Amurkawa na janye goyon bayan da suka saba bai wa Isra'ila

Hoton Donald Trump da Benjamin Netanyahu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alaƙar da ke tsakanin Amurka da Isra'ila ta fara samun tangarɗa ne tun bayan harin Hamas na 7 ga Oktoban 2023 da martanin da Isra'ila ta mayar.
    • Marubuci, Tom Bateman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, US State Department correspondent
    • Marubuci, Luke Mintz
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Marubuci, Giles Edwards
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Cikin gaggawa na fice daga ɗakin ganawa da manema labarai zuwa inda muka ajiye na'urar ɗaukar hoto domin fara aika bayanan kai-tsaye zuwa ɗakin gabatar da shirye-shiryenmu.

Jim kaɗan sai mai gabatar da shirye-shiryen ke tambaya ta game da wata magana da aka ji daga Shugaban Amurka Donald Trump.

Sai na ce lallai an ɗan fara samun koma-baya a matsayar Amurka kan rikicin Isra'ila da mutanen yankin Falasɗinu.

A watan Febrairun bana ne Trump ya gana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda shugaban na Amurka ya lashi takobin karɓe iko da Zirin Gaza.

Jawabin Trump sun ja hankalin duniya, musamman ganin yadda aka fara samun raguwar goyon baya da Isra'ila, wanda a baya ake bayyanawa da "goyon bayan duk wahala duk rintsi."

An fara jin tsakanin ƙasashen biyu ne tun bayan harin Hamas na 7 ga Oktoban 2023 da martanin da Isra'ila ta mayar a Gaza.

A yaƙin, gwamnatin Joe Biden ta tallafa wa Isra'ila da makaman da adadinsu ya kai dala biliyan 18, kimanin fam biliyan 13.5, wanda har sai da wasu ƴan Amurka suka gudanar da zanga-zangar rashin amincewa.

Na halarci zanga-zangar da wasu suka riƙa kiran Joe Biden da "Joe mai kisan kiyashi" duk da musanta zargin.

A lokacin Trump ya bayyana zanga-zangar da rashin hankali, sannan yanzu gwamnatinsa na yunƙurin korar ɗaruruwan ɗalibai baƙi da ake zargi da goyon bayan Hamas, matakin da wasu suke ƙalubalanta a kotu.

Ɗaya daga cikin na hannun Biden musamman a batun alaƙarsa da Isra'ila har yanzu yana cigaba da ba matakan da suka ɗauka kariya.

"Tun da farko na fahimci cewa matakan za su samar da ra'ayoyi mabambanta tsakanin Larabawa ƴan Amurka da waɗanda ba Larabawa da Yahudawa ƴan Amurka," in ji Sullivan, tsohon mai ba Biden shawara kan tsaro.

Ya ƙara da cewa Amurka ta goyi bayan Isra'ila da duk abin da za ta iya bayan harin na 7 ga Oktoba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai ƙididdiga na nuna cewa goyon bayan da Amurkawa ke bai wa Isra'ila na raguwa sosai.

Wata ƙididdiga ta Gallup da aka yi a watan Maris ta gano cewa kashi 46 kawai na Amurka suke goyon bayan Isra'ila, wanda shi ne mafi ƙaranci a shekara 25 da ake fitar da ƙididdigar ta Gallup duk shekara.

Haka kuma kashi 33 sun bayyana cewa suna tausayawa Falasɗinawa - wanda shi ne mafi yawa a tarihin ƙididdigar. Haka kuma wasu ƙididdigar sun samar da sakamako irin wannan.

Ƙididdiga, duk da cewa suna nasu naƙasun, suna nuna yadda ƴan jam'iyyar Democrast da matasa suke sauya ra'ayi, duk ba su kaɗai ba ne. A tsakanin 2022 zuwa 2025, cibiyar binciken Pew Research ta gano ƴan jam'iyyar Republican da ba sa jin daɗin abin da Isra'ila ke yi ya ƙaru daga kashi 27 zuwa 37.

Tun a watan Mayun 1948 ne Amurka take zaman babbar ƙawar Isra'ila. Duk da cewa Amurka za ta cigaba da zama ƙawar Isra'ila, wannan sauyin ra'ayin yana alamta wasu abubuwa, musamman tambayar da wasu ke yi ko zai yi tasiri a fadar shugaban ƙasar.

Ofishin gwamnatin Amurka

Wasu na ganin alaƙar da ke tsakanin Amurka da Isra'ila dawwamammiya ce.

A farkon shekarar 1984, shugaban Amurka na lokacin Harry S Truman ya shiga tasku domin ɗaukar mataki kan yankin Falasɗinu. A lokacin ana gwabzawa ne tsakanin Larabawan yankin da Yahudawa bayan mulkin mallakan Burtaniya na kusan shekara 30. A lokacin Truman ya yi matuƙar tausayawa Yahudawan da suka tsira daga yaƙin kisan kiyashin Yahudawa a Turai, waɗanda suka tare a sansanonin gudun hijira a ƙasashen Turai.

Shugaban Amurka ya lashi takobin cewa ƙasarsa za ta karɓe iko da Zirin Gaza

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka ya lashi takobin cewa ƙasarsa za ta karɓe iko da Zirin Gaza

A lokacin gwamnatin Truman ta shiga ruɗani kan makomar Yahudawa. A lokacin hukumar leƙen asirin ƙasar ta gargaɗi shugaban da amincewa da ƙasar Isra'ila, domin tana fargabar hakan zai haifar da zubar da jini tsakaninta da ƙasashen Larabawa.

Kwana biyu kafin Birtaniya ta fice daga yankin Falasɗinu, sai aka yi zazzafar muhawara a ofishin gwamnatin Amurka.

Hadimin Truman Clarck Clifford ya nuna goyon bayan amincewa da ƙasar Isra'ila, a ɗaya ɓangaren kuma sakataren harkokin wajen ƙasar na lokacin George Marshall yana cikin waɗanda ba su amince ba.

Tun a shekarar 1984 Amurka take goyon bayan Isra'ila bayan ta zama ƙasa ta farko da ta amince da ƙafa sabuwar ƙasar Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun a shekarar 1984 Amurka take goyon bayan Isra'ila bayan ta zama ƙasa ta farko da ta amince da ƙafa sabuwar ƙasar Isra'ila

Amma duk muhawarar da aka yi, a ƙarshe sai da Truman ya amince da kafa sabuwar ƙasar bayan Firaministan ƙasar na farko David Ben-Gurion ya sanar da kafa ƙasar.

Masanin tarihi Rashid Khalidi, wanda ɗan yankin Falasɗinu amma haifaffen New York, wanda yake cikin waɗanda Turawan Birtaniya suka fatattaka daga Jerusalem a shekarun 1930, ya ce alaƙar da ke tsakanin Amurka da Isra'ila ɗaɗaɗɗiya ce.

Shugaban Amurka Harry S. Truman sai da amince da kafa ƙasar Isra'ila bayan muhawarar da aka riƙa yi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Harry S. Truman ya amince da kafa ƙasar Isra'ila bayan muhawarar da aka riƙa yi
Tsohon firaministan Isra'ila PM Ehud Olmert ya ce yaƙin 1967 ne ya buɗe sabuwar ƙofar gyara alaƙa tsakanin Amurka da Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon Firaministan Isra'ila Ehud Olmert ya ce yaƙin 1967 ne ya buɗe sabuwar ƙofar gyara alaƙa tsakanin Amurka da Isra'ila

Ehud Olmert, wanda a lokacin ɗan fafutika ne, wanda daga bisani ya zama firaministan ƙasar ya ce yaƙin 1967 ne ya buɗe sabuwar ƙofar gyara alaƙa tsakanin Amurka da Isra'ila da ake gani har yanzu.

A yaƙin ne Isra'ila ta samu galaba a kan maƙwabtanta Larabawa a kwana shida, har ta faɗaɗa ƙasarta, sannan ta ƙaddamar da mamaye yankunan gaɓar yamma da tekun Jordan da Gaza.

Ko alaƙar na samun koma-baya?

A yanzu dai yadda ra'ayoyin mutane suka fara sauyawa bai sa ƙasar ta ɗauki wani sabon mataki ba. A daidai lokacin da wasu ƴan ƙasar suke juya wa Isra'ilar baya, wasu manyan ƴan siyasar na ci gaba da goyon bayanta.

Sai dai wasu na tunanin idan aka ci gaba da samun sauyin ra'ayoyin nan daga ƴan ƙasar, dole ƙasar ta rage wasu abubuwan.

An ga irin haka har a Isra'ila, inda wani tsohon janar na soja Tamir Hayman da ya taɓa jagorantar sashen tattara bayanan sirrin sojin ƙasar ya yi gargaɗin za a iya samun saɓani a alaƙar da ke tsakanin ƙasar da Amurka.

Jake Sullivan ya ce har yanzu yana tababar ko akwai wani abu da gwamnatin Biden za ta iya yi domin hana aukuwar harin 7 ga Oktoba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jake Sullivan ya ce har yanzu yana tababar ko akwai wani abu da gwamnatin Biden za ta iya yi domin hana aukuwar harin 7 ga Oktoba

A watan Maris na bana, cibiyar nazarin tsaro ta Institute for National Security da Hayman ke jagoranta ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa canjin ra'ayoyin Amurkawa game da Isra'ila ya fara yawa.

Dennis Ross wanda yake cikin waɗanda suka jagoranci yarjejeniyar Oslo da shugaban Amurka Bill Clinton ya ce dambarwar siyasa na cikin abubuwan da suka jawo ƙaruwar sauyin ra'ayi game da goyon bayan Isra'ila a Amurka.

"Ƴan Democrats ba sa son Trump," in ji Ross.

Sai dai ya ce yana tunanin Amurka za ta cigaba da goyon bayan Isra'ila da makama da harkokin diflomasiyya.