Liverpool ta nace wa Rodrygo, Xhaka zai koma Sunderland

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗanwasan gaba na Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24, na cikin zaɓin Liverpool domin maye gurbin Luis Diaz idan har ɗanwasan mai shekara 28 na Colombia ya bar Anfield. (Florian Plettenberg)

Ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, na son a biya shi fam 300,000 a mako kafin sabunta yarjejeniya a Newcastle. (Talksport)

Granit Xhaka ya amince da yarjejeniya da Sunderland, inda kungiyar ke tattaunawa da Bayer Leverkusen kan cinikin ɗanwasan na tsakiya mai shekara 32 ɗan ƙasar Switzerland (Times - subscription required)

Brentford ta yi watsi da tayin fam miliyan 30 da Newcastle ta yi kan ɗanwasan gaba na DR Congo mai shekara 28 Yoane Wissa. (Tbrfootball)

Atalanta da Lazio na hamayya kan ɗanwasan Manchester United da Denmark mai shekara 22- Rasmus Hojlund. (Footmercato - in French)

Atletico Madrid ta fara tattaunawa da Chelsea kan yarjejeniyar Renato Veiga, inda Chelsea ke neman fam miliyan 35 ga ɗanwasan na Portugal. (Fabrizio Romano)

Everton na son ɗanwasan Bayern Munich da Morocco mai shekara 19 Adam Aznou. (Athletic - subscription required)

Manchester United na sa ido kan ɗanwasan Angers da Mali ɗan ƙasa da shekara 20 Dan Sinate. (Sun)

Everton na son ɗanwasan gaba na Atletico Madrid da Brazil Samuel Lino. (AS - in Spanish)