Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ‘yan sandan Najeriya suka kama mace mai garkuwa da mutane
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wata mace mai shekara 28 da ke cikin gungun masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a jihohin arewacin kasar.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Tatala, wanda kakakinta Frank Mba ya sanya wa hannu, rundunar ta ce matar mai suna Fatima Garba na cikin gungun masu garkuwa da mutane da suka addabi jihohin Sokoto, Kebbi, Niger da kuma Kaduna da ke arewacin kasar.
"Fatima ta amince cewa ta kwashe shekara daya tana bai wa masu garkuwa da mutane makamai, inda ake biyanta kudade da dama kan kowanne makami idan an yi amfani da shi wajen yin garkuwa da mutane," in ji Mr Mba.
Rundunar ta yi ikirarin cewa wani saurayin Fatima ne ya shigar da ita sana'ar garkuwa da mutane.
A cewar Mr Mba, jami'ansu sun kama sauran mutanen da ke gungun, wadanda suka hada da Samaila Usman, Mohammed Ibrahim, Mohammed Agali, Dahiru Bello, Shamsu Mohammed, Mohammed Usman, Umar Abdullahi, Buhari Abubakar da kuma Abubakar Garba.
Ya ce sun kama makamai da dama daga wurinsu da suka hada da:
Bindiga bakwai da suka hada da samfurin AK47 biyar, da G3 da fistol daidaya da harsasai 1476 da harsasai samfurin G3 guda 36 da kuma da wayar hannu takwas da sauransu.
Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa ta kama wasu masu satar motocin mutane a birnin Jos na jihar Filato, kuma a sakamon haka an gano motoci 21 da aka sace da wadanda duk da hannunsu a ciki.
"Sannan a sakamakon kama wadancan mutum biyu na Jos an gano wasu da suke hada baki da su wajen aikata hakan a garin Funtua da kuma Sakkwato,'' a cewar sanarwar.