Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 31/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Mutum 10 sun mutu, yayin da bakwai suka jikkata bayan rushewar gini a Ibadan

    Rushewar gini

    Aƙalla mutum 10 ne suka mutu yayainwa su bakwai suka jikkata bayan faɗuwar gini a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

    Cikin wata sanarwa da hukumar kashe gobara ta jihar ta fitar, ta ce lamarin ya faru da tsakar daren da ya gabata a unguwar Jegeda Oluloyo da ke binrin na Ibadan, kamar yadda Jaridar unch ya ruwaito.

    Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da aka zaƙulo gawarwarkin mutum 10 daga cikin ɓaraguzan ginin, an kuma ceto wasu mutum bakwai da raunuka, sannan an ci gaba da aikin ceton domin nemo ƙarin mutane.

    Faɗuwar gine-gine dai wani lamari ne da ke neman zaman ruwan dare a Najeriya, inda da dama takan zo da asarar rayuka masu yawa.

    Mahukuntar ƙasar na ɗora alhakin matsalar kan rashin bin ingantaccen tsari da ƙa'ida a lokacin yin gine-ginen.

  2. Babu barazanar ƙarancin man fetur a Najeriya - Manyan dillalai

    man Fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan dillalan man fetur a Najeriya, sun tabbatar wa 'yan ƙasar cewa akwai wadattacen man fetur a ƙasar, don haka 'yan ƙasar su kwantar da hankalinsu.

    Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar manyan dillalan, Clement Isong, ya fitar ranar Laraba ya ce akwai wadattacen mai a rumbunan ajiyar matatar mai ta Dangote da na babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL.

    Isong ya ƙara da cewa babu wata barazana game da ƙarancin man fetur a ƙasar.

    A makon nan ne dai kamfanin mai na NNPCL ya ƙara farashin man fetur a ƙasar.

    To sai dai duk da haka an riƙa ganin dogayen layuka a wasu gidajen man ƙasar, wani abu da ya ƙara haifar da fargabar ƙaruwar farashin man a zukatan 'yan ƙasar.

  3. An dakatar da sufurin jiragen ƙasa tsakanin Valencia da Madrid saboda ambaliya

    Ma

    Asalin hoton, Getty Images

    An dakatar da sufurin jiragen ƙasa masu saurin gaske na tawon kwana 15, tsakanin wasu manyan biranen Sifaniya, Valencia da Madrid sakamakon mummunar ambaliya da ta shafi ƙasar.

    Ministan sufurin ƙasar, Óscar Puente, ne ya bayyana haka a birnin Madrid, ya ce dakatarwar za ta iya kai wa mako uku saboda yadda ɓarnar ta yi yawa.

    ''Ambaliyar lalata layukan dogon da ya haɗa tsakanin manyan biranen biyu, kuma zai ɗauki lokaci kafin a gyara su'', kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ambato ministan na bayani.

  4. Kotun Ƙolin Ghana ta yi watsi da matakin rufe majalisar dokokin ƙasar

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun kolin Ghana ta yi watsi da matakin rufe majalisar dokokin ƙasar a makon da ya gabata.

    An dai ɗauki matakin rufe majalisar ne ƙasa da wata biyu a yi babban zaɓen ƙasar.

    Kotun ta ce matakin na shugaban majalisar bai yi daidai ba, kuma ya nuna rashin fahimtar doka.

    Matakin da shugaban majalisar dokokin ƙasar ya ɗauka na ƙwace kujerun wasu ƴan majalisa huɗu da suka sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya ya haifar da hargitsi a zauren majalisar, da kuma taƙaddamar shari'a kan jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisar.

    Kundin tsarin mulkin Ghana bai ba ƴan majalisa damar sauya sheƙa daga jam'iyar da aka zaɓe su ba.

  5. An dawo da wutar lantarki a wasu jihohin arewacin Najeriya

    Lantarki

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya, TCN ya ce ya fara gyara matsalar da ta haifar da katsewar lantarki a wasu jihohin arewacin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Laraba da maraice, ya ce ya samu nasarar mayar da wutar lantakin zuwa wasu yankunan arewacin ƙasar, bayan gyaran layin rarraba wutar na Ugwuaji-Apir da ya samu matsala.

    TCN ya ce yankunan da wutar ta dawo sun haɗa da Lafiya da Makurdi da Jos da Kano da Nasarawa da Benue da Kano da Kaduna da Bauchi da kuma Gombe.

    Haka kuma kamfanin ya ce injiniyoyinsa na ci gaba da aiki domin tabbatar da komai ya daidaita, kuma wutar ta isa sauran yankunan da matsalar ta shafa, nan ba da jimawa ba, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    A farkon wannan makon ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta gyaran layin rarraba wutar da ya lalace sakamakon ayyukan 'yan bindiga.

    Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar, Tinubu ya bayar da umarnin jibge jami'an tsaro a wurin gyaran domin bai wa masu gyaran kariya.

  6. Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami da zai iya ratsa nahiyoyi

    Makami

    Asalin hoton, Reuters

    Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami da zai iya ratsa nahiyoyi, wanda ya yi tafiyar mintuna 86.

    Makamin shi ne irinsa na farko mafi cin dogon zanzo da aka taɓa yin gwajinsa.

    An harba makamin da aka yi wa laƙabi da ICBM, wanda ya yi tafiyar nisan kilomita 7,000 a sama, wanda hakan ke nufin inda a kwance aka harba zai yi doguwar tafiyar da babu makami mai linzamin da ya taɓa yin irinta.

    Bayan ya dawo ƙasa, makamin ya faɗa cikin ruwan tekun gabashin ƙasar, kamar yadda ƙasashen Japan da Koriya ta Kudu suka bayyana.

    Gwajin - wanda aka yi ranar Alhamis - na zuwa ne a daidai lokacin da ke ƙara samun tsamin dangantaka tsakanin Koriya ta Arewa da maƙwabciyarta ta Kudu.

    Amurka ta ce gwajin irin waɗannan makaman ya saɓa wa dookin Majalisar Dinkin Duniya.

    Ma'aikatar tsaron koriya ta Kudu ta ce gwajin wani yunƙurin Koriya ta Arewa ne ƙara ƙarfafa makamanta.

    Cikin wani jawabi da ba kasafai yake irins a gidan talbijin na ƙasar, Shugaban Koriya ta Arewar, Kim Jong Un ya ce gwajin na cikin atisayen soji d ƙasar ke yi, kuma tauna tsakuwa ne kan yadda "za mu mayar da martani kan maƙiyanmu".

  7. Jihar Rivers ta ɗaukaka ƙara kan hana CBN bai wa jihar kasonta na gwamnatin tarayya

    Gwamnan Rivers

    Asalin hoton, Siminalayi Fubara/X

    Gwamnatin jihar Rivers ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja, da ya hana CBN bai wa jihar kason kuɗinta daga gwamnatin tarayya.

    A ranar Laraba ne alƙalin kotun, Mai Shari'a, Joyce Abdulmalik ya umarci Babban Bankin Najeriya CBN da ya dakatar da bai wa jihar kasonta daga asusun gwamnatin tarayya na wata-wata.

    Mai shari'a Abdulmalik ya ce kason jihar da Gwamna Fubara ke karɓa daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa yanzu ya saɓa doka, kuma dole a dakatar.

    Alƙalin ya ce gabatar da kasafin kuɗin da gwamna Fubara ya yi a gaban ƴan majalisar jihar guda huɗu kacal ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

    To sai dai kwamishin yaɗa labaran jihar, Joseph Johnson, ya shaida wa Jaridar Punch a ƙasar cewa gwamnatin jihar ta ɗaukaka ƙara kan batun, tare da fatn cewa kotun ɗaukaka ƙara zat soke hukuncin babbar kotun tarayyar.

  8. Yau ake bikin ranar birane ta duniya

    Birnin

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Birnin Beijing na ƙasar China

    A yau ne ake bikin ranar birane ta duniya, ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware don jawo hankali hukumomin game da yadda za a inganta birane da shigar da matasa cikin harkokin tafiyar da biranen.

    Ranar ta kasance wata dama ce ta bayyana wa hukumomin duniya muhimmancin samar da nagartattun tsare-tsaren da za su kawo sauƙi ga mazauna birane musamman wajen tafiyar da harkokin rayuwar yau da kullum da kuma kawo ci gaba mai ɗorewa.

  9. An sako likitar da aka yi garkuwa da ita a Kaduna bayan wata 10

    Popoola

    Asalin hoton, NARD

    Likitar nan da aka yi garkuwa da ita a jihar Kaduna, Dr Ganiyat Popoola ta shaƙi iskar ƴanci bayan shafe kimanin wata 10 a hannun masu garkuwa.

    Poppola, wadda take aiki a asibitin ido na ƙasa da ke Kaduna, an sace ne a ranar 27 ga Disamban shekarar 2023 tare da mijinta, Nurudeen Popoola wanda sojan sama ne da ɗanuwanta Folaranmi Abdul-Mugniy, amma a watan Maris aka sako mijinta, amma masu garkuwar suka ci gaba da riƙe likitar da ɗanuwan nata.

    A watannin baya ne ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa suka shiga yajin aiki saboda nuna rashin daɗin su kan gaza ƙwato likitar a hannun masu garkuwa.

    A jiya Laraba ne dai aka sako likitar da ɗanuwanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga shugaban ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa, Dr Tope Zenith Osundara, wanda ya bayyana cewa ba a biya kuɗin fansa ba.

  10. Waɗanda suka rasu a ambaliyar Spain sun kai 95

    Spain

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da ayyukan ceto a ambaliyar da ta ɗaiɗaita yankin Valeancia a ƙasar Sifaniya a cikin sa'a 24 da suka gabata.

    Zuwa yanzu dai waɗanda suka rasu sun kai aƙalla mutum 95, a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.

    Daga cikin waɗanda suka rasu akwai ɗan Burtaniya mai shekara 71 bayan an ceto shi a gidansa da ke Alhaurin de la Torre a garin Malaga.

    Kawo yanzu dai ruwan ya tsagaita, amma firaiministan ƙasar Pedro Sanchez, ya ce akwai buƙatar mazauna yankin su ɗan dakata a tabbatar da tsayawar ambaliyar.

    Hukumomi dai a ƙasar sun ce har yanzu ba a tantance haƙiƙanin mutane nawa suke ɓace ba a sanadiyar ambaliyar.

  11. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafinmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.