Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Senegal za ta dauko malamin tsubbu don yi wa Mane magani, Borussia Dortmund za ta rike Bellingham
Senegal za ta yi amfani da malamin tsubbu a kokarin taimaka wa dan wasan gaba na Bayern Munich Sadio Mane, mai shekaru 30, wanda ya ji rauni a makon nan, domin ya samu halartar gasar cin Kofin Duniya da za a yi a wannan watan a Qatar. (Mail)
Mai tsaron gida na Canada Alphonso Davies, ya yi amanna cewa zai iya zuwa gasar cin Kofin Duniya, bayan dan wasan, mai shekaru 22, ya gurde a kafada a lokacin wasan Bayern Munich da Hertha Belin ranar Asabar da ta wuce. (Mail)
Borussia Dortmund na da kwarin gwiwar dan wasan tsakiy na Ingila mai shekara 19 Jude Bellingham, zai ci gaba da zama a kungiyar ko da kwantiraginsa ya kare, duk da cewa wasu kungiyoyin na zawarcinsa, ciki har da Chelsea, Liverpool, Manchester City da Manchester United. (90min)
Paris St-Germain na sha’awar dauko mai kai hari na Atletico Madrid, kuma zakaran kasar Faransa Joao Felix mai shekara 23 wanda ke zaman aro a Portugal daga nan zuwa badi. (Le Parisien, via Marca)
Aston Villa na zawarcin dan wasan gaba idan an bude kasuwar musayar ‘yan kwallo a watan Janairu, ya yin da dan wasan Villarreal, kuma mai tsaron gida na Sifaniya Pau Torres, mai shekara 25, da ke sha’awar aiki da sabon manajan kulup din Unai Emery. (Football Insider)
Dan wasan Everton da England kuma mai kai hari, Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 25, zai nutsu domin samun sauki daga ciwon kafada da yake fama da shi . (Guardian)
Barcelona ka iya dauko dan wasan gaba na Netherland Memphis Depay, mai shekara 28, idan an bude kasuwar ‘yan wasa a watan Janairu mai zuwa. (Caught Offside)
Southampton za ta biya Luton Town sama da fam miliyan 4 a matsayin diyya ga manaja Nathan Jones, wanda aka sanar zai maye gurbin Ralph Hasenhuttl da aka sanar da korarsa a ranar Alhamis. (Telegraph - subscription required)
Roma za ta sake nuna sha’awar dauko dan wasan Barcelona kuma mai tsaron baya na Sifaniya Hector Bellerin, mai shekaru 27, da dan wasan Portugal Diogo Dalot, mai shekara 23, wanda ke taka muhimmiyar rawa a Manchester United.