Zaɓen Amurka: Jihar da yaƙin Gabas ta Tsakiya zai iya sauya sakamakon zaɓenta

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Rafid Jabouri
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Aiko rahoto daga, Michigan
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Yayin da ranar zaɓen shugaban ƙasar Amurka ke ƙara matsowa al'ummar Larabawa 'yan Amurka da ke jihar Michigan sun samu kansu a wani yanayi na tunanin ina za su karkata a zaɓen.
Kasancewar jihar tana da ƙuri'un wakilai 15 da ke da muhimmanci wajen sauya sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, yawancin al'ummar jihar, Larabawa suna cikin tababa kan inda za su karkata a zaɓen, tsakanin Donald Trump da Kamala Harris, musamman ma ga waɗanda suka damu da abubuwan cikin gida na Amurka da kuma abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.
Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa ba a taɓa kan-kan-kan ba a tarihin zaɓen Amurka kamar wannan, inda Kamala Harris take gaban Donald Trump a yawan jama'a to amma ba a nan take ba - domin ƙuri'ar wakilan jihohi ce ke tabbatar da wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasar.
Kasancewar Michigan ɗaya daga cikin jihohin da ba-a-san-machi-tuwo... a zaɓen, kuma da ganin irin yawan al'ummar Larabawa da ke jihar, wannan zai iya sauya sakamakon zaɓen.
Al'ummar da kanta yake rarrabe

Ra'ayin Larabawa 'yan Amurka da ke Michigan, ya rarrabu kamar yadda ainahin tarihi da al'adunsu suke, a kan manufofin Amurka na cikin gida da kuma waje.
Rima Meroueh, ta ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙi da jin daɗin al'ummar Amurkawa Larabawa a birnin Dearborn a jihar ta Michigan, ta gaya wa BBC cewa, yin ƙiyasin ainahin yawan ƙuri'ar al'ummar Larabawa abu ne mai sarƙaƙiya.
Ƙidayar jama'a ta Amurka ba ta ɗaukar Larabawa a matsayin wata ƙabila ta daban, wanda hakan ya sa da wuya a iya tantance yawansu, to amma Ms Meroueh ta yi ƙiyasin cewa aƙalla akwai Larabawa 'yan Amurka 300,000 a Michigan.
Idan aka duba wannan yawa, Trump ya ci Michigan a 2016 da ƙuri'a 10,000 kawaiLokacin da Joe Biden ya ci jihar a 2020, da tazarar ƙuri'a 100,000 ne.
Saboda haka duk da cewa yawan ƙuri'ar Larabawa kaɗan ne a jihar ta Michigan, za su iya yin tasiri sosai a zaɓen.
Ms Meroueh ta ce yawanci Larabawa 'yan Amurka a lokacin zaɓe ba su cika karkata ra'ayi ɗaya ba, to amma a wannan karon batun yaƙin Gaza yana zuciyar yawancinsu.
To amma duk da haka akwai daga cikin Larabawan masu zaɓe da suka yarda da manufar Trump ta “Amurka Farko” inda suke ganin da haka zai kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya.
Wasu kuma na ganin cewa Harris za ta fi ƙoƙari ta hanyar diflomasiyya a kai ga cimma sasanto mai ɗorewa.
Akwai kuma rukuni na uku, da ke goyon bayan 'yar takarar jam'iyyar Green Party, wadda take adawa da goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra'ila.
Fafatawa kan manufar Gabas ta Tsakiya

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamala Harris ta ɗan lasa wa al'ummar Larabawa zuma a baki, da alƙawarin tabbatar da an dakatar da yaƙin na Gabas ta Tsakiya, tana kuma ƙara tabbatar da goyon bayan da jam'iyyarta ta Democrat ta daɗe tana ba Isra'ila.
Duk da wannan kuma ta yi magana kan 'yanci da damar Falasɗinawa ta rayuwa cikin 'yanci da cin gashin-kai ga dukkanin al'ummomin yankin. Wannan magana ce mai daɗi to amma kuma wadda ke da wuyar gamsar da Larabawa kamar Sam Abbas.
Mista Abbas na nuna irin baƙin ciki da ɓacin ran da Larabawa ke nunawa a kan Biden da Harris, inda suke ɗora musu alhakin jinin da ake zubarwa a Gabas ta Tsakiya, inda ya ce duk wanda ya sani ya ce ba zai zaɓi Harris ba.
Amma duk da haka ya ce yana tunani kan zaɓen kuma ƙila sai a ranar zaɓe zai yanke shawara - wanne ne daga cikin ''munanan abubuwa biyu'' ya fi dama-dama?
A ɗaya ɓangaren duk da manufarsa ta ƙin baƙi, da mutane da yawa ke kallo ta ƙyamar Musulmi ce da Larabawa, da kuma goyon bayansa ga Isra'ila da kuma alaƙarsa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, abin mamaki Trump yana da magoya baya Larabawa.
Iƙirarinsa cewa ba yaƙin da aka yi a lokacinsa da kuma cewa da ya ci gaba da mulki da an kauce wa yaƙin Ukraine da Gabas ta Tsakiya, ya ja hankalin waɗanda ba sa son rikici.
Haka kuma Trump na bugun ƙirji da cewa baban mijin 'yarsa Balarabe ne, kuma nan da ɗan lokaci zai samu jika da rabisa Balarabe ne.
Sauya sheƙa
Haushin da ake ji na jam'iyyar Democrat, ya sa aka samu kungiyoyi a cikin al'ummar Larabawa 'yan Amurka da ke nuna adawa da jam'iyyar.
Masu irin wannan adawa na zargin jam'iyyar da maganar fatar baka kan batutuwan da suka shafi Musulmi da Larabawa, yayin da a fakaice suke bayar da goyon baya ga ci gaba da rikicin Gabas ta Tsakiya.
Ɗaya daga cikin masu wannan fushi da duka jam'iyyun biyu, shi Abdel Salam, wanda ya ce ba batu ba ne na ɗan takarar wata jam'iyya, magana ce ta goyon bayan Isra'ila da jam'iyya ke yi.
A saboda matsayin duka manyan jam'iyyun biyu ne ya ce sun karkata ga 'yar takarar jam'iyyar Green Party, Jill Stein ko da kuwa hakan zai ba Trump damar ci.
Abdel Salam ya ce za su yi hakan ne domin nuna wa jam'iyyar Democrat fushinsu kan watsi da ta yi da muryar Larabawa da Musulmi.

Samara Luqman, wadda Ba'amurkiya ce asalin Yemen - mai rajin tabbatar da dumukuraɗiyya da kuma harkar gidaje, ta daɗe tana goyon bayan jam'iyyar Democrat to amma abin mamaki a wannan karon ta sauya sheƙa inda ta zaɓi Trump.
Ta ce ba abin da ya sa ta sauya ra'ayinta kamar gayyatar da kwamitin yaƙin neman zaɓen trump ya yi mata tare da alƙwarin haɗa ta da Trump su tattauna.
Ta ce ganawarta da Trump ta sa ta fahimce shi, baya ga alƙawarin da ya yi na dakatar da yaƙin Gaza.
Bugu da ƙari ta ce ƙuria'r tata da ta wasu Larabawa Amurkawa, ladabtarwa ce ga jam'iyyar Democrat kan abin da ta yi a rikicin na Gabas ta Tsakiya.
Ko Harris za ta iya samun ƙuri'un Larabawa?

Duk da samun goyon bayan da Trump ke yi a Michigan, jam'iyyar Democrat ba ta karaya ba.
Tana da goyon baya sosai a tsakanin Amurkawa Larabawa , musamman ma tun bayan hare-haren 11 ga watan Satumba, na abin da ya biyo bayan harin a kan al'ummar.
Sami Khalidi, wanda shi ne shugaban ƙungiyar magoya bayan jam'iyyar Democrat a Michigan, yana cike da ƙwarin gwiwa duk da haka Harris za ta yi nasarar samun ƙuri'un Larabawa.
A hirarsa da BB, ya ce har kullum Harris na magana kan sake gina Gaza da kai wa Falasɗinawa kayan agaji, inda ya ƙara da cewwa ba ta yarda da batun sake mamaye Gaza ba - kuma wannan ya sa Larabawa Amurka goyon bayanta.
Fushi da ƙin zaɓe

To amma ga wasu Larabawan 'yan Amurka ba wani daɗin baki da kamfe da za a yi musu da zai sa su sauya ra'ayinsu saboda irin fushin da suka yi.
Jenine Yassin, Ba'amurkiya asalin Falasɗinu, mai zane-zane ta yanke shawarar cewa ba ma za ta yi zaɓen ba gaba ɗaya.
A wajenta manufar Amurka a kan Isra'ila aba ce da ba za ta sauya ba, kuma ta zargi dukkanin 'yan takarar da goyon bayan abin da ta kira kisan kiyashi a kan Falasɗinawa.
Wannan ra'ayi na Yassin na ƙin zaɓe ya nuna irin fushin da Larabawa 'yan Amurka da dama ke ciki.
Amma duk da haka ta bayyana ƙwarin gwiwarta na samun sauyi nan gaba, ganin yadda sa'o'inta matasan Amurkawa ke nuna adawa ga manufofin Amurka a kan Isra'ila.











