Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye daga 19-25/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku sharhi da bayanan wasanni a faɗin duniya daga Asabar 19 - 25 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

  • Arsenata kusan kammala sayen ɗan wasan Sporting, Viktor Gyokeres
  • Rashford na shirin buga wa Barcelona wasannin sada zumunta daga Man Utd
  • Dan wasan Valencia, Mosquera ya haɗu da Arsenal a Singapore inda Gunners ke fatan kammala cinikinsa
  • Liverpool ta nace wa Rodrygo, Xhaka zai koma Sunderland
  • Za a auna koshin lafiyar Ekitike, domin kammala cinikin da Liverpool ta amince fam miliyan 69 daga Eintracht Frankfurt
  • Ɗan ƙwallon Brighton, Evan Ferguson zai buga wa Roma wasannin aro
  • Za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Barau FC ta naɗa Ladan Bosso sabon kocinta

    Ladan Bosso

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta sanar da naɗa Ladan Bosso a matsayin sabon kocinta kafin fara kakar wasa ta bana.

    Wata sanarwa da kulbo ɗin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce nan gaba zai yi ƙarin bayani kan yarjejeniyar da ya ƙulla da Boso.

    Wannan ne karon farko da ƙungiyar ta jihar Kano za ta buga babbar gasar firimiya ta Najeriya NPFL bayan samun gurbi a kakar wasa ta 2024-25 a gasar NNL.

    Ladan Bosso ya jagoranci tawagar Najeriya ta 'yan ƙasa da shekara 20 wato Flying Eagles zuwa kofin ƙasashen Afrka da kuma Kofin Duniya daga 2020 zuwa 2023.

    Haka nan ya yi aikin horar da ƙungiyoyi a Najeriya da suka haɗa da Bayelsa United da kuma El-kanemi Warriors.

  2. AC Milan ta ɗauki Estupinan daga Brighton

    Pervis Estupinan

    Asalin hoton, Reuters

    Pervis Estupinan ya koma ƙungiyar AC Milan ta Italiya daga Brighton kan kuɗi fan miliyan 17.

    Ɗanwasan bayan na ƙasar Ecudor ya kasance mai muhimmanci a Brighton tun bayan da ya koma can daga Villarreal a 2022, inda ya ci ƙwallo biyar a wasa 104.

    Yana cikin tawagar da ta samu gurbin buga gasar zakarun Turai karon farko a tarihin Brighton a 2023, kafin Roma ta fitar da su daga gasar Europa League a zagayen 'yan 16.

    Tuni Milan ta ɗauki Luka Modric daga Real Madrid, da Samuele Ricci daga Torino, da Pietro Terracciano daga Fiorentina.

  3. Barcelona ta dakatar da buga wasa a Japan saboda saɓa yarjejeniya

    Barcelona

    Asalin hoton, Reuters

    Barcerlona ta dakatar da wasan sada zumunta da ta tsara bugawa da Vissel Kobe a birnin Tokyo na Japan saboda "saɓa yarjejeniyar" da kamfani mai ɗaukar nauyin wasannin ya yi.

    Balaguron ƙungiyar zuwa Japan na cikin abin da ta tsara a matsayin shirye-shiryen fara kakar wasa ta bana, kuma yanzu ta ce ɗaya karawar da za ta yi a Koriya ta Kudu ma na cikin haɗarin sokewa.

    Barca ba ta bayyana sunan kamfanin ba amma kuma ta ayyana sunan Yasuda Group a lokacin da ta fitar da sanarwar yin balaguron tun da farko.

    Wata sanarwa da ta fitar ta ce: "Ya zama dole Barcelona ta dakatar da wasan da aka shirya yi ranar Lahadi mai zuwa a Japan saboda saɓa yarejejeniya da wani kamfani ya yi.

    "Saboda haka, kulob ɗin zai duba yiwuwar ɗaga wasannin da zai buga a Koriya ta Kudu idan kamfanin ya cika wasu sharuɗɗa."

  4. Wolves ta ɗauki Arias daga Brazil

    Arias

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wolves ta ɗauki Jhon Arias daga Fluminense ta Brazil ka kuɗi fan miliyan 15.

    Cinikin ya ƙunshi ƙarin fan miliyan huɗu na tsarabe-tsarabe da za a biya kan takardun zama a Turai na ɗanwasan na ƙasar Colombian.

    Ɗanƙwallon mai shekara 27 da ke buga gefe ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara huɗu tare da zaɓin tsawaita ta da wata 12.

    Zai saka riga mai lamba 10 wadda Matheus Cunha ya bari bayan komawa Man United a watan da ya gabata.

    Aris na iya bugawa a ɓangaren hagu ko dama, duk da cewa ba a kallonsa a matsayin wanda ya maye gurbin Cunha kai-tsaye.

  5. Barcelona ta kammala ɗaukar aron Rashford daga Man United

    Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya kammala sa hannu kan yarjejeniyar buga wa Barcelona wasannin aro zuwa karshen kakar bana.

    Cikin ƙunshin ƙwantiragin, Barcelona za ta iya sayen ɗan wasan mai shekara 27 kan fam miliyan 30.3 da zarar ya taka rawar gani.

    Haka kuma Barcelona ce za take biyan ɗan wasan a karawar aron da zai yi mata kaka ɗaya..

    United ta samu rarar fam miliyan 14 zuwa 15 ƙudin albashin Rashford, zuwa karshen kakar bana, wanda ya rage albashinsa.

    Wannan shi ne karo na biyu da Rashford zai buga wasannin aro, bayan da ya yi a Aston Villa a Premier League a kakar da ta wuce.

    Rashford ya ci kwallo 138 a wasa 426 a Manchester United tun daga lokacin da ya fara taka mata leda a 2016.

  6. Bayern Munich ta shiga zawarcin Simon ɗan wasan da Chelsea ke son saya

    Xabi Simon

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich ta shiga zawarcin Xavi Simons, wanda Chelsea ke son saya, inda tuni ƙungiyar Stamford Bridge ke tattaunawa da RB Leipzig.

    To sai dai Chelsea za ta fuskanci kalubale a cinikin, saboda Bayern Munich da ta shiga zawarcin ɗan ƙwallo.

    Simon, ɗan wasan tawagar Netherlands ya fara daga makarantar koyon tamaula ta Barcelona daga nan ya koma Paris St Germain a 2019.

    Ya yi kaka ɗaya a PSV Eindhoven a 2022-23 daga nan ya sake komawa PSG, ya kuma buga wasannin aro a .2023-24 a RB Leipzig daga baya ta mallake shi a Janairun shekarar nan.

    An ce chelsea tana son kulla yarjejeniyar da za ta haɗa da yin musaya da Carney Chukwuemeka.

    Chukwuemeka ya buga wasannin aro a Borussia Dortmund a kakar da ta wuce.

    Tuni dai Chelsea ta sayi Joao Pedro daga Brighton kan £60million da kuma Jamie Gittens daga Dortmund.

  7. Barcelona za ta je buga wasannin sada zumunta a Japan da Koriya ta Kudu

    Ranar Alhamis Barcelona za ta sauka a Japan, domin buga wasannin tunkarar kakar da za mu faɗa a cikin watan Agusta, wadda za ta yi karawa uku har da ziyartar Koriya ta Kudu.

    Mai rike da La Liga da Copa del Rey da Spanish Super Cup za ta fara fafatawa da Vissel Kobe ta Japan ranar Lahadi, kwana hudu tsakani ta fuskanci FC Seoul ta Koriya ta Kudu, sannan ta kare da wasa da FC Daegu ranar 4 ga watan Agusta.

  8. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Atletico Madrid ta fara tattaunawa da Chelsea kan yarjejeniyar Renato Veiga, inda Chelsea ke neman fam miliyan 35 ga ɗanwasan na Portugal. (Fabrizio Romano)

    Everton na son ɗanwasan Bayern Munich da Morocco mai shekara 19 Adam Aznou. (Athletic - subscription required)

    Manchester United na sa ido kan ɗanwasan Angers da Mali ɗan ƙasa da shekara 20 Dan Sinate. (Sun)

    Everton na son ɗanwasan gaba na Atletico Madrid da Brazil Samuel Lino. (AS - in Spanish)

  9. Arsenal ta ci AC Milan 1-0 a wasan sada zumunta

    Saka

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Arsenal ta fara wasannin tunkarar kakar bana da kafar dama, bayan da ta doke AC Milan 1-0 ranar Laraba a wasannin sada zumunta da take yi a nahiyar Asia.

    Bukayo Saka ne ya ci mata ƙwallon a wasan farko da ta fara don shirin ganin ta taka rawar gani a kakar da za a fara a cikin watan Agusta.

    Haka kuma Gunners ta yi amfani da sabbin ƴan ƙwallon da ta dauka a wasa da ya haɗa da Christian Norgaard da Martin Zubimendi da kuma Kepa Arrizabalaga.

    Har da matashin ɗan wasa mai shekara 15, Max Dowman, wanda ake sa ran za take saka shi a wasanni a kakar bana, duk da karancin shekarunsa.

  10. Brys ya ajiye aikin horar da Kamaru wata biyar a fara gasar kofin Afirka

    bRYS

    Asalin hoton, Michel Mvondo/BBC

    Marc Brys ya ajiye aikin kociyan tawagar Kamaru, wata biyar kafin a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka a Morocco, inda ɗan kasar Belgium ya ce ba a biya shi albashi ba tare da mataimakansa.

    Tun farko Brys ya samu rashin jituwa da hukumar ƙwallon kafar Kamaru karkashin Samuel Eto'o tun lokacin da ya karɓi aiki a Afirilun 2024, amma kuma ma'aikatar wasanni ke biyan ɗawainiyarsa.

    Kamaru tana rukunin da ya haɗa da mai riƙe da kofin Ivory Coast da Gabon da Mozambique a wasannin cin kofin Afirka da za a fara daga 21 ga watan Disamba zuwa 16 ga watan Janairun 2026 a Morocco.

    Haka kuma Kamaru tana ta biyu a rukunin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Mexico da Canada a 2026 da tazarar maki ɗaya tsakani da Cape Verde mai jan ragama, kuma saura wasa hur-huɗu suka rage.

    Tawaga ɗaya za a ɗauka a rukunin, za kuma a ci gaba da fafatawa cikin watan Satumba da Oktoba.

  11. Ferguson zai buga wa Roma wasannin aro daga Brighton

    Ferguson

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan ƙwallon tawagar Ireland, Evan Ferguson zai buga was AS Roma wasannin aro zuwa karshen kakar nan, kamar yadda ƙungiyar dake buga Serie A ta sanar ranar Laraba.

    Ferguson zai taka leda a Roma da yarjejeniyar sayensa da zarar ya taka rawara gani.

    Ɗan ƙwallon ya koma Brighton daga Bohemians a Janairun 2021 lokacin yana da shekara 16 da haihuwa.

    Ya fara buga mata tamaula a Agustan karkashin kociya, Graham Potter.

  12. Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗanwasan gaba na Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24, na cikin zaɓin Liverpool domin maye gurbin Luis Diaz idan har ɗanwasan mai shekara 28 na Colombia ya bar Anfield. (Florian Plettenberg)

    Ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, na son a biya shi fam 300,000 a mako kafin sabunta yarjejeniya a Newcastle. (Talksport)

    Granit Xhaka ya amince da yarjejeniya da Sunderland, inda kungiyar ke tattaunawa da Bayer Leverkusen kan cinikin ɗanwasan na tsakiya mai shekara 32 ɗan ƙasar Switzerland (Times - subscription required)

    Brentford ta yi watsi da tayin fam miliyan 30 da Newcastle ta yi kan ɗanwasan gaba na DR Congo mai shekara 28 Yoane Wissa. (Tbrfootball)

  13. Ƙungiya takwas ce za su nemi lashe kofin Premier League a bana - Arteta

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Mikel Arteta ya ce kakar tamaula da za a fara a cikin watan gobe, za a yi tata burza, kuma kungiya takwas ce za suyi takarar lashe kofin Premier League.

    Gunners na fatan ɗaukar babban kofin tamaula na Ingila a karon farko tun bayan 2020 - hakan ya sa take ta kara karfin kungiyar da yin cefane.

    Tuni ta sayi Noni Madueke da Martin Zubimendi da Christian Norgaard da Kepa Arrizabalaga, sannan ta amince za ta ɗauki mai tsaron bayan Valencia, Cristhians Moskera.

    Haka kuma Gunners na fatan kammala sayen dan wasan Sporting, Victor Yokeresh kafin karshen mako.

    Abin da ya kawo tsaiko shi ne kudin karin tsarabe-tsarabe da Spotring ke son Arsenal ta biya.

    Tuni shikuwa Gyokeres ya amince da kwantiragin kaka biyar a Gunners.

    A kakar da ta wuce Arsenal ta yi ta biyu a teburin Premier League ba tare da lashe kofi koda na shayi ba.

  14. Alcaraz ba zai buga gasar Canadian Open ba

    Alcaraz

    Asalin hoton, Getty Images

    Wanda yake na biyu a kwallon tennis a duniya, Carlos Alcaraz ya bi sawun fitattun yan wasan da ba za su buga Canadian Open ba da za a fara a makon gobe.

    Dan kasar Sifaniya ya ce yana son ya huta, bayan raunin da ya ji a wasan karshe da Jannik Sinner ya doke shi ya lashe Wimbledon Open.

    Alcaraz, mai shekara 22 ya dauki Italian Open da French Open da kofin Queen's Club daga nan Sinner ya taka masa burki, bayan cin wasan tennis karo 24 a jere, sannan ya rasa kofin da yake da shi biyu a jere a All England Club a farkon watan nan.

  15. WAFCON: Za buga wasan karshe tsakanin Morocco da Najeriya

    Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria za ta buga wasan karshe da mai masaukin baƙi Morocco a karshen mako a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

    Super Falcons ta yi nasarar doke mai rike da kofin Afirka ta Kudu 2-1 aranar Talata

    Ita kuwa Morocco ta kai wasan karshe ne sakamakon doke Ghana da cin 4-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci.

    Za kuma a buga neman mataki na uku tsakanin Ghana da Afirka ta Kudu ranar Juma'a daga nan a fafata a karawar karshe ranar Asabar.

    Super Falcons

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Paul Gascoigne ya samu sauki, bayan jinya a asibiti

    Paul Gascoine

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitatcen tsohon dan wasan tawagar Ingila, Paul Gascoigne na kara samun sauki a gida, bayan da aka sallamo shi daga asibiti.

    Wani babban amininsa, Steve Foster ne ya same shi kwance a galabaice a gida shi kadai, daga nan ya garjaya da shi asibiti,

    Gascoigneya yi rawar gani a murza leda, wanda ya yi fice a Newcastle da Tottenham da Lazio da Rangers da Middlesbrough da kuma Everton.

    To sai dai bayan da ya yi ritaya ya ci karo da kalubalen rayuwa, sakamakon yawan ƙwanƙawaɗar barasa da ciwon damuwa.

  17. Ten Hag ba zai bar Xhaka ya koma Sunderland ba

    Xhaka

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Sunderland ta son kammala sayen Granit Xhaka daga Bayer Leverkusen, sakamakon gogewar da yake da ita a Premier League.

    Dan wasan tawagar Switzerland mai shekara 32, ya fara tamaula a kwararren dan wasa a Basel daga nan ya je Borussia Monchengladbach, sai Arsenal ta saye shi, wadda ya yi wa kaka bakwai a Emirates.

    Ya fara wasa a Gunners a 2016, wadda ya yi wa karawa 297 da lashe FA Cup biyu, sai ya koma Leverkusen a Yulin 2023.

    Xhaka, wanda ya buga wa kasarsa wasa 137 ya lashe lik a kakarsa ta farko da yin karawa 49 a dukkan fafatawa daga ciki ya yi karawa 10 a Champions League a kakar da ta wuce.

    To sai dai kociyan Leverkusen, Erik Ten Hag ya ce ba zai bari Xhaka ya bar ƙungiyar ba.

  18. Ina aka kwana kan tafiyar Gyokeres zuwa Arsenal?

    Victor Gyokeres

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Victor Gyokeres

    Arsenal na ci gaba da matsa ƙaimi a yunƙurinta na sayen dan wasan gaba Viktor Gyokeres daga kungiyar Sporting CP domin cike gibin da take da shi na rashin tsayayyen mai ɗaga raga.

    Sai dai lamarin na ta jan ƙafa inda har magoya bayan ƙungiyar ke nuna gajiyawa kan abin da suke gudu ya zama ‘jiran gawon shanu’.

    Sai dai ana ganin cewa yanzu akwai haske kan yunkurin, inda ake ganin cewa yana gab da tafiya Emirates.

    Tun a makon jiya ne BBC ta ruwaito cewa an kai matakin ƙarshe a cinikin ɗan wasan kan kuɗi fam miliyan 63.5, sai dai daga baya an tsaya ana tataɓurza tsakanin Arsenal da Sporting kan sauran kuɗaɗen tsarabe-tsarabe.

    Gyokeres dai ya riga ya amince cewa zai tafi Arsenal kan kwantaragi mai tsawon shekara biyar.

    An shafe shekaru ana kiraye-kirayen cewa ya kamata Arsenal ta dauko garnannen mai zura zura kwallo, abin da ake ganin tamkar Arteta ya yi kunnen uwar-shegu da su.

    Gyokeres dan asalain kasar Sweden ya zura kwallo 39 a kakar da ta gabata – fiye da kowane dan wasa a manyan gasannin kungiyoyin Turai guda takwas.

    Idan sayen Gyokeres ya tabbata, zai zama daya daga cikin cinikin dan wasa da ya fi jan hankali a wannan lokaci na musayar ‘yan wasa.

    Ganin cewa ɗan wasan gaba na Arsenal Gabriel Jesus zai kai ƙarshen wannan shekara yana jinya, ana kallon Viktor a matsayin wanda ya dace da Arsenal a wannan lokaci ganin cewa ba a cika yi wa Kai Haverts kallon cikakken lamba 9 ba.

    Gyokeres ya ƙware wajen riƙe ƙwallo da gudu da ita a ƙafarsa da kuma kutsawa ta tsakiyar masu tsaron baya.

    Haka nan ɗan ƙwallon na da ɗan karen gudu, wanda ake ganin wannan ma zai taimaka wa Arsenal.

  19. Crystal Palace ta ɗaukaka ƙara kan hana ta buga gasar Europa

    Crystal Palace ta lallasa Manchester City inda ta lashe kofin ƙalubale na Ingila - FA

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Crystal Palace ta lallasa Manchester City inda ta lashe kofin ƙalubale na Ingila - FA

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace da ke Ingila ta miƙa koke ga Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen wasannin motsa jiki kan mayar da ita ƙaramar gasar Conference League bayan cancantar buga gasar Europa.

    Ƙungiyar ta shigar da ƙorafin nata ne a kan hukumar kula da wasan ƙwalon ƙafa ta Turai, Uefa, wadda ita ce ta yanke hukuncin, da ƙungiyar ƙwallon kafa ta Lyon da ke Faransa da kuma ƙungiyar Nottingham Forest da ke Ingila.

    Forest wadda ta gama gasar Premier a matsayi na bakwai a kakar da ta gabata, ana sa ran za ta maye gurbin Palace wadda ta lashe kofin ƙalubale na FA a gasar ta Europa.

    A korafin da ta gabatar, Crystal Palace ta buƙaci a soke matakin da ɓangaren kula da zuba jari na Uefa ya ɗauka, sannan a mayar mata da gurbinta na buga gasar Europa a maimakon Nottingham ko kuma Lyon.

    Ana sa ran a yanke hukunci kan wannan ƙorafi daga nan zuwa ranar 11 ga watan Agusta, inda wasannin rukuni na gasar ta Europa za su fara a ranar 24 ga watan Satumba.

    Dokokin Uefa sun tanadi cewa ba za a bar ƙungiyoyi biyu da ke ƙarƙashin mutum ɗaya taka rawa a gasa ɗaya ba.

  20. Ƴanwasa 10 mafiya tsada da ƙungiyoyin Premier suka saya a kwanan nan

    Kammala yarjejeniyar komawar Byan Mbeumo zuwa Manchester United na daga cikin waɗanda suka ja hankali tun bayan buɗe kasuwar musaya a gasar Premier a halin yanzu.

    Ɗan wasan ya tafi Manchester United ne kan kuɗi fam miliyan 55.

    Ga jerin ƴan wasan da ƙungiyoyi suka ɗauka da kuma kuɗinsu:

    ...