Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye daga 19-25/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku sharhi da bayanan wasanni a faɗin duniya daga Asabar 19 - 25 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

  • Arsenata kusan kammala sayen ɗan wasan Sporting, Viktor Gyokeres
  • Rashford na shirin buga wa Barcelona wasannin sada zumunta daga Man Utd
  • Dan wasan Valencia, Mosquera ya haɗu da Arsenal a Singapore inda Gunners ke fatan kammala cinikinsa
  • Liverpool ta nace wa Rodrygo, Xhaka zai koma Sunderland
  • Za a auna koshin lafiyar Ekitike, domin kammala cinikin da Liverpool ta amince fam miliyan 69 daga Eintracht Frankfurt
  • Ɗan ƙwallon Brighton, Evan Ferguson zai buga wa Roma wasannin aro
  • Za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Isak zai ci gaba da taka leda a Newcastle United - Howe

    Kociyan Newcastle United, Eddie Howe ya amince Alexander Isak ya ci gaba da hutu, kuma hakan yana kokarin ya dakushe zawarcin ɗan ƙwallon, bayan da za su buga wasan sada zumunta da Celtic.

    Howe ya ce yana sa ran Isak zai ci gaba da taka leda a St James Park.

    Ranar Juma'a Isak ya bar sansanin horo da suke yi a Austria, kuma ba za a je da shi Glasgow ba.

    Mai shekara 25, wanda aka sauya shi a wasan sada zumunta da yake yi wa kasarsa Sweden, saboda rauni, ana ta alakanta shi da zai koma wasa Liverpool ko kuma Al-Hilal ta Saudiyya, inda Howe ke fatan riƙe Isak, wanda ya ci ƙwallo 27 a kakar da aka kammala.

  2. Galatasaray ta miƙa tayin fam miliyan 2.6m kan golan Manchester City da Brazil Ederson, mai shekara 31. (L'Equipe)

    Barcelona, da AC Milan, da Al Hilal da Al Nassr suna cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gaban Liverpool da Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 26. (Caughtoffside)

    Manchester City na tunanin zawarcin golan Burnley da Ingila James Trafford, mai shekara 22, amma sai idan ɗaya daga cikin manyan masu tsaron gidansu biyu ya tafi. (Fabrizio Romano)

    Ɗan wasan tsakiya na Netherlands da RB Leipzig Xavi Simons, mai shekara 22, ya fi son komawa gasar Premier, inda Chelsea da Arsenal su ka sanya ido kan halin da yake ciki a ƙungiyarsa. (Bild)

  3. Qinwen Zheng za ta yi ɗan hutu daga buga ƙwallon tennis

    Ƴar kasar China, Qinwen Zheng ta sanar ranar Asabar cewa za ta huta daga buga ƙwallon tennis, sakamakon raunin gwiwar hannu.

    Wadda ta lashe lambar yabo a Olympic a 2024 tana mataki na shida a jerin waɗanda ke kan gaba a wasan.

    Sai dai Zheng, mai shekara 22 ta yi rashin nasara a zaagayen farko a hannun Katerina Siniakova a Wimbledon a farkon watan Yuli.

    Zheng ta lashe kofi biyar har da na Pan Pacific Open a Japan a cikin Oktoban 2024, sai dai ba ta taɓa lashe Grand Slam ba.

  4. Yamada ya koma Celtic daga Kawasaki

    Ɗan wasan tawagar Japan, Shin Yamada ya koma Celtic daga Kawasaki Frontale kan yarjejeniyar kaka huɗu.

    Mai shekara 25 ya ci ƙwallo 32 a wasa 121 da ya buga a babbar gasar tamaula ta Japan.

    Ya yi ban kwana da ƙungiyarsa, bayan da take mataki na shida a teburi, bayan karawa 23 wadda ya yi wa wasa 21 da cin ƙwallo biyu.

    Yamada ya bi sawun ƴan ƙwallon da suka koma Celtic a kwanan nan da ya haɗa da Benjamin Nygren da Callum Osmand da Hayato Inamura da Kieran Tierney da kuma Ross Doohan.

  5. Arsenal ta sanar da waɗanda za su yi mata sada zumunta a Singapore da Hong Kong

    Arsenal ta bayyana matashi mai shekara 15, Max Dowman da Marli Salmon daga cikin waɗanda za ta je da su wasannin sada zumunta a Singapore da kuma Hong Kong.

    Dowman da Salmon za su haɗe da sabbin ƴan wasan da Gunners ta ɗauka, wato Martin Zubimendi da Kepa Arrizabalaga da Christian Norgaard daga cikin 30 da za ta yi tafiyar da su.

    Sai dai Noni Madueke da ta saya daga Chelsea, ba zai je buga wasannin ba, domin an bashi hutu, sakamakon Club World Cup da ya buga wa ƙungiyar Stamford a Amurka.

    Kenan ɗan wasan tawagar Arsenal zai kari horo tare da ƴan wasa da zarar Arsenal ta koma Ingila.

    Arsenal za ta fara wasa a Singapore da AC Milan ranar 23, sai kuma ta kece raini da Newcastle ranar 27 ga watan Yuli.

    Daga nan za ta je Hong Kong domin fuskantar Tottenham ranar 31 ga watan Yuli.

  6. Ons Jabeur ta daina yin tennis saboda koshin lafiyarta

    Ons Jabeur ta hakura da buga wasan ƙwallon tennis, domin kula da koshin lafiyarta.

    Ƴar kasar Tunisa kenan ba za ta kara a wasannin da za a yi a Montreal Open ba, kuma ita ce daga waɗanda ke jerin zuwa 99 a kwallon tennis a duniya da ba za ta shiga US Open ba.

    Jebeur ta taɓa kaiwa mataki na biyu a jerin ƙwallon tennis a duniya, yanzu ta yi kasa zuwa ta 71.

    Wadda ta yi ta biyu karo biyu a baya a Wimbledon Open ta yi ban kwana da gasar bana a zagayen farko a wasannin da aka kare a All Engalnd Club.

  7. Bell da Dobson da kuma Lake sun yi rawar gani a Diamond League

    Ƴan Burtaniya, Georgia Hunter Bell da Charlie Dobson da kuma Morgan Lake sun taka rawar gani a gaban ƴan kaloo 60,000 a London Diamond League.

    Mai lambar yazo ta azurfa a Olympic, Hunter Bell ta lashe gudun mita 800 na mata cikin dakika 56.74.

    Shi kuwa Dobson ya yi nasara a gudun mita 400, wanda ya kare a dakika 44.14.

    Lake ta yi nasarar lashe tsallen rairayi, bayan takara da gwarzuwar duniya mai rike da kambi Yaroslava Mahuchikh da mai rike da lambar yabo ta Olympic, Eleanor Patterson.

  8. Juventus na tunanin yin musayar ƴan wasa da Manchester United inda za ta miƙa ɗan wasan tsakiyar Brazil Douglas Luiz, mai shekara 27 ta kuma karɓo dan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22. (Tuttosport)

    Jose Mourinho yana sha'awar sayen ɗan wasan Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, a Fenerbahce. (T24)

    Sunderland ta amince ta biya fam miliyan 17.5 kan ɗan wasan Faransa da Sassuolo Armand Lauriente, mai shekara 26. (Sky Sports).

  9. Ya kamata Napoli ta ɗauki darasi daga abin da ya faru da ita a baya - Conte

    Ya kamata Napoli, wadda ta lashe kofin Serie A a kakar da ta wuce ta ɗauki darasi daga abin da ya faru da ita a kakar 2023/24, in ji koci, Antonio Conte.

    Napoli ta fuskanci kalubale a kakar 2023/24, wadda ta kare a mataki na 10 a teburin gasar da sauya masu horar da tamaula uku, ciki har da Luciano Spalletti, wanda ya bar ƙungiyar

    Spalletti ya ja ragamar Napoli ta lashe Scudetto a karon farko bayan shekara 33 a kakar 2022-23.

    A watan Yunin bara aka bai wa Conte aikin horar da Napoli, wanda ya lashe Serie A uku a Juventus da ɗaya a Inter Milan da kofin Premier League a Chelsea, domin ya mayar da ƙungiyar kan ganiya.

    Tuni dai Napoli ta ɗauki ƴan wasa domin tunkarar kakar bana da ya haɗa da Kevin De Bruyne da Noa Lang da kuma Luca Marianucci da sauransu.

  10. Man United da Leeds sun tashi ba ci a wasan sada zumunta

    Ƙungiyar da Ruben Amorim ke jan ragama, Manchester United ta tashi 0-0 da Leeds United a wasan sada zumunta da suka buga a Stockholm.

    Leeds wadda za ta koma buga Premier League a kakar da za a fara a cikin watan Agusta ta fafata da United a gaban ƴan kallo 45,345 a Strawberry Arena, filin da United ta lashe Europa League a 2017.

    Sabbin ƴan wasan da United ta ɗauka kwanan nan, wato Matheus Cunha da kuma Diego Leon sun buga mata karawar.

  11. Ɗan wasan tsakiyar Ingila Ethan Nwaneri, mai shekara 18, ya ƙulla sabuwar yarjejeniya ta shekara biyar da Arsenal. (Telegraph)

    Tottenham ta fara neman ɗan wasan Bournemouth da Ukraine Ilya Zabarnyi mai shekara 22. (TalkSport)

    Ipswich na jiran ingantacciyar tayi daga Brentford kan ɗan wasan gaban Ingila Omari Hutchinson mai shekara 21. (Sky Sports)

    Norwich na daf da sayar da ɗan wasan gaban Amurka Josh Sargent, mai shekara 25, ga Wolfsburg kan fam miliyan 21. (Sky Sports)

  12. Leeds ta amince da farashin da Hoffenheim ta yi wa Stach

    Leeds United ta amince da farashin £17m da Hoffenheim ta yi wa Anton Stach.

    Stach zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka huɗu da zarar an kammala komai, har da karin tsarabe-tsarabe.

    Da zarar Stach ya kammala komawa Leeds, zai zama na shida da ta ɗauka a kakar nan.

    Wakila Leeds United za take sa ɗan wasan tawagar Jamus tare da Sean Longstaff a fili, wanda aka tabbatar da ɗaukarsa ranar Juma'a daga Newcastle United kan £12m.

    Tuni dai Leeds ta ɗauki mai tsaron baya, Sebastiaan Bornauw da Jaka Bijol da Gabriel Gudmundsson da kuma Lukas Nmecha.

  13. Barcelona tana tattaunawa da Man United kan cinikin Rashford

    Barcelona ta kusan kammala ɗaukar Marcus Rashford daga Manchester United.

    Tun cikin Disamba Barcelona ke son sayen Rashford, wanda ya samu rashin jituwa da koci, Ruben Amorim.

    An sanar da BBC cewar Barcelona na tattaunawa da United, ana kuma sa ran idan komai ya kammala a ƙulla yarjejeniya nan kusa.

    Tun a kakar nan Barcelona ta yi niyar sayen Nico Williams, sai kuma daga baya mai shekara 22 ya kara tsawaita sa hannu a kan kwantiragin kaka 10 a Athletic Bilbao.

    Rashford ya buga wasannin aro a Aston Villa a kakar da ta wuce tun daga watan Janairu, wanda ya yi karawa 11 a dukkan fafatawa da cin ƙwallo huɗu da bayar da shida aka zura a raga.

    Yana ɗaya daga ƴan wasa biyar a United masu karɓar albashi mai tsoka - amma sai Amorim ya bukaci ɗan ƙwallon Ingila da ya koma yin atisaye shi kaɗai.

    Da kyar ne idan mai shekara 27 zai sake yi wa United tamaula karkashin Amorim.

  14. Ko Madueke zai taka rawar gani a Arsenal kuwa?

    Tuni dai Arsenal ta kammala ɗaukar Noni Madueke daga Chelsea kan £48.5m.

    Mai shekara 23 yana daga cikin ƴan wasan Chelsea da suka buga mata Club World Cup a Amurka, daga baya ya bar sansanin tun kafin wasan da Chelsea ta doke Paris St Germain 3-0 ta lashe kofin, wanda ya koma Ingila domin kammala rattaba kwantiragi.

    Madueke ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar a Emirates kan kuɗin da ya kai £50m har da tasarabe-tsarabe.

    Ya buga wa Chelsea wasa 92 tun bayan da ya koma Stamford Bridge daga PSV Eindhoven kan £30m a Janairun 2023 da cin ƙwallo 20 da lashe Conference League a bara.

    Madueke shi ne na huɗu da Arsenal ta saya kawo yanzu, bayan Kepa Arrizabalaga daga Chelsea da Christian Norgaard daga Brentford da Martin Zubimendi daga Real Sociedad da kuma Cristhian Mosquera daga Valencia.

  15. Jama'a barkan mu da kasancewa a shirin sharhi da bayanai kan labaran wasanni daga sassan duniya daga ranar Asabar 19 - 26 ga watan Yulin 2025.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma a X.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar da shirin.