Gasar za ta ƙunshi rukuni shida masu ƙunshe da ƙasashe hurhuɗu (A-F) inda ƙasashe biyu na farko za su cancanci zuwa zagayen kifa-ɗaya-ƙwala na ƙasashe 16.
Ƙasashen huɗu da suka fi taka rawar gani a matsayi na uku daga rukuni shida za su shiga cikin ƙasashe 12, inda za a yi amfani da tsarin head-to-head a sakamako da kuma head-to-head na yawan ƙwallayen da aka zura.
Wanda ya gudanar da bincike: Damilola Ojetunde, Tsarawa: Olaniyi Adebimpe, Hadawa: Boaz Ochieng