Zaben Pakistan: Jam'iyyun siyasa sun ki amicewa da zabe

Pakistani opposition leader Maulana Fazalur Rehman (2nd R) and Shahbaz Sharif (2nd L), younger brother of Nawaz Sharif, attend an All Parties Conference in Islamabad on July 27, 2018

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugabannin jam'iyyun da ke kan hanyar shan kashi: Shahbaz Sharif na PML-N (Na biyu daga hagu) da Maulana Fazalur Rehman na MMA (Na biyu daga dama)
An wallafa

Wata hadakar jam'iyyun siyasa a Pakistan ta yi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar na ranar Laraba wanda tsohon dan wasan kiriket Imran Khan ke kan hanyar lashewa.

Jam'iiyar Mista Khan ta PTI na kan gaba a zaben kuma tuni ya ayyana cewa shi yayi nasara a zaben.

Sauran jam'iyyu kuma sun ki amicewa da sakamakon wucin gadi da hukumar zabe ta fitar.

Bayan wata ganawa da suka yi a birnin Islamabad, daya daga cikin shugabannin jam'iyyun ya ce za su nemi a sake gudanar da wani sabon zabe.

Jam'iyyun sun hada da tsohuwar jam'iyyar PML-N wadda a baya ita ke mulkin kasar, kuma har ta amince da ta sha kaye a wannan zaben.

Jagoranta Shahbaz Sharif, dan uwan tsohon firai minista Nawaz Sharif wanda ke zaman kaso a kurkuku, ya ce jam'iyyarsa ba ta yanke shawara game da shiga majalisar kasar ba ko a'a.

Ga akaluman zaben a halin yanzu

Jam'iyyar Imran Khan na da kujeru 115 a cikin majalisa mai kujeru 272, inda ita kuma jam'iyyar PML-N ke da 64.

Ita kuma jam'iyyar PPP a karkashin jagorancin Bilawal Bhutto Zardari, dan marigayiya Benazir Bhutto na da kujeru 43.

Amma jam'iyyar ta PPP ba ta halarci taron na hadakar jam'iyyun ba na ranar Jumma'a.

Ana bukatar jam'iyya ta sami kujeru akalla 137 kafin ta iya kafa gwamnati, duk da cewa Mista Khan na kan hanyar zama firai minista, amma sai ya nemi hadin kan wata jam'iyya kenan kafin ya kafa gwamnati.

Supporters of Imran Khan celebrate in Karachi on July 27, 2018

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Imran Khan na cike da murna a birnin Karachi