro da shigo da mai daga waje da kuma matatar Dangote.

    Bisa bayanan ƙungiyar, har zuwa watan Maris babu wani fetur da aka fara fitarwa daga matatar Fatakwal wadda a da ita ce mafi girma a kasar.

    A cikin wannan watar dai, matatar Dangote ta samar da lita miliyan 20.6 na fetur, yayin da aka shigo da ƙarin lita miliyan 25.19 daga waje—wanda duka ya kai kashi 92 cikin 100 na buƙatar lita miliyan 50 da ake bukata kullum a Najeriya.

    Matatar Fatakwal dai na ci gaba da tace danyen mai don samar da dizel.

    Kamfanin NNPC, wanda ke gudanar da matatun Fatakwal da Warri, bai mayar da martani ba kan dalilin da yasa ba a fara fitar da man fetur ba

    Kungiyar PETROAN ta buƙaci a bayyana gaskiya game da halin da matatun ke ciki, tana mai cewa: “'Yan Najeriya na son sanin taƙamaiman ranar da za a kammala aikin gyaran matatun.”

  18. 'Hare-haren Isra'ila ya hallaka aƙalla mutum 38 a Gaza cikin rabin sa’a'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Akalla Falasdinawa 38 ne suka rasa rayukansu a wani jerin hare-haren jiragen yaƙin Isra’ila da aka kai a sassa daban-daban na Gaza cikin rabin sa’a da dare, in ji likitocin Falasɗinawa.

    Rahotanni daga hukumar agajin gaggawa da ke ƙarkashin Hamas sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a wurare da dama, ciki har da wata makaranta a gabashin birnin Gaza, da kuma wani tsohon gidan mai a sansanin ’yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, inda iyalai da dama ke neman mafaka.

    Hukumar ta ƙara da cewa tawagar ceto na fuskantar matsaloli wajen kai ɗauki ga waɗanda suka jikkata saboda ƙarancin kayan aiki da kuma tsananin harin.

    Wannan hari ya biyo bayan umarnin kwashe jama’a gaba ɗaya da Isra’ila ta bayar a wani shiri na kai “mummunan hari da ba a taɓa gani ba,” a cewarta.

    A cewar wasu masu rajin kare haƙƙin dan Adam a birnin Gaza, mutum 10 ne suka mutu a lokacin da wani hari da jirgi a makarantar Musa bin Nusayr inda ɗaruruwan ’yan gudun hijira ke fakewa.

    A tsakiyar Gaza, rahotanni sun ce mutum 15 sun mutu a wani hari da aka kai kan tantuna a wani tsohon gidan mai da ke sansanin Nuseirat.

  19. Ambaliya ta malale birnin Bengaluru dake ƙasar Indiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ambaliyar ruwa ta malale wasu sassa na birnin Bengaluru da ke kudancin Indiya, wanda aka fi sani da “cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire” na kasar bayan ruwan sama mai karfi da ya fara zuba tun ranar Lahadi har zuwa Litinin.

    Hukumomi sun sanya birnin cikin matakin shirin gaggawa, yayin da ake sa ran ƙarin ruwan sama na kafin damina zai sauka a ranar Talata, sakamakon haɗuwar guguwa a saman Tekun Andaman.

    Mutum uku, ciki har da wani yaro ɗan shekara 12, sun mutu sakamakon ambaliyar ruwan a ranar Litinin.

    Bengaluru na dauke da manyan kamfanonin fasaha na duniya, inda da dama daga cikinsu suka umurci ma’aikatansu da su yi aiki daga gida saboda ambaliya ta toshe hanyoyi.

    Yawancin sassan birnin sun fara ambaliya tun daga ranar Lahadi, kuma an ruwaito cewa an samu ruwan sama mai yawa da ya kai milimita 100 a ranar Litinin, wanda ya kafa tarihin mafi yawan ruwa da aka taba samu tun 2011.

    Wannan lamari “abun mamaki ne” ga Bengaluru, a cewar CS Patil, darektan sashen yanayi na yankin yayin da yake magana da kafafen yaɗa labarai.

    Baya ga ambaliya da kuma cunkoson ababen hawa da ke kawo cikas ga rayuwar yau da kullum, ruwan sama mai karfi ya haddasa lalacewar kadarori da dama.

  20. Birtaniya da Faransa sun yi barazanar ɗaukar mataki kan Isra'ila game da Gaza

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya soki shugabannin Faransa da Birtaniya da Canada, bayan sun nemi ya kawo ƙarshen sabbin hare-haren da sojijinsa suka sabunta a Gaza.

    Idan kuma ba haka ba, shugabannin uku sun yi barazanar ɗaukan ƙwaƙwaran matakai muddin Isra'ila ta cigaba da nuna kunnen kashi da ƙin ɗage takunkuman hana shigar da kayan agaji Gaza.

    Netanyahu ya ce waɗannan kalamai na su tamkar nuna goyon-baya ne ga Hamas.

    A jiya Litinnin ne Isra'ila ta sassauta haramcin shigar da kayayyaki a Gaza, sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya na cewa hakan da tayi bai wadatar ba.

    Ana dai cigaba da luguden bama-bamai babu kakautawa a sassan Gaza.