Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, A'isha Babangida and Abdullahi Bello Diginza

  1. Gwamnati ta rufe katafaren shagon Sahad stores a Abuja

    Awa 24 bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hanyoyin dakile matsalar karancin abinci da tsadarsa a kasar, jami'an hukumar da ke kare muradan masu saye ta kasa sun rufe, babban shagon nan na Sahad Stores da ke yankin Area 11 a Abuja.

    An dai zargin cewa masu gkatafaren shagon da kara wa abokan huldarsu kudin kaya fiye da farashin da ke makale a jikin kayan.

    Da yake yi wa 'yan jarida bayani, shugaban hukumar mai kare muradan masu saye ta kasa, Adamu Ahmed Abdullahi ya ce wani bincike da hukumar ta gudanar kan katafaren shagon ya nuna musu yadda masu gudanar wa shagon suke "cutar" masu saye.

    Ya kara da cewa shagon zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

    “ Mun fahimci cewa mutanen nan abun da suke yi yaudara ne inda babu gaskiya da yin abu a faifai dangane da farashin kayan da suke da su wanda kuma hakan ya yi karo da sashe na (135) da dokar da ta hana a yaudari abokin hulda ta hanyar cea ka da mai saye ya biya kudin kaya fiye da abin da ke rubuce a kan kayan.” In ji Adamu Ahmed Abdullahi.

  2. Shugaba Tinubu na shan suka kan bai wa surukinsa mukami

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinibu ya nada surukinsa a matsayin wanda zai jagoranci hukumar samar da gidaje ta kasa, FHA, wani al'amarin da ya janyo cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya, inda suke alakanta abin da nuna son kai ga iyali.

    Oyetunde Oladimeji dai na auren babbar 'yar Tinubu, Folashade.

    Wannan ne dai karon farko da shugaba Tinubun ke nada wani daga cikin iyalinsa a wani matsayin jagoranci a matakin gwamnatin tarayya.

    Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa "Mista Ojo na da " gogewa na fiye da shekaru 10 a harkar gidaje da otal-otal. Sannan kuma tsohon dan majalisar tarayya ne."

    To sai dai 'yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani dangane da nadin, inda wasu ke cewa akwai mutanen da suka fi shi goge da cancanta.

    Nada mista Ojo dai a cewar mai magana da fadar shugaban kasa shi ne " kokarin yi wa hukumar samar da gidaje ta gwamnatin tarayya garambawul.

    • Dalilan da suka sa Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu
    • Abin da Tinubu ya fada wajen gabatar da kasafin kudi
  3. Yadda aka kama masu kasuwancin sassan jikin bil adama a Ogun

    'Yan sanda a jihar Ogun sun ce sun kama wani gungun mutane da suka ƙware wajen cinikin sassan jikin bil adama domin yin tsafi.

    Kwamishinan 'yan sanda, Mista Abiodun Olamutu ya ce daga cikin abubuwan da aka gano a hannun mutane har da zuciyar bil adama da jarkoki biyu cike da sassan jikin bil adama.

    Alamutu ya ce rundunar ta samu rahoton ɓatan wata mata masi suna Ms Sulaiimon Adijat ranar 9 ga watan Janairu bayan wani Adebayo Azeez ya gayyace ta.

    A bayanin kwamishinan, an yi ta kiran wayar matar tun lokacin da aka ba da rahoton ta ɓata amma ba a same ta ba kuma a cewarsa, hakan ne ya sa jami'an da ke yaƙi da masu sace mutane suka baza komarsu domin gano abin da ya faru da ita.

    Ya ƙara da cewa, binciken da aka yi ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna cikin wata ƙungiyar asiri mai suna 'Oshole' domin su haɗa naira miliyan ɗari biyu cikin mako ɗaya.

    Kwamishinan 'yan sandan ya ce duka mutanen da ake zargi sun amsa aikata laifin da ake zarginsu da shi. Ya ƙara da cewa ana gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ake zargi da suka tsere.

    • Ma'anar cinikin sassan jikin ɗan Adam, tasirinsa da haɗarinsa
    • Tattaunawa da mai safarar sassan jikin 'yan gudun hijira
  4. Sojin Isra'ila sun kama gomman mayaƙan Hamas a kudancin Gaza

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kama gomman mayaƙan Hamas a wani asibitin da suka kai samame a kudancin Gaza.

    Mai magana da yawun sojin, Daniel Hagri ya ce sun kai samamen da bai wuce iyaka ba a asibitin Nasser a Khan Younis.

    Sai dai wasu majiyoyin kiwon lafiya sun ce sojojin Isra'ilar sun bude wuta a asibitin sun kuma kashe marasa lafiya tare da jikkata wasu da dama.

    Mai magana da yawun sojin ya yi zargin cewa Hamas na amfani da asibitin wajen aje waɗanda ta yi garkuwa da su, sai dai ya ce basu samu wata sheda da za ta tabbatar da zarginsu ba.

    • Yadda Isra'ila ke shirin ƙaddamar da hari kan mafakar Falasɗinawa ta Rafah
    • Kotun Duniya: Me ya sa take sauraron zargin Isra'ila da kisan ƙare-dangi?
  5. 'Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace mutane a Sokoto

    Rundunar 'yan sanda a Sokoto ta kama mutum 15 da ake zargi da sace-sacen mutane da fashin daji da sauran laifuka a faɗin jihar.

    Rundunar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai inda ta yi holen wasu motoci ƙirar Toyota da suka an same su ne a hannun waɗanda ake zargi.

    Samamen da ya kai ga kama mutanen, a cewar kwamishinan 'yan sandan jihar, Aliyu Hayatu Kaigama, an kai shi ne a wurare daban-daban a wasu yankuna da ke Gwadabawa da Wurno da Wamakko da kuma kan titun Bodinga/Tambuwal.

    Kaigama ya bayyana hakan a lokacin da ake holen mutanen da ake zargi ciki har da yara ƙanana daga ƙaramar hukumar Binji waɗanda mutanen da ake zargi ke amfani da su domin nemo bayanai.

    Ya ce waɗanda ake zargi 16 an kama su ne a wasu samame na daban bayan wasu bayanai da rundunar ta samu daga jami'an da ke yaƙi da masu sace mutane da aikata ta'addanci.

    Ya bayyana cewa an samu mutanen da makamai da alburusai masu yawa.

    Kaigama ya kuma tabbatar da kama mutum biyu da ake zargi da samar da bindigogi a ƙaramar hukumar Bukuyum da ke maƙwabtaka da jihar Zamfara.

    • Matsalar tsaro na ƙara ta'azzara a jihar Sokoto
    • Wa'adin Ecowas ga Nijar ya tsunduma arewacin Najeriya cikin fargaba
  6. 'Ana kashe miliyoyin jakai duk shekara don haɗa maganin gargajiya'

    Wata ƙungiyar tallafi ta ƙiyasta cewa ana kashe kusan jakuna miliyan shida duk shekara domin biyan buƙatar maganin gargajiya na China.

    Ƙungiyar mai suna Donkey Sanctuary, ta ce raguwar yawan jakuna a China ya tilasta wa masana'antar karkatar da hankalinta zuwa Afirka domin samun fatar jakunan da za a yi amfani da su wajen samar da sinadarin gelatine.

    Hakan ya janyo ƙaruwar satar jakunan Afirka lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin jama'a da ke yankunan marasa galihu da ke dogara kan dabbobi wajen tafiyar da ayyukansu na karkara.

    Yanayin ya tilasta wa ƙungiyar tarayyar Afirka tattauna yiwuwar sa dokar haramci kan kashe jakuna da kuma fitar da fatunsu a wani taro da za a yi ranar Asabar a Addis Ababa.

    Afirka gida ne ga kashi biyu bisa uku na jakuna sama da miliyan hamsin a duniya.

    • Abin da ya sa muke so a yi doka a kan jakai — Dan majalisa
    • An hana fitar da jakai daga Nijar
  7. Ɗage zaɓen Senegal ya ci karo da doka – Kotu

    Kotun tsarin mulkin Senegal ta yanke hukuncin cewa ɗage zaɓen shugaban ƙasa zuwa watan Disamba da gwamnatin ƙasar ta yi ya saɓawa doka.

    Kotun ta kuma yi watsi da ƙudurin da majalisar ƙasar ta amince da shi na ƙarawa shugaba Macky Sall wa'adin mulki.

    Masu suka sun zargi shugaban da yunƙurin yin juyin mulki a ƙasar, da ake kallo a Afrika da ba a fiye yin juyin mulki ba.

    Wakiliyar BBC ta ce Senegal ta sha banban da sauran ƙasashen da take makwabtaka da su saboda dorewar dimokuradiyya.

    Hukumomin yankin yammacin Afrika da na Tarayyar Turai sun bayyana damuwarsu kan jinkirta zaɓen.

    • Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe
    • Me ya sa har yanzu wasu ƙasashen Afirka ke maraba da sojojin Faransa?
  8. Barkan mu da Juma'a – Babbar rana!

    Masu bibiyar mu, barka da warhaka. Da fatan muna lafiya a wannan rana.

    A yau ma, kamar kodayaushe, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe maƙwabta.

    Sai ku kasance tare da mu.