Fitaccen jagoran 'yan hamayya a Rasha, Alexei Navalny ya mutu a wani gidan yari da ke wani yanki mai tsananin sanyi kamar yadda kamfanonin dillancin labarai suka ruwaito abin da hukumar kula da gidan yarin ƙasar ta ce.
Ana kallonsa a matsayin ɗan adawar da yake yawan sukar Shugaba Vladimir Putin.
Yana zaman gidan yari na tsawon shekara goma sha tara saboda laifukan da ake ganin ƙulli ne na siyasa.
A ƙarshen shekarar da ta gabata ne aka mayar da shi gidan yarin da ke yankin Arctic da ake gani a matsayin mafi azabtarwa.
Hukumar gidan yarin da ke lardin amalo-Nenets ta ce tana bincike kan abin da ya janyo mutuwar tasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tass ya bayyana.
A tsawon shekaru, Alexey Navalny ya zame wa gwamnatin Rasha, ala ƙaƙai.
An soma jin sunansa ne a shekara ta 2011 lokacin zanga-zanga a Moscow bayan an tafka maguɗi a zaɓukan majalisun dokokin ƙasar.
A wajen zanga-zangar jami’an tsaro suka kamashi, kuma tun daga lokacin ya zama madugun ‘yan adawa.
Yana da dubban magoya baya a shafukan sada zumunta kuma yana yawan bankaɗo abubuwan rashawa, lamarin da ya sa shi tsule idon hukumomi a Rasha.
A bara ne, aka saka mishi guba, bayan ya ji ba ya jin daɗi a cikin jirgin lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa Siberiya. Daga bisani an garzaya da shi zuwa Jamus, inda a nan ƙwararru suka gano cewa akwai gubar Novichok a cikin jininsa.
A lokacin dai fadar Kremlin ta Rasha ta musanta cewa tana yunƙurin kashe shi, amma kuma bayan kammala jinya a Jamus, yana komawa Moscow a watan Junairun bara sai aka kama shi aka tisa ƙeyarsa zuwa gidan yari.
An yi zanga-zanga a faɗin ƙasar, bayan an wallafa wani bidiyo da ke zargin shugaba Vladmir Putin da cin hanci da rashawa.
Alexie Navalny ya mutu ya bar matarsa da ‘ya’ya biyu.
-
Yevgeny Prigozhin: Putin ya miƙa ta'aziyya kan mutuwar shugaban Wagner
-
Putin da Kim: Abokai a lokacin neman makamai