Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye daga 19-25/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku sharhi da bayanan wasanni a faɗin duniya daga Asabar 19 - 25 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

  • Arsenata kusan kammala sayen ɗan wasan Sporting, Viktor Gyokeres
  • Rashford na shirin buga wa Barcelona wasannin sada zumunta daga Man Utd
  • Dan wasan Valencia, Mosquera ya haɗu da Arsenal a Singapore inda Gunners ke fatan kammala cinikinsa
  • Liverpool ta nace wa Rodrygo, Xhaka zai koma Sunderland
  • Za a auna koshin lafiyar Ekitike, domin kammala cinikin da Liverpool ta amince fam miliyan 69 daga Eintracht Frankfurt
  • Ɗan ƙwallon Brighton, Evan Ferguson zai buga wa Roma wasannin aro
  • Za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ƴan wasan Arsenal 30 da za su buga mata wasanni a Asia

    Masu tsare raga

    • David Raya
    • Kepa Arrizabalaga
    • Tommy Setford
    • Alexei Rojas-Fedorushchenko

    Masu tsare baya

    • William Saliba
    • Ben White
    • Gabriel Magalhaes
    • Jurrien Timber
    • Jakub Kiwior
    • Oleksandr Zinchenko
    • Riccardo Calafiori
    • Myles Lewis-Skelly
    • Josh Nichols
    • Marli Salmon

    Masu buga tsakiya

    • Martin Odegaard
    • Christian Norgaard
    • Mikel Merino
    • Sambi Lokonga
    • Martin Zubimendi
    • Declan Rice
    • Louie Copley

    Masu cin ƙwallaye

    • Bukayo Saka
    • Gabriel Martinelli
    • Leandro Trossard
    • Ethan Nwaneri
    • Reiss Nelson
    • Kai Havertz
    • Ismeal Kabia
    • Max Dowman
    • Andre Harriman-Annous
  2. Manchester City ta ƙayyade farashi fam miliyan 35 kan ɗanwasan tsakiya na Ingila James McAtee, mai shekara 22, wanda West Ham da Eintracht Frankfurt rubibinsa. (Telegraph - subscription)

    Real Madrid za ta jira har baɗi kafin ɗauko ɗanwasan baya na Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara. (Football Insider)

    An ɗage sabunta kwangilar ɗanwasan gaba na Brazil da Real Madrid Vinicius Jr, mai shekara 25, har sai zuwa 2026. (AS - in Spanish)

    Real Madrid na sa ido kan ɗanwasan Arsenal da Faransa William Saliba, mai shekara 24. (L'Equipe - in French)

  3. Wasannin sada zumunta da Arsenal za ta buga a Asia

    Arsenal za ta fuskanci Tottenham da Newcastle United da kuma AC Milan a karawar da za ta yi a Asia.

    Gunners ta je nahiyar da ƴan wasa 30 a mako biyun da za ta yi daga ciki har da sabon ɗan wasan da ta saya, Kepa Arrizabalaga da Martin Zubimendi da kuma Christian Norgaard, amma Noni Madueke na hutuwa, saboda ya buga wa Chelsea wasannin Club World Cup a Amurka.

    Jadawalin wasannin Gunners a Asia.

    • AC Milan (Laraba, 23 Juli)
    • Newcastle United (Lahadi, 27 Juli)
    • Tottenham Hotspur (Alhamis, 31 Juli)
  4. An kammala auna koshin lafiyar Rashford a Barcelona cikin nasara

    An kammala auna koshin lafiyar ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford a Barcelona cikin nasara, wanda zai buga mata wasa wata 12.

    Mai shekara 27 ya je Catalonia ranar Lahadi, bayan da Manchester United ta ba shi izinin zuwa Sifaniya, domin kammala ƙulla yarjejeniya.

    ƊAan wasan tawagar Ingila ya samu tarbar girma daga wajen koci, Hansi Flick da darakta Deco a filin atisayen ƙungiyar ranar Litinin.

  5. Wafcon - Abin da ya kamata ku sani kan karawar Najeriya da Afirka ta Kudu

    Ƙungiyoyi huɗu kaɗai suka rage a Gasar Cin Kofin Afirka ta Mata zuwa, yayin da ake gab da fara karawar daf da karshe.

    Ƙungiyoyin da suka rage a gasar da ake yi a Moroko sun kasance waɗanda ake ganin sun fi ƙwarewa wajen taka leda a nahiyar - Moroko mai masaukin baƙi da ke samun ɗimbin goyon baya a gida da Ghana da ke son cimma burinta na lashe kofin gasar a karon farko da masu son kare kambinsu na cikin abubuwan da suka sa wasannin za su ƙayatar.

    A ranar Talata, ƙungiyoyi biyu za su fara ɓarje gumi, wato Moroko da kuma Ghana a filin wasa na Olympic a birnin Rabat - sai kuma Afirka ta Kudu da za ta fafata da Najeriya a filin wasa na cauldron of Stade Larbi Zaouli a birnin Casablanca.

    Za ku iya ci gaba da karanta labarin idan kuka latsa nan.

  6. Ba ƙungiyar da za ta iya sayen Isak - in ji John Anderson

    Alexander Isak zai ci gaba da taka leda a Newcastle United a kakar da za a fara daga watan Agusta, domin ba ƙungiyar da za ta iya sayen ɗan ƙwallo.

    Wannan shi ne ra'ayin tsohon ɗan wasan Newcastle, John Anderson, bayan da ake tantama kan makomar ɗan wasan tawagar Sweden, saboda bai buga wasan sada zumunta da Celtic ba ranar Asabar.

    An yi ta yayata labarin Isak a makon jiya, lokacin da Liverpool ta nuna sha'awar sayen ɗan ƙwallo kan fam miliyan 120.

    Anderson ya kara da cewar da zarar kana da fitattun ƴan wasa to koda yaushe za ka jin jita-jitar da ba tushe balle makama.

    Newcastle United za ta buga wasan sada zumunta a kakar da za a fara mai zuwa.

  7. Kocin Manchester United Ruben Amorim na son sake shiga kasuwa domin ƙaro wasu sabbin ƴanwasa. (Mirror)

    Haka kuma United ta taya ɗanwasan gaba na Sporting Viktor Gyokeres, mai shekara 27, tare fatan janyo ra'ayin ɗanwasan zuwa Old Trafford maimakon Arsenal. (A Bola - in Portuguese)

    Kuma tana son ɗanwasan gaba na Italiya Francesco Pio Esposito, mai shekara 20, tayin da Inter Milan ta yi watsi a Janairu. (Football Italia - in Italian)

    Manchester United ta kamma diba lafiyar ɗanwasan gaba na Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, wanda ta karɓo daga Brentford. (Fabrizio Romano)

    Nottingham Forest na kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiya na Ingila Jacob Ramsey, mai shekara 24, daga Aston Villa. (Football Insider)

  8. Har yanzu Arsenal na karancin ƴan wasa - Arteta

    Mikel Arteta ya ce Arsenal tana karancin ƴan wasa, amma yana duba hanyar da zai inganta nagarta da kwarewa ƴan ƙwallon ƙungiyar.

    Tuni dai Gunners sai cefane take don shirin tunkarar kakar bana da za a fara a cikin watan Agusta, inda ta sayi Martin Zubimendi da Kepa Arrizabalaga da Christian Norgaard da Noni Madueke jimilla kan fam miliyan 123.5.

    Haka kuma Arsenal tana tattaunawa da Sporting kan sayen Viktor Gyokeres kan fam miliyan 63.5 tana kuma son ɗaukar Cristhian Mosquera daga Valencia.

    Ƙungiyar Emirates na fatan kammala cinikin Gyokeres, domin ta je da shi Asia, inda za ta buga wasannin sada zumunta.

    Arsenal za ta kara da AC Milan a Singapore da Newcastle United, daga nan ta je Hong Kong don fuskantar abokiyar hamayya, Tottenham.

  9. Rashford yana tattaunawa da Barcelona kan buga mata wasannin aro

    Ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford yana Sifaniya, domin tattaunawa kan buga wa Barcelona wasannin aro zuwa kaka ɗaya.

    Mai shekara 27 ɗan wasan tawagar Ingila ya je Catalonia ranar Lahadi, bayan da United ta amince ya je ya kammala kulla yarjejeniya da Barcelona.

    Tun cikin watan Disamba Rashford ya ce yana fatan gwada sa'a a wata ƙungiyar, bayan da Ruben Amorim ya ajiye shi a benci.

    Rashford zai buga wasannin aro karo na biyu a jere, bayan wata shida da ya yi a Aston Villa a Premier League a kakar da ta wuce.

    Ana sa ran za a cimma yarjejeniya tsakanin Barcelona da Rashford a makon nan, sannan ya bi ƙungiyar wasannin sada zumunta da za ta yi a Japan da Koriya ta Kudu a shirin tunkarar kakar bana.

  10. Liverpool ta amince da farashin fam miliyan 69 da Frankfurt ta yi wa Ekitike

    Liverpool ta amince za ta sayi ɗan wasan Eintracht Frankfurt, Hugo Ekitike kan fam miliyan 69.

    Ana sa ran ɗan wasan tawagar Faransa, mai shekara 23 zai je Ingila ranar Talata, domin a auna koshin lafiyarsa.

    Frankfurt ta kulla kwantiragin ne kan fam miliyan 79 daga ciki fam miliyan 10 na karin tsarabe-tsarabe.

    Ana sa ran Ekiteke zai sa hannu kan kunshin yarjejeniyar kaka shida, sannan a makon nan zai je ya samu Liverpool, wadda za ta yi wasannin sada zumunta a Asia.

    Ekitike ya ci ƙwallo 15 a wasa 31 a Frankfurt, wadda ta yi ta uku a kan teburin Bundesliga a kakar da ta wuce.

    Kawo yanzu Liverpool ta kashe fam miliyan 250 wajen sayen ƴan wasa, domin tunkarar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.

    Liverpool ta sayi Florian Wirtz a matakin mafi tsada a Burtaniya kan fam miliyan 116m da Milos Kerkez da Jeremie Frimpong da kuɗinsu ya kai fam miliyan 70 jimilla..

  11. Ya kamata Man United ta kara sa ƙwazo - Amorim

    Ya kamata Manchester United ta kara sa ƙwazo in ji koci Ruben Amorim, ya faɗi haka ne bayan da suka tashi 0-0 a wasan sada zumunta da Leeds United a shirin tunkarar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.

    United ta kammala kakar da ta wuce a mataki mafi muni, bayan da ta kare a mataki na 15 a kasan teburin Premier League, sannan ta kasa samun gurbin shiga gasar Champions League, bayan da Tottenham ta doke ta a wasan karshe ta lashe Europa League.

    Ƙungiyar Old Trafford ba ta yi wani abin gwaninta ba sosai a karawar da ta yi da Leeds United United a Stockholm ranar Asabar, duk da ta fara karawar da sabon ɗan wasan da ta saya, Matheus Cunha.

    United za ta kara da Werst Ham United a MetLife Stadium in New Jersey ranar 26 ga watan Yuli.

  12. Wasan sada zumunta da za a buga ranar Litinin

    Las Palmas da Brighton

    Sporting da Sunderland

  13. Liverpool ta kusan kammala sayen Hugo Ekitike daga Frankfurt

    Liverpool ta kusan sayen Hugo Ekitike daga Eintracht Frankfurt, har ana cewa an amince da farashin £78m.

    Sai dai abinda ya rage matashin ɗan wasan mai shekara 23 ya amince da kunshin kwantiragin da za a gabatar masa, wanda ya koma buga Bundesliga daga Paris St Germain.

    Tun farko Ekitike ya koma Frankfurk, domin buga wasannin aro kan yarjejeniyar wata takwas daga baya ta mallaki ɗan ƙwallo, wanda ya ci ƙwallo 15 daga wasa 31, inda Frankfurt ta kare a mataki na ukun teburi a kakar da ta wuce.

    Tun farko Newcastle United ta yi niyar zawarcin matashin mai buga wa tawagar Faransa tamaula ta ƴan kasa da shekara 21 kan £70m daga baya ta hakura.

    Haka kuma Liverpool na duba yiwuwar ko za ta iya sayen ɗan wasan Newcastle United, Alexander Isak, sai dai tuni aka sanar da ita cewar bana sayar wa bane.

    Kawo yanzu Liverpool ta ɗauki Florian Wirtz da Jeremie Frimpong da Milos Kerkez.

    Idan har Liverpool ta kai ga sayen Ekitike, tabbas Darwin Nunez da kuma Federico Chiesa za su bar Anfield.

    Haka kuma ƙungiyoyi da yawa na son sayen Luis Diaz, amma Liverpool ba ta shirya sayar da ɗan ƙwallon tawagar Colombia ba.

  14. Juventus na dab da kammala cinikin ɗanwasan Ingila Jadon Sancho daga Manchester United yayin da ƙungiyoyin biyu suka cimma matsaya kan farashin ɗanwasan na gaba mai shekara 25. (Tuttosport - in Italian)

    Juventus a shirye take ta biya farashin da Manchester United take nema sama da fam miliyan 21 kan Sancho wanda ya ƙulla yarjejeniyar shekara huɗu da Juve. Sportmediaset - in Italian)

    Liverpool ce kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekara 21, inda ta sha gaban Tottenham - amma ɗanwasan na son ya ƙara yin shekara gudana a Selhurst Park. (Sun on Sunday)

    Manchester United da Newcastle United na hamayya kan ɗanwasan gaba na Paris St-Germain da Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26. (Footmercato - in French)

  15. Jack Draper ba zai buga gasar ƙwallon tennis biyu ba

    Jack Draper ba zai buga gasar ƙwallon tennis biyu ba, sakamakon raunin da ya ji a hannunsa.

    Mai shekara 23 ba zai samu shiga wasannin Canadian Open a karshen watan Yuli da kuma Cincinati Open da za a yi a cikin watan Agusta.

    Ɗan wasan Burtaniya, wanda shi ne na ɗaya a ƙwallon tennis a kasar, zai yi jinya, domin ya murmure da wuri ya fuskanci US Open, wanda za a fara daga ranar 24 ga watan Agusta a birnin New York.

    Draper ya ji raunin ne a Wimbledon Open a zagaye na biyu, inda Marin Cilic ya yi waje da shi.

    Sauran fitattun yan wasan da ba za su buga Canadian Open har da Jannik Sinner da Novak Djokovic.

  16. Zelensky ya taya Usyk murna buge Dubois a turmi na biyar

    Shugaba, Volodymyr Zelensky ya taya ɗan damben Ukrainian, Oleksandr Usyk murna, bayan da ya yi nasarar lashe dukkan damben boksin na duniya ajin babban nauyi wato WBA, WBC, IBF da kuma WBO, kuma karo na biyu a tarihi.

    Ya kuma kira shi da sunan gwarzo da cewar duk lokacin da ya samu nasara ya kan karawa kasar kwarin gwiwa.

    A karshen mako ne Usyk ya yiwa ɗan Burtaniya, Daniel Dubois bugun kwaf daya a damben boksin a turmi na biyar a wasan da suka yi a Landan.

    Dan damben Ukraine ya ce burinsa ya cika zai kuma huta tare da iyalansa, wanda ya killace kansa sama da wata uku domin yin atisaye tukuru.

  17. A shirye Arsenal take ta lashe manyan kofuna - Madueke

    Noni Madueke ya ce a shirye Arsenal take ta lashe manyan kofuna, wanda ya sanar da hakan bayan kammala komawa Gunners kan £48million daga Chelsea.

    Ɗan wasan tawagar Ingila, shi ne na huɗu da Mikel Arteta ya ɗauka domin tunkarar kaka mai zuwa da za a fara a cikin watan Agusta.

    Ana ta yin cece-kuce da Arsenal ta ɗauki Madueke da cewar nagartarsa ba ta kai Gunners ta saye shi ba, kuma kawo yanzu Gunners ta kashe £120million.

  18. Messi ya ci New York Red Bull ƙwallo biyu a MLS, yana da 18 jimilla

    Lionel Messi ya ci wa Inter Miami ƙwallo biyu a babbar gasar tamaula ta Amurka, MLS, bayan da suka ci New York Red Bulls 5-1.

    Mai shekara 38 yana da hannu a cin huɗu daga biyar da aka zura a raga a karawar da suka yi a New Jersey.

    Kenan ya ci wa Inter ƙwallo biyu a wasa shida daga bakwai baya, yana da 18 jimilla.

    Inter Miami tana ta biyar a kan teburi.

  19. Bayern Munich na samun ci gaba kan buƙatar karɓo ɗanwasan gaba na Liverpool Luis Diaz bayan watsi da tayinta har sau biyu. Ana sa ran ƙungiyoyin biyu za su tattauna kan ɗanwasan mai shekara 28 na Colombia. (Bild - in German)

    Fenerbahce ta cimma yarjejeniyar ɗauko ɗanwasan baya na Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 30, da ɗanwasan tsakiya na Spain Marco Asensio, mai shekara 29 daga Paris St-Germain. (Footmercato - in French)

    Ɗanwasan gaba na Gabon striker Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 36, ya yi watsi da buƙatarsa da Al-Ettifaq ta yi bayan ya baro Al-Qadsiah amma ɗanwasan ya zaɓi ya koma Marseille. (Footmercato - in French)

    Chelsea na fatan sayar da ɗanwasan gaba na Ingila Raheem Sterling kan fam miliyan 20m, domin dawo da wani kaso na kuɗin da ta biya Manchester City fam miliyan 47.5 shekaru uku da suka gabata. (Sun on Sunday)

    Tottenham na tattaunawa da Bayern Munich domin sayen ɗanwsan tsakiya na Portugal Joao Palhinha, amma dole sai ta biya fam miliyan 26 kan ɗanwasan mai shekara 30 . (Christian Falk)

  20. West Ham ta ɗauki Kyle Walker tsohon ɗan wasan Southampton

    West Hata kammala ɗaukar Kyle Walker-Peters, wanda yarjejeniyarsa ya kare a Southampton.

    Ɗan wasan tawagar Ingila mai shekara 28, mai tsaron baya ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku a West Ham.

    Walker-Peters ya fara tamaula a Tottenham daga nan ya koma wasannin aro a Southampton a Janairu daga baya ta mallaki ɗan wasan.

    Ya buga wa Southampton wasa 202, amma ya bar ƙungiyar sakamakon da ta faɗi daga Premier League a kakar da aka kamma, bayan da ƙwantiraginsa ya kare.

    Kaɗan ya rage Walker-Peters ya koma Besiktas karkashin Ole Gunnar Solskjaer, daga baya aka watsar da batun, sakamakon da ɗan wasan ya zabi ya buga wa West tamaula.

    A kakar nan West Ham ta ɗauki mai tsaron bayan Senegal, Al Hadji Malick Diouf daga Slavia Prague da ɗaukar aron mai tsaron baya, Jean-Clair Todibo daga Nice.

    Ta kuma sayar da Mohammed Kudus ga Tottenham kan £55m.