Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Qatar ta lashe gasar kofin ƙasashen Nahiyar Asiya

    C

    Asalin hoton, Qatar X

    Qatar ta zama gwarzuwar shekarar 2023, inda ta lashe gasar cin kofin ƙasashen Nahiyar Asiya.

    Ta doke Jordan da ci 3-1, hakan ya bata damar lashe gasar sau biyu kenan a jere.

    Qatar ce ta karbi baƙuncin gasar ta 2023.

    Qatar ta samu damar zuwa wasan ƙarshen wasan ne bayan doke Iran da ta yi a wasan kusa da na ƙarshe, ita kuma Jordan bta samu nasara ne a kan Koriya ta Kudu.

  2. Bankwana

    Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.

    Mu kwana lafiya.

  3. Za a fara baiwa matasa damar shiga aikin soji a Myanmar

    e

    Asalin hoton, RFA

    Shugabannin mulkin soja na Myanmar sun sanar da cewa matasa maza da mata za su yi aikin soja akalla na shekaru biyu.

    Sojojin da suka yi juyin mulki shekaru uku da suka gabata, na fafutukar yadda za su magance ayyukan ta'addanci.

    Rahotannin sun kuma bayyana yadda sojojin su ka fuskanci kalubale lokacin da za su dauki sabbin jami'ai bayan hambarar da gwamnatin farar hula.

  4. Macky Sall ya ce a shirye yake ya sauka daga mulkin Senegal

    S

    Shugaban Kasar Senegal Macky Salla ya yi watsi da zargin da 'yan dawa suke masa na maƙalewa a mulki, bayan ya sanar da ɗage lokacin zabe yunkurin da ya haifar da zanga-zanga.

    Ya kuma ƙara da cewa an dakatar da zabe a wannan lokaci ne, domin a samu damar kawo karshen rikici tsakanin yan takarar shugabancin ƙasar bayan an hana wasu takara a hukumance.

    Shugaban Senegal ya ce a shirye ya ke ya sauka daga mulki.

    Kungiyoyin masu rajin kare hakkin yan adam sun ce karkashin mulkinsa abokan hamayya na fuskantar shari'oi, yayin da ake harbe masu zanga-zangar adawa a tituna.

    Majalisar dokoki ta amince da karin watanni goma nan gaba kafin zaben, batun da 'yan adawa suka bayyana a matsayin yi wa dimukuradiyya juyin mulki.

  5. Sojin Amurka biyar sun mutu a hatsarin jirgin sama

    A

    An gano gawarwakin sojin ruwan Amurka biyar da suka mutu a farkon wannan makon a hatsarin jirgin saman da ya taso daga Nevada zuwa Calfornia.

    Jirgin mai saukar ungulu ƙirar CH-53E ya ɓata ne a ranar Laraba daga baya kuma an gano shi wani yankin mai duwatsu a Califonia.

    Jirgin dai na atisayen yaƙi ne ya kuma taso daga sansanin mayaƙan saman Amurka da ke Nebada kusa da San Diego.

    Har yanzu dai ba a san dalilin faruwar hatsarin ba, amma ana bincike a kan haka.

    An gano jirgin ne a cikin dusar ƙanƙara a yankin duwatsun Califonia - mai nisan kilomita 74 da inda zai sauka.

  6. Pakistan na neman shiga halin rashin tabbas

    g

    Asalin hoton, EPA

    Pakistan na fuskantar rashin tabbas yayinda ake ci gaba da dakon sakamakon zaben da aka gudanar a aranar Alhamis.

    Yan sanda a birnin Talagang da ke lardin Punjab sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa dandanzon masu zanga-zangar jinkirin sanar da sakamakon zaben.

    Jam'iyyar tsohon firaiministan Pakistan Imran Khan wanda ke tsare, da jam'iyyar abokin hamayyarsa Nawaz Sharif, dukkansu na ikirarin sun yi nasara a zaben

  7. Harin saman da Isra'ila ta kai Labanon ya kashe mutum biyu

    Aƙalla mutum biyu ne suka mutu, ciki harda badakaren Hezbollah, a harin da Isra'ila ta kai mai nisan kilomita 60 zuwa Labanon.

    Rahotanni sun ce harin ya rutsa da wani Bafalasdine da ke da alaƙa da Hamas, sai dai an ce ya tsira da ransa.

    Tun watan Nuwamba, bayan fara yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas, kusan kullum sai an yi musayar wuta tsakanin Mayaƙan Hezbollah da Isra'ila, sai dai wannan hare-haren da ake kai wa na baya-bayan nan sun da muni.

    Har yanzu sojin Isra'ila ba su ce komi ba kan batun.

  8. Jam'iyyar Imran Khan ta yi Allah wadai da toshe shafin X a Pakistan

    v

    Har yanzu ba a saki sakamakon ƙarshe na zaɓen Pakistan ba, a gefe guda kuma an tashi da tabarin sufe shfin X a ƙasar a safiyar Asabar.

    Hukumar NetBlocks da ke lura da intanet a ƙasar ta tabbatar da rufe shafin na X, tana cewa tun safe ba ya aiki a Pakistan.

    An ɗauke sabis ɗin waya a ranar da aka yi zaɓe a ƙasar kwanaki biyu da suka gabata a duka faɗin ƙasar.

    Jam'iyyar Tehreek-e-Insaf ta Pakistan ta fitar da wata sanarwa a shafinta na X tana Allah-wadai da rufe shafin, ta ce yanzu ana ƙarni na 21 ne irin wannan matakin na son zuciya babu abin da zai haifar sai rashin kwanciyar hankali a ƙasa.

  9. Falasɗinawa a arewacin Gaza na kokawar neman ruwan sha da abinci

    .

    Asalin hoton, MEE

    Dubban Falasɗinawan da suka maƙale a arewacin Gaza na fama da wahalar samun ruwan sha da abinci.

    Wakilin kafar yaɗa labarai ta 'Middle East Eye' a yankin Al-Sahaba da ke makwabtaka da yankin, ɗaya daga cikin wuraren da suka fi yawan jama'a a arewacin Gaza, ya ce Falasɗinawa a yankin na kokawar samun ruwan sha daga wani bututun ruwa da ya fashe, sakamakon hare-haren Isra'ila a yankin, bayan da suka fitar da rai daga samun ruwan sha a garin.

  10. Qatar 1-0 Jordan : An juya hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na yankin Asiya

    f

    An juya hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na nahiyar Asiya na 2023, Qatar na gaba a wasan inda ta doke Jordan da ci daya da nema.

    Afif ne ya ci kwallon a minti na 22 da fara wasan, lokacin da aka bai wa Qatar bugun fanareti.

    Qatar ta samu damar zuwa wasan ƙarshen wasan ne bayan doke Iran da ta yi a wasan kusa da na ƙarshe, ita kuma Jordan bta samu nasara ne a kan Koriya ta Kudu.

    Babu wanda za iya cewa ga yadda wannan wasa zai ƙare har sai an tashi.

  11. An kuɓutar da ƙaramar yarinya sa'o'i 60 bayan zaftarewar laka a Philippines

    .

    Asalin hoton, EPA

    An kuɓutar da wata ƙaramar yarinya da ta maƙale cikin laka, sa'o'i 60 bayan zaftarewar lakar da ta auku a Philippines.

    Masu aikin ceto sun fitar da rai daga samun wani da rai, to amma sun yaba da ceto ƙaramar yarinyar da aka yi ranar Juma'a, inda suka bayyana lamarin da abin ''al'ajabi''.

    A ranar Talata ne aka samau zanftarewar lakar a wajen haƙar ma'adinai a ƙauyen Masara na lardin Davao de Oro da ke yankin Mindanao.

    Jami'ai sun ce mutum 28 ne suka mutu, yayin da kusan 77 suka ɓace.

  12. Hezbollah ta ce ta kama jirgin Isra'ila maras matuƙi

    .

    Asalin hoton, Elbit Systems

    Kungiyar Hezbollah ta ce kwace wani jirgi maras matuƙi na Isra'ila, yayin da yake shawagi a sararin samaniyar Lebanon.

    hezbollah ta ce lami lafiya ta kama jirgin, kuma yanzu haka yana cikin halin lafiya.

    Jirgin mai suna Skylark, na daga cikin jirage marasa matuƙa da Isra'ila ke amfani da su wajen leƙen asiri.

    Kamfanin ƙera mkamai na Isra'ila, Elbit Systems ne ya ƙera jirgin.

  13. Shugabar Tanzaniya na alhinin rasuwar tsohon firaministan ƙasar

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, ta ce ta kaɗu da jin labarin rasuwar tsohon firaministan ƙasar Edward Lowassa.

    Cikin saƙon ta'aziyya da ta wallafa a shafinta na X, Mrs Sulu ta ce mista Lowassa mutum ne mai fikara da basira da Tanzaniya za ta daɗe tana tunawa da shi.

    Shugabar ƙasar da ake yi wa laƙabi da Mama Samia ta ce Mista Lowassa ya kwashe fiye da shekara 35 yana bauta wa Tanzaniya a ɓangarori daban-daban.

    "Mun yi rashin shugaba mai hikima, wanda ya sadaukar da kansa wajen bauta wa ƙasarsa,' kamar yadda Mama Samia ta wallafa.

  14. Lafiya Zinariya: Kan ciwon mara lokacin jinin al'ada

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  15. 'Yansanda sun kama mutanen da ake zargi da safarar ƙananan yara a Abuja

    .

    Asalin hoton, NIGERIA POLICE

    Rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja ta kama wani mutum da take zargi da safarar ƙananan yara kimanin 12 a cikin mota zuwa jihar Ogun.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta kama mutumin ne ranar Juma'a da rana a lokacin da yake safarar ƙananan 12 da suka haɗar da mata takwas da maza huɗu a cikin mota a kan hanyarsa ta zuwa wani wuri a jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.

    Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa ƙananan yaran 'yan tsakanin shekara biyar zuwa 16, dukkansu 'yan asalin ƙaramar hukumar Akwanga ne daga jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.

    'Yan sandan sun zargi wani fasto mai suna Simon Kado da wani mutum guda - waɗanda ta ce suna hannunsu - da hannu a safarar yaran zuwa jihar ta Ogun wa.

    Rundunar 'yan sandan Abujan ta ce tana tuntuɓar takwararta da ke jihar Nasarawa domin shirya yadda za a mayar da yaran wajen danginsu.

  16. Na kamu da cutar tsananin damuwa bayan rabuwa da matata - Zango

    .

    Asalin hoton, Adam Zango/Instagram

    Fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-fina ta Kannywood Adam Zango ya ce ya shiga tsananin damuwa, sakamakon abubuwan da suka taso bayan rabuwarsu da matarsa.

    Cikin tattaunawarsa da BBC a shirin Mahangar Zamani, jarumin ya ce yanzu haka ya ja baya daga harkokin yau da kullum kuma yana nazari domin gano daga ina matsalar take.

    ''Har yanzu ba mu sasanta da matata ba, hasalima yanzu haka ta kusa yin aure'', in ji jarumin.

    Sai da jarumin ya ce maganar da ya yi a baya cewa ba zai sake yin aure ba, ya faɗe ta ne a lokacin da yake cikin fushi, amma yanzu da ya sauko, ya jingine wannan maganar.

    ''Dole ne na yi aure don kare mutuncin kaina, da na 'ya'yana da kuma na mahaifiyata, saboda a yanzu ne nake cika cikakken mutum'', in ji Adam Zango.

    Adam Zango ya ce babban abin da ya haɗa shi da matarsa da ya saki a baya-bayan nan shi ne amfani da shafukan sada zumunta, wanda shi kuma ba ya so.

    Ya ce a karon farko shi ne ya amince ta riƙa amfani da shafukan domin harkokin kasuwancinta, amma ya ce daga baya sai wasu abubuwa suka riƙa faruwa wanda shi kuma yake ganin ba daidai ba ne.

    Jarumin ya ce nan gaba idan zai yi aure abin da zai yi la'akari da shi ne danginta, saboda ya ce yawan auren da ya yi ya sa ya gano cewa ana auren mace ne tare da danginta.

    Adam Zango ya ce babau maganar da ta fi tsaya masa a rai ko take ɓata masa rai ba, irin yadda ake jifansa da siffar mai auri-saki.

    Jarumin ya ce babban burinsa a yanzu bai wuce samun mace tagari ba.

  17. Gasar Afcon: Kashim Shettima zai jagoranci wakilan gwamnatin Najeriya zuwa wasan ƙarshe

    .

    Asalin hoton, X/Kashim Shettima

    Bayanan hoto, Kashim Shettima ya wakilci Tinubu a wasan kusa da na ƙarshe

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙashen na gasar Kofin ƙasashen Afirka (Afcon) da ke gudana a ƙasar Ivory Coast.

    Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan sadarwa, Stanley Nkwocha ya fitar, shugaba Tinubu ya buƙaci tawagar Super Eagles ta Najeriya, ta yi duk mai yiwuwa don sanya 'yan ƙasar alfahari da tawagar a nahiyar Afirka.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya wakilci shugaba Tinubu a wasan kusa da na ƙarshe da ƙungiyar ta doke Afirka ta Kudu a tsakiyar mako.

    Tawagar ta Najeriya dai za ta yi gumurzu da mai masaukin baƙi, Ivory Coast a wasan ƙarshe ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu.

    Ƙasashen biyu dai sun fafata a wasan cikin rukuni a wannan gasar, inda Najeriya ta yi nasara da ci 1-0.

    ''Ƙwallon ƙafa ke taka rawa wajen haɗa kan 'yan ƙasa, kuma rawar da tawagar super Eagles ta taka wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin 'yan Najeriya ya tabbatar da haka'', in Tinubu.

    Shugaban na Najeriya ya ce ya yi imanin zuwa wasan ƙarshen da mataimakinsa da sauran 'yan tawagarsa za su yi, alama ce da ke tabbatar da goyon bayan gwamnatin ƙasar ga tawagar Super Eagles kan sadaukarwa da nasarorin da take yi.

    Haka kuma gwamnatin ƙasar ta yi kira ga 'yan Najeriya da ke ciki da wajen ƙasar da su haɗa kansu wajen nuna goyon baya ga tawagar ƙasar, ta hanyar furta kalaman ƙarfafa wa 'yan wasan gwiwa, domin samun nasara a wasan.

    .

    Asalin hoton, X/Stanley Nkwocha

  18. Bayanai kan wasan ƙarshe a gasar Afcon

    Bayan buga wasa 50, gasar AFCON ta zo ƙarshe yayin da ake shirin gumurzu tsakanin Najeriya da Ivory Coast a ranar Lahadi.

    Da maraicen yau Asabar ne dai za a fafata a wasan neman gurbin na uku tsakanin tawagogin Afirka ta Kudu da DR Kongo.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  19. Zaɓen Pakistan: 'Yan takarar Indifenda da ke samun goyon bayan Imran Khan na kan gaba

    b

    Sakamakon zaɓe a Pakistan na ci gaba da fitowa, bayan zaɓen kujerun 'yan majalisun dokoki 266 da aka gudanar ranar Alhamis.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta ce, har yanzu tana dakon sakamakon kujerun majalisa 12.

    Sakamakon da hukumar ta bayyana ya nuna cewa 'yan takarar indifenda da ke samun goyon bayan tsohon firaministan ƙasar Imran Khan, sun samu kujeru 91, yayin da jam'iyyar PML ta firaministan ƙasar Nawaz Sharif ta samu kujeru 71.

    Sai kuma jam'iyyar PPP da ta samu kujeru 52, da sauran ƙananan jam'iyyu da suka samu kujeru 36.

    Jam'iyyar PTI ta tsohon firaministan ƙasar Imran Khan, ta fitar da wata sanarwa da taimakon fasahar ƙirƙirarriyar basira, inda a ciki aka ga mista Khan na jawabi, duk da yana tsare a gidan yari.

    A cikin sanrawar, mista Khan ya taya magoya bayansa murnar lashe zaɓen da aka gudanar.

  20. Yadda 'yan siyasar Indonesia ke tururuwa zuwa wajen bokaye da masu tsafi

    Indonesia ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan musulmai a duniya, to sai dai duk da haka bokaye da matsubbata na cin karensu babu babbaka a ƙasar.

    A ranar 14 ga watan Fabrairun da muke ciki ne, fiye da al'ummar ƙasar miliyan 200 za su kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen shugaba ƙasar da na 'yan majalisun dokokin ƙasar.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon