KAI TSAYE, Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni game da jana’izar Khamenei da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/07/2026

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. 'Amurka ta soke ganawa da Netanyahu kan sayar wa Turkiyya jiragen yaƙi'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta soke wata ganawa da aka shirya tsakanin Sakataren Tsaro Pete Hegseth da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan batun yiwuwar sayar wa Turkiyya jiragen yaƙin F-35 kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito.

    Netanyahu ya nuna adawarsa ga shirin, yana mai cewa zai iya sauya daidaiton ƙarfin soja a Gabas ta Tsakiya.

    Duk da haka, Shugaba Donald Trump ya nuna goyon baya ga sassauta takunkumi kan Turkiyya da kuma yiwuwar sayar mata da jiragen.

    Wannan mataki na iya fuskantar ƙalubale daga Majalisar Dokokin Amurka da kuma Isra'ila, wadda ke ganin sayar wa Turkiyya irin waɗannan jirage zai iya zama barazana ga rinjayenta na soja a yankin.

    Sai dai ana sa ran Hegseth zai gana da Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz, inda batun Iran zai kasance cikin abubuwan da za su tattauna.

  2. Iran ta gargaɗi ƙasashen Tekun Fasha kan ba da haɗin kai wajen kai mata hari

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Iran ta yi gargaɗi ga ƙasashen yankin Tekun Fasha da kada su bari a yi amfani da ƙasashensu ko kayayyakin sojinsu wajen kai hari a kanta, tana mai cewa duk wata haɗin kai da Amurka, Iran za ta ɗauke shi a ,matsayin aikata laifi.

    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce Amurka ta kai hari kan wasu cibiyoyin sa ido da leƙen asiri da ke tekun kudancin Iran, abin da ta bayyana a matsayin karya yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi.

    Iran ta kuma zargi Amurka da alhakin lalata wasu muhimman sassan yarjejeniyar, tana mai cewa ci gaba da hare-haren Isra’ila a Lebanon da shiga cikin lamarin mahigar Hormuz zai sa yarjejeniayar ta rasa tasiri.

    A ƙarshe, Iran ta yi barazanar cewa dakarunta za su kai farmaki ga duk wata ƙasa ko wurin da ta bari a yi amfani da ita wajen kai mata hare-hare.

  3. Farashin mai ya tashi bayan Trump ya rushe yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ƙaru da sama da kashi biyar cikin 100 ranar Laraba, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe.

    Bayan kalaman Trump, farashin ɗanyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin kasuwar mai ta duniya, ya tashi zuwa dala 78.09 kan kowace ganga.

    Rahotanni sun nuna cewa masu zuba jari na sa ido sosai kan yadda rikicin tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara taɓarɓarewa.

    Tun kafin wannan sanarwa, farashin mai ya fara nuna alamun tashin gwauron zabi sakamakon musayar hare-haren da Amurka da Iran suka yi wa juna, musamman bayan hare-haren da aka kai kan tankokin dakon mai a mashigar Hormuz.

    Masana tattalin arziki na gargaɗin cewa idan rikicin ya ci gaba da tsananta, hakan na iya ƙara dagula kasuwannin makamashi na duniya tare da haifar da ƙarin hauhawar farashin mai a kwanaki masu zuwa.

  4. Tsagaita wuta tsakaninmu da Iran ta rushe - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe bayan sabbin hare-haren da ɓangarorin biyu suka kai wa juna.

    Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a gefen taron ƙasashen NATO da aka gudanar a Ankara ranar Laraba.

    Ya ƙara da cewa ba ya son ci gaba da mu'amala da Iran, yana mai bayyana tattaunawa da ƙasar a matsayin "ɓata lokaci."

    Trump ya kuma yi kalamai masu zafi kan shugabannin Iran, yana mai cewa ba ya ganin wata fa'ida a ci gaba da yin hulɗa da su.

    Kalaman na Trump na zuwa ne bayan Iran da Amurka sun yi musayar hare-hare tare da zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a baya, lamarin da ya sake ƙara tayar da hankalin rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

  5. Yau za a kai gawar Khamenei Karbala a Iraq domin bankwana da ita

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ne za a kai gawar tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, zuwa birnin Karbala da ke ƙasar Iraq domin ba jama'a damar yi masa bankwana na ƙarshe a wani ɓangare na jerin bukukuwan jana'izarsa.

    Ana gudanar da jana'izar Khamenei ne bayan shafe kwanaki ana addu'o'i da jerin gwanon bankwana a biranen Iran da dama, ciki har da Tehran da Qom.

    Hukumomin Iran sun ce dubban mutane ne suka halarci bukukuwan domin nuna alhini da girmamawa ga marigayin.

    Bayan isarta Karbala, ana sa ran masu makoki daga Iraq da sauran ƙasashe za su hallara domin yi wa gawar bankwana.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Karbala na da muhimmanci matuƙa ga mabiya Shi'a, kasancewar tana ɗaya daga cikin wuraren addini mafi tsarki a gare su.

    Kammala wannan ziyara a Iraq na daga cikin shirye-shiryen jana'izar da aka tsara kafin a kai gawar zuwa Mashhad, mahaifar Khamenei, inda ake sa ran za a binne shi.

    A gobe ne ake sa ran za a kammala janai'zar marigayin.

  6. Yadda aka yi cushen naira biliyan 8 a kasafin kuɗin ma'aikatar Almajirai

    Bayanan bidiyo, Shugaban hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta
  7. China ta soki Iran da Amurka kan sake tayar da rikici

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar China ta soki Iran da Amurka kan abin da ta bayyana a matsayin sake tayar da rikici tsakanin ɓangarorin biyu bayan musayar hare-haren da suka yi.

    A ranar Laraba, Beijing ta bayyana damuwarta kan ci gaba da tashin hankalin, tana mai cewa hakan na iya ƙara dagula al'amura a yankin.

    China ta yi kira ga Iran da Amurka da su kauce wa matakan da za su ƙara rura wutar rikici.

    Haka kuma ta buƙaci ɓangarorin biyu su warware saɓanin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya maimakon amfani da ƙarfin soja.

  8. Ba za mu taɓa miƙa wuya ba - Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa miƙa wuya ba sa’o’i bayan musayar hare-hare tsakanin Iran da Amurka.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, Qalibaf ya ce: “Mu ba mutanen da za su ja da baya ko mu mika wuya ba ne.” Ya kuma shaida wa Amurka cewa lokacin nuna ƙarfin iko da matsin lamba ya wuce, yana mai cewa ba za ta cimma abin da take so ta wannan hanyar ba.

    Shugaban majalisar ya zargi Amurka da karya wasu muhimman yarjejeniyoyi da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu, yana mai cewa hare-haren da aka kai a yankunan kudancin Iran na daga cikin matakan da suka saɓa wa yarjejeniyar da aka cimma.

    Qalibaf ya kuma ce barazanar ci gaba da kai hare-haren soja, dawo da takunkumin mai, da kuma ci gaba da hare-haren Isra’ila a Lebanon na cikin abubuwan da suka saɓa wa yarjejeniyar.

  9. Iran ta ce ta kai hare-hare 85 kan sansanonin sojin Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kai hare-hare 85 kan wuraren sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin martani ga hare-haren da ta ce rundunar Amurka ta CENTCOM ta kai kan wasu wurare a kudancin Iran.

    A wata sanarwa da ta fitar a ranar 8 ga Yuli, rundunar ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta tare da kai hare-hare ta sama kan wasu sansanonin gaɓar teku da wuraren fararen hula a lardunan Hormozgan da Mahshahr.

    IRGC ta ce matakin na Amurka wani yunƙuri ne na karkatar da hankalin jama'a daga wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a Iran da maƙwabciyarta Iraki.

    Sanarwar ta kuma ce sojojin ruwa da na sama na rundunar sun gudanar da hare-hare ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan muhimman cibiyoyin sojin Amurka a Bahrain da Kuwait.

    Bugu da ƙari, IRGC ta ce ta harbo wani jirgin leƙen asirin Amurka kirar MQ-9.

    Wannan sabon rikici ya ƙara tsananta tashin hankalin da ke tsakanin Iran da Amurka.

  10. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da wannan safiya ta ranar Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai kan jana'izar Ali Khamenei da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.