Ƴanbindiga sun yi garkuwa da jami'in ma'aikatar tsaron Haiti

Asalin hoton, EPA
Rahotanni daga ƙasar Haiti na cewa wasu mutane masu ɗauke da makamai sun yi garkuwa da babban jami'in ma'aikatar ministan tsaron ƙasar a babban birnin ƙasar, Port-au-Prince.
James Boyard, wanda fitaccen masanin harkokin tsaro ne, kuma babban sifeton 'yan sanda na ƙasar, ana kyautata zaton shi ne jami'i mafi girma da aka yi garkuwa da shi a Haiti cikin 'yan shekarun nan.
Wasu mutane biyu da suka san yadda lamarin ya faru sun tabbatar wa jaridar The New York Times da batun sace shi. Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an yi garkuwa da Boyard ne a yankin Bourdon, ɗaya daga cikin wuraren da ake ganin har yanzu suna da ɗan tsaro a babban birnin kasar.
Ƙasar Haiti, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'umma a yankin Karebiyan, ta shafe shekaru tana fama da tashe-tashen hankula da ayyukan ƙungiyoyin masu laifi. Rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da mutum miliyan ɗaya da muhallansu.




