Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ra'ayi Riga: Kan tsadar rayuwa a Najeriya

    Shirin Ra'ayi riga na wanna makon ya duba batun tsadar rayuwa da ake fuskanta a Najeriya, da kuma matakan da gwamnati ƙasar ke ɗauka don magance matsalar.

    A cikin shirin an tattauna da ministan yaɗa labaran ƙasar da masana fannonin tattalin arziki da 'yan kasuwa da kuma talakawa, wadanda su ne suka fi kowa jin raɗaɗin tsadar rayuwar da ƙasar ke fuskanta.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  2. EFCC na neman matar Emefiele ruwa-a-jallo

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar da ke Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon-ƙasa ta EFCC ta ayyana neman matar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, ruwa-a-jallo.

    Cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar ta ce tana neman Margaret Dumbiri Emefiele, tare da wasu mutum uku bisa laifukan da suka shafi almundahanar kuɗi.

    Sanarwar ta ce hukumar na zargin mutanen huɗu da laifin haɗa baki da tsohon gwamnan babban bankin wajen karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗen gwamnatin Tarayya.

    Tun bayan kama Mista Emifeile ne dai rahotonni ke cewa matar tasa ta riƙa ɓoye kanta.

    Sauran mutanen da hukumar ke nema sun haɗar da wani jami'an babban bankin ƙasar CBN, mai suna Eric Odoh, da Anita Omoile wata 'yar ƙasuwa da kuma Jonathan Omoile wani jami'i a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje.

    Hukumar ta buƙaci 'yan ƙasar da su taimaka mata da bayanan da za su kai ga kama mutanen duk inda aka gansu.

    Tun bayan datakar da tsohon gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, yake ci gaba da tsare a hannun hukumomi bisa zargin almundahanar kuɗi.

  3. 'Sojojin Isra'la sun kama mutane a samamen asibitin Khan Younis'

    Ƙungiyar agaji ta Falasɗinawa ta ce dakarun Isra'ila sun kama mutane a yayin wani samame da suka kai a asibitin Khan Younis da ke kudancin Gaza.

    Ƙungiyar ta ce waɗanda aka kama sun haɗa da likitoci da marasa lafiyar da suka ji rauni da ƴan uwansu.

    Sojojin Isra'ilar sun tabbatar da sun kai samame a asibitin da suka ce Hamas na amfani da shi wajen kai hare-hare.

    Mutane sama da dubu takwas ne ke zaman gudun hijira a asibitin

  4. Sojojin Pakistan sun buƙaci a kawo ƙarshen siyasar fitina a ƙasar

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Babban hafsan sojin Pakistan ya yi kira da a kawo ƙarshen siyasar rashin zaman lafiya a ƙasar.

    Janar Asim Munir ya ce ana buatar tsayayyayen mutumin da zai jagoranci ƙasar.

    Gargain jagoran sojojin asar na zuwa ne a daidai lokaci da duka bmanyan jam'iyyan kasar biyu suka gaza samu gagarumin rinjaye a zaen asar da aka gudanar cikin makon nan.

    'Yan takara masu zaman kansu da ke samun goyon bayan tsohon firayim minista Imran Khan da aka ɗaure, sun lashe mafi yawan kujeru.

    Sojoji na taka muhimmiyar rawa a siyasar Pakistan.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawa kan labaran da muke wallafa a shafukanmu na sada zumunta.

    Mu je zuwa ...