Yevgeny Prigozhin: Putin ya miƙa ta'aziyya kan mutuwar shugaban Wagner

An wallafa

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi jawabi a karon farko game da faɗuwar jirgin sama na ranar Laraba. Ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, kuma ya bayyana shugaban kamfanin sojojin hayar Wagner, Yevgeny Prigozhin a matsayin mutum mai baiwar kasuwanci.

A wani saƙo da ya gabatar ta kafar talbijin, Putin ya ce masu bincike za su yi nazari a kan abin da ya faru - amma dai hakan zai ɗauki lokaci

Ya ce da safiyar Alhamis ɗin nan ne aka shaida masa game da faɗuwar jirgin saman na ranar Laraba.

Ana kyautata zaton cewa Prigozhin ya mutu ne a wata faɗuwar jirgin saman da ta faru ranar Laraba, tare da ƙarin mutum tara.

Shugaban Rasha ya ce jagoran sojojin hayar Wagner "mutum ne mai hazaƙa" wanda "ya yi manyan kura-kurai a rayuwa".

Sai dai ƙiris ya rage ya tabbatar ƙarara da mutuwar Prigozhin.

Daga lokacin da jirgin saman ya faɗo, an yi ta zuzuta raɗe-raɗi game da abin da ya haddasa mummunar faɗuwar.

Tun da farko, wani zauren dandalin Telegram mai suna Grey Zone ne ya ba da rahoton cewa an harbo jirgin da wasu makaman kakkaɓo jiragen sama a yankin Tver, na arewacin birnin Moscow.

Jirgin saman, wanda ya tashi daga Moscow zuwa birnin St Petersburgh, ɗauke da fasinjoji guda bakwai da ma'aikatan jirgi uku.

Prigozhin ya jagoranci wani boren sojoji da bai yi nasara ba a kan rundunar sojin Rasha cikin watan Yuni.

Shafin Telegram na Grey Zone ya ruwaito mazauna yankin na cewa sun ji ƙarar fashewar wani abu har guda biyu kafin faɗuwar jirgin, kuma sun ga layukan tururi guda biyu a lokacin.

Kamfanin dillancin labarai na Tass ya ce jirgin saman ya kama da wuta a lokacin da ya dira a ƙasa, inda ya ƙara da cewa tuni aka gano gawawwakin mutane.

Ya ce jirgin ya yi tafiyar ƙasa da rabin sa'a bayan tashinsa.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha Interfax ya ruwaito ma'aikatar ba da agajin gaggawa na cewa ana kyautata zaton dukkan mutanen da ke cikin jirgin saman sun mutu, lokacin da ya faɗo ƙasa.

Ma'aikatar ta ƙara da cewa jirgin ya rikito ƙasa ne a kusa da unguwar Kuzhenkino a lardin Tver.

Rahotanni sun ce an gano gawawwakin mutum takwas a wurin da jirgin ya faɗo, haka zalika, babu tabbaci a kan cewar Yevgeny Prigozhin yana cikin jirgin saman.

Yevgeny Prigozhin shi ne shugaban kamfanin sojojin hayar Wagner, wanda ya kafa a shekara ta 2014.

Hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da tarihin aikata laifuka, ana yi masa inkiya da "Mai dafa wa Putin abinci" saboda yana samar da abinci ga fadar Kremlin.

A watan Yuni ne, ya jagoranci dakarunsa wajen gudanar da wani boren sojoji na taƙaitaccen lokaci, bayan ya ƙwace iko da birnin Rostov-on-Don na kudancin Rasha kuma ya tunkari birnin Moscow, da niyyar hamɓaras da shugabannin sojojin ƙasar.

Tun lokacin da ya jagoranci boren sojoji zuwa Moscow a ƙarshen watan Yuni, masu lura da al'amura da yawa a Rasha suka yi wa shugaban kamfanin Wagner nan, Yevgeny Prigozhin laƙabi da "Gawa tana tafiya".

'Ramuwa ce'

Martanin Shugaba Putin na farko ga ƙalubalantar shugabannin tsaron Rasha, cike yake da ɓacin rai, inda ya bayyana lamarin da cin amana da kuma yankan baya a cikin wani saƙon bidiyo da ya fitar ranar 24 ga watan Yuni.

Kuma duk da yake, cikin sauri an cimma yarjejeniyar da ta bai wa Prigozhin ci gaba da watayawarsa kuma daga bisani ya tafi Belarus, kafin ya koma birnin St Petersburg da kuma wannan mako, inda aka gan shi a wani wuri a Afirka, hakan ba ya nufin cewa yaba cikin aminci.

Da yake tsokaci game da batun Daraktan Hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA ya bayyana lamarin da cewa "ramuwa ce", ya ƙara da cewa "Putin ya fi son ya yi zubin abincinsa da sanyi ƙalau".

Duka wannan dai, tabbas, ba hujja ba ce cewa da gangan aka kai wa Prigozhin da ayarinsa hari.

Fadar Kremlin 'za ta yi ƙoƙarin ɗora wa Ukraine alhaki'

Wani tsohon mai ba da shawara ga Ma'aikatar Harkokin Wajen Ukraine, Dr Yuri Felshtinsky, ya ce idan Yevgeny Prigozhin ya mutu, to mai yiwuwa ne fadar Kremlin za ta yi ƙoƙarin ɗora alhaki a kan Ukraine.

Sai dai ya ce yana tunanin mutane kaɗan ne za su yarda da wannan labari, don kuwa Shugaban Russia yana da dalilin aikata haka fiye da haka.

Felshtinsky ya faɗa wa BBC ya yi imani cewa mutane kaɗan ne za su yi makokin mutuwar Prigozhin amma ya ce "ba zai yi mamaki ba" idan shugaban na Wagner daga bisani aka ce ya tsallake rijiya da baya.