Ina bindigogin ƴansandan Najeriya fiye da 178,000 da suka ɓace?

Kayode Egbetokun

Asalin hoton, NPF

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wani rahoton da babban mai binciken kuɗi na Najeriya ya bai wa kwmaitin majalisar dattawa mai binciken lalitar gwamnati, ya fito da wani abu mai ban tsoro da ya kwashe shekaru na faruwa a aikin ƴansandan ƙasar.

Rahoton na 2019 wanda Samuel Godwin ya gabatar a madadin babban mai binciken kuɗin ƙasar Shaaka Chira ya nuna cewa bindigogi 178,459 mafi yawanci ƙirar AK-47 sun ɓace daga ofisoshin ƴansanda a faɗin ƙasar.

"Tun daga watan Disamban 2018, an rasa bindigogi 178,459 da suka haɗa da ƙirar AK-47 guda 88,078. Haka kuma ya zuwa watan Janairun 2020, aƙalla bindigogin iri daban-daban da suka haɗa da ƙanana na hannu guda 3,907 sun ɓata", in ji rahoton.

Abu ne mai tayar da hankali - Kabiru Adamu

Kabiru Adamu

Asalin hoton, Beacon Consulting

Bayanan hoto, Malam Kabiru Adamu ya ce binciken da kamfaninsa ke yi ya tabbatar da cewa makaman ne a hannun bata-gari.

Malam Kabiru Adamu mai bincike a harkokin tsaro a yankin Sahel da Sahara ya ce al'amarin yana da ban tsaro bisa la'akari da yawan makaman da kuma halin da Najeriya ke ciki ta fuskar tsaro.

"Idan har wata hukumar gwamnati za ta fitar da irin wannan bayanai to lallai abin tsoro ne da ya kamata ace gwamnati gabaɗaya wato ɓangaren zartarwa da majalisa da shari'a su tashi tsaye a bi diddigin inda waɗannan makamai suka shiga.

Ba wannan ne karon farko da ofishin babban mai binciken kuɗi na ƙasa ke fitar da irin wannan rahoton ba. Sannan ya yi tambayoyi har guda takwas da ya kamata rundunar ƴansandan Najeriya ta ba da amsarsu." In ji Malam Kabiru Adamu.

Hannun wa bindigogin ke shiga?

Wannan tambayar ce ƴan Najeriya ke ta yi tun bayan ɓullar wannan batu ranar Laraba, inda suke son sanin ina makaman masu yawa haka suke shiga?

Malam Kabiru Adamu ya ce wurin da makaman suke shiga abu ne a fili musamman bisa la'akari da irin yadda makamai suka yi yawa a hannun ƴan bindiga.

"Lallai suna faɗa wa hannun ɓarayi da ƴanbindiga da ma ƴan ta'adda. Binciken da muke yi duk suna nuna hakan. Akwai shaidu masu ƙwari da ke nuna waɗannan makaman na zuwa hannun ɓata-gari ne.

Illar hakan kuma ita ce haifar da babbar matsalar kasa magance tsaron da ƙasar ke fama da shi saboda mutumin da zai magance matsalar tsaro ya miƙa wa ƴanta'adda makaman nasa. Ka ga ai akwai matsala kenan." In ji Kabiru Adamu.

Ko za a iya mayar da makaman rumbun ƴansanda?

Makaman sun ɓata daga 2018 zuwa 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malam Kabiru Adamu ya ce abu ne mai yiwuwa amma sai idan hukumomin da abin ya shafa za su aiwatar da hakan bisa gaskiya da tsari.

:Idan aka bi hanyoyin da suka dace to za a iya mayar da makaman rumbun ajiyarsu tunda kowanne makami yana da lamba lokacin da aka sayo shi saboda haka ana iya bibiyar su a gano inda suke a kuma mayar da su tunda ana yin hakan a sauran sassan duniya."

Sai dai kuma masanin tsaron ya ce hukumar da za ta iya tabbatar da tattaro makaman da ke hannun jama'a ba ta cin gashin kanta a Najeriya.

"Ana ganin cewa cibiyar ke saka ido kan bazuwar makamai da ke ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro tana da rauni wajen aiwatar da aikinta ba tare da an yi mata shisshiga ba.

Ya kamata ace hukuma ce mai cin gashin kanta kamar shawarar da Ecowas ta bayar wajen kafa irin wannan hukuma, maimakon cibiya a ƙarƙashin wani ofishi." In ji Kabiru Adamu.

Daga ƙarshe masanin ya yi kira ga majalisar dokoki ta yi duba dangane da dokokin da suka kafa wannan cibiya mai saka ido kan bazuwar makamai a ƙasa domin ba ta damar aiwatar da aikace-aikacenta ba tare da katsalandan ba.

Martanin ƴansanda

Kwamitin ya nemi amsar tambyoyin da wannan rahoto na babban mai bincike na Najeriya ya bankaɗo, sai dai kuma babban sifeto na ƴansandan ƙasar Kayode Egbetokun bai samu halartar zaman ba sai wakilci da ya aika.

Yayin da yake jawabi a madadin babban sifeton ƴandan ƙasar, mataimakin sifeton ƴansandan ƙasar, AIG Abdul Sulaiman ya ce wasu daga cikin bindigogin an sace su ne a lokacin fashi da hare-haren da ake kai wa ƴansanda.

Ya kuma buƙaci kwamitin majalisar dattawan ya ba shi ƙarin lokaci, domin gabatar da cikakken rahoto kan bindigogin da ba a san inda suke ba.

"A fahimtata, babu wata bindiga da ba za a iya faɗin abin da ya same ta ba. Ina roƙon kwamitin da ya ba mu lokaci, za mu miƙa cikakken rahot kan al'amarin," in ji AIG Sulaiman.

Kwamitin na majalisar dattawa ya sake bai wa sifeto janar na Najeriya da ya bayyana gabansa a ranar Litinin 17 ga watan Fabrairu tare da cikakken rahoto kan bindigogin da ake nema da kuma na wani zargin badaƙalar kuɗaɗe da kwamitin ya yi wa rundunar ƴansandan.