Wanne tasiri yajin aikin likitoci ya fara yi a asibitocin Najeriya?

liktoci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayanai sun ce kwana biyu da shiga yajin aikin amma har wasu asibitoci sun daina karɓar marasa lafiya
An wallafa

An shiga rana ta uku a yajin aikin sai Baba ta gani da likitoci masu neman ƙwarewa ke yi a Najeriya.

Likitocin sun shiga yajin aikin ne ranar Litinin bisa wasu batutuwa da suka ce gwamnati ta ƙi ba su haɗin kai ciki har da tsaiko wajen biyan albashi da alwus-alawus.

Ba wannan ne karon na farko da likitocin masu neman ƙwarewar ke shiga yajin aiki ba, asali ma wannan ne karo na huɗu cikin shekara guda da likitocin ke shiga yajin aiki.

Wasu majinyata da ke kwance a wani asibitin gwamnati da ke babban birnin Abuja, sun ce sun shiga damuwa saboda ƙauracewar likitocin da ya kamata su ci gaba da duba lafiyarsu.

Wani magidanci da ke kwance a babban asibitin Gwarimpa ya ce a tsawon ranar Talata, babu likita ko ɗaya da ya je babban ɗakin maza da suke kwance kamar yadda aka saba don ganin halin da suke ciki.

"Sai magungunan da ke nan kawai aka ba ni. Jikina akwai dai ɗan sauƙi amma tun da babu likitoci, muna cikin damuwa," in ji majinyacin da ba a ambaci sunansa ba.

Ya faɗa wa BBC wani dattijo da ke kwance a kusa da shi yana cikin wani hali saboda babu wani (likita) da ya zo ya gan shi.

Wakilin BBC da ya zagaya asibitin, ya ce tun daga ƙofar shiga ana iya gane alamu na tasirin yajin aiki da likitoci masu neman ƙwarewar suka fara daga ranar Litinin.

A cewarsa, likitoci kimanin sittin ne suka shiga yajin aikin a wannan asibiti na Gwarimpa, hakan kuma ba ƙaramin giɓi ba ne a wannan cibiyar lafiya.

Shi ma wani da ke jinyar ƙafarsa da ta karye a asibitin na Gwarimpa ya ce yana fargabar lafiyar ƙafarsa wadda ya kamata ta samu kulawar likita duk bayan kwana biyu zuwa uku.

Ya ce masifar yajin aikin likitoci ba abu ne mai kyau ba a gare su. Don haka ya yi kira ga ɓangarorin biyu su daure su sasanta.

Irin waɗannan asibitoci ana samar da manyan likitoci waɗanda kuma ba sa cikin yajin aiki, sai dai yawansu bai taka kara ya karya ba.

Dr. Dare Godia, shi ne zaɓaɓɓen shugaba ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa na ƙasa mai jiran gado ya kuma shaida wa BBC cewa za su ci gaba da yajin aiki har sai baba ta gani.

Ya dai zargi gwamnati da nuna rashin gaskiya da kuma gaza cika alƙawari daga ɓangarenta, lamarin da a cewarsa ya tilasta musu ɗaukar wannan mataki.

Ya ce za su ci gaba da yajin aiki, don kuwa ba sa so nan da nan a koma kuma daga bisani su sake tsunduma yajin aiki, don haka dai gwamma a yi ta, ta ƙare.

Likitocin dai suna neman gwamnatin Najeriya ta cika alƙawari wajen biyan buƙatunsu ciki har da inganta yanayin aiki da biyan kuɗaɗen alawus-alawus da ma albashinsu.

Zuwa yanzu dai ba a ji martani daga bakin gwamnatin ƙasar kan wannan yajin aiki da likitocin suka fara ranar Litinin ba.