Ko sabon jagoran addinin Iran zai halarci jana'izar mahaifinsa?

Asalin hoton, Tasnim News Agency
Yayin da ake shirye-shiryen jana'izar tsohon Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, duniya ta zura idon domin ganin ko wanda ya maye gurbinsa, wato sabon jagoran ƙasar zai halarci jana'izar.
Tun bayan da aka zaɓi sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei bai fito a bainar jama'a ba.
A watan Maris ne Majalisar ƙwararru ta ƙasar ta zaɓe shi a matsayin sabon jagoran addini na ƙasar, wanda zai gaji mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei, da aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila cikin watan Fabrairu.
A rana Asabar ne za a fara hidimar jana'izar Ayatollah Khamenei a birane biyar na ƙasashen Iran da Iraqi, inda ake sa ran miliyoyin mutane za su halarta.
Tun da farko an jinkirta hidindimun jana'izar ne saboda yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra'ila da kuma Iran.
Saɓanin mahaifinsa, Mojtaba mai shekara 56 ba fitaccen ba ne a ƙasar.

Asalin hoton, EPA
Bai taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba, kuma bai taɓa yin wani jawabi na ƙasa ko hira da wata kafar yaɗa labarai ba, kuma ko hutuna da bidiyonsa da ake da shi ba su da yawa.
Amma an kwashe shekaru ana yaɗa iƙirarin cewa yana da babban tasiri a tafiyar da Iran a bayan fage.
Musayar saƙonnin sirri tsakanin jami'an diflomasiyyar Amurka da WikiLeaks ta wallafa a ƙarshen shekarun 2000 sun bayyana shi a matsayin "mai iko da tasiri a bayan fage", wanda mutane da dama ke kallonsa a matsayin "gogagge kuma mai ƙarfi" a cikin gwamnatin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
Wane ne Mojtaba Khamenei?

Asalin hoton, West Asia News Agency via Reuters
An haifi Mojtaba ne ranar 8 ga watan Satumban 1969 a garin Mashhad, kuma shi ne na biyu a cikin ƴaƴan Ali Khamenei shida.
Ya yi karatunsa na sakandire a makarantar addini ta Alavi a birnin Tehran.
Lokacin da ya kai shekara 17, Mojtaba ya shiga aikin soja na wani ɗan lokaci, sa'ilin yaƙin Iran da Iraqi, kamar yadda kafafen yaɗa labaran Iran suka ruwaito.
A shekarar 1999, Mojtaba ya tafi Qom, birnin da mabiya Shi'a ke ɗauka a matsayin mai tsarki kuma cibiyar mabiyan.
An bayyana cewa sai da ya je wannan birni ne ya fara sanya tufafin malunta.
Ya shiga siyasa?
An fara jin suna Mojtaba ne a zaɓen 2005 na shugaban ƙasar Iran, wanda Mahmoud Ahmadinejad mai ra'ayin mazan jiya ya lashe.
Bayan nasarar ne, Mehdi Karroubi ya rubuta wasiƙa zuwa ga Khamenei, inda ya zargi Mojtaba da katsalanda a zaɓen ta hanyar amfani da dakarun juyin juya-hali da dakarun Basij, waɗanda suka riƙa raba kuɗi ga masu zaɓe domin taimakon Ahmadinejad.
Bayan shekara huɗu, Mojtaba ya sake fuskantar wani zargin, inda sake lashe zaɓen Ahmadinejad ya haifar da zanga-zanga a ƙasar da ake kira da gwagwarmayar Green Movement.
Mostafa Tajzadeh, wanda mataimakin ministan harkokin cikin gida ne a lokacin ya bayyana sakamakon zaɓen a matsayin "juyin mulkin zaɓe." An ɗaure shi shekara bakwai saboda wannan, wanda kuma ya alaƙanta da "umarnin Mojtaba Khamenei".

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma an yi wa wasu masu sauƙin ra'ayi guda biyu Mir-Hossein Mousavi da Mehdi Karoubi ɗaurin talala bayan zaɓen. A watan Fabrairun 2012, Mojtaba ya gana da Mousavi, inda ya buƙace shi da ya haƙura, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.
Masana suna tunanin Mojtaba zai ɗaura daga inda mahaifinsa ya tsaya na ɗaukar matakai tsaurara, wasu ma suna ganin mutum da ya rasa mahaifinsa da mahaifiyarsa da matarsa a hare-haren Amurka da Isra'ila, zai fi zafin rai da ƙin amincewa da ƙasashen yamma.
Amma zai fuskanci ƙalubalen tabbatar da wanzuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma bayyana wa mutane cewa zai iya aikin, musamman fitar da ƙasar daga matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki da siyasa.











