'Ƴanbindiga sun ƙaƙaba mana harajin da ba mu da ƙarfin biya'

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, ƴanbindiga sun sara harajin naira miliyan goma kan mutanen garin Faru na yankin karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, idan har suna son zaman lafiya, kuma su rika aikin gona.
Wannan dai ƙari ne kan hare-hare da sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa da ƴanbindigan kan yi yau da kullum.
Al'amarin dai ya ta'azzara har mutanen garuruwa aƙalla shida na yankin suna ta yin ƙaura zuwa wasu wurare.
Bayanai daga garin na Faru da wasu wasu garuruwa biyar da ke yankin ƙaramar hukumar ta Maradun a jihar Zamfarar, sun ce hare-hare da sauran ta'asar da ƴanbindiga ke tafka wa jama'a ta kai intaha.
Wani mazaunin gari ya shaida wa BBC cewa suna cikin mummunan yanayi, "Ko yaushe kwana muke cikin zullumi, a mazaɓu shida dake nan yankin duk matsalolinmu guda, cikin ɗar ɗar muke kwana muke tashi."
Mutum wanda ya nemi a sakaya sunanshi ya ce garuruwa shida ne da suka haɗa da Goron Namaye, Janbaƙo, da Faru magami, Ƙaya, da Magami.
Abin bai tsaya nan ba , domin kuwa ƴanbindigar sun ƙaƙaba masu harajin dole, kamar yadda wani mutumin garin ya bayyana."Sun sa mana haraji, kasantuwar wannan kuɗin ba a samu an haɗa masu shi ba, shine dalilin da ya sa suka matsa mana da kai hare-hare.
" Asalin mutanen mu da ke wurin su mu kan mu ba mu san adadinsu ba, akwai jami'an tsaro a garin amman kuma kasantuwarsu bai sanya ƴanbindigar sun daina abunda suke ba."
Yanzu haka dai jama'ar garuruwan da wannan al'amari ya shafa a yankin na Maradun suna cikin tsaka mai wuya.
"Amfanin gona musamman gyaɗa ya kai lokacin girbi, anaso a shiga a ɗebo amman abun ya gagara, kowa yana jin tsoron ya fita abakin ranshi."
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin ɓangaren gwamnatin jihar ta Zamfara game da wannan batu, amma kuma ba mu yi dacen samun mai magana da yawunta ta waya ba.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin johohin da matsalar tsaro ta fi kamari a faɗin Najeriya, inda barayin daji ke afkawa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.
Sai dai gwamnatin jihar da ta tarayya da jami'an tsaro na cewa su na bakin kokari domin magance matsalar, a wasu lokutan ma jami'an tsaro kan sanar da nasarar kashe wasu daga cikin 'yan bindigar.











