Isra'ila ta ce tana fadada mamaye ta kasa da matsanancin luguden bam

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Sabbin bayanai kan yaƙin Isra'ila da Gaza

    • Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Hamas, wanda ya taimaka wajen tsara harin na ranar 7 ga watan Oktoba.
    • Rundunar sojin Isra'ila ta kuma ce ta kai hare-hare da dama a kan mayaƙan Hamas a cikin sa'o'i 24 da suka wuce, yayin da ta kai hare-hare a tsakiyar yankin Zirin Gaza.
    • Matsugunan Majalisar Dinkin Duniya a Gaza a yanzu sun ninka karfin da ake so sau uku, in ji Hukumar Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) yayin da babban jami’in jin kai na Majalisar ya yi gargaɗin cewa agajin “da kyar yake shiga."
    • Amurka ta ce ta kai hari kan wasu cibiyoyi guda biyu a gabashin Syria, tana mai cewa sojojin Iran da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da su ne ke amfani da su, amma ta jaddada cewa hare-haren sun bambanta da rikicin Gaza kuma babu wani haɗin kai da Isra'ila.
    • Amurka ta kuma dauki matakin da ba kasafai ba na aika wa Jagoran addini na Iran saƙon kai tsaye, bayan an kai wa sojojinta hari a yankin akalla sau 16 a cikin makon da ya gabata.
    • Shugabannin Tarayyar Turai sun amince da yin kira ga "hanyoyi na jin kai" don samun agajin gaggawa a Gaza.
    • Majalisar Dinkin Duniya za ta kada kuri'a a yau Juma'a don tsagaita wuta nan take a Gaza. Daftarin kudurin ya buƙaci agajin jin kai mara iyaka da kuma bin dokokin jin kai na ƙasashen duniya.
    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
    • Abin da Isra'ila take lissafawa kafin ta auka wa Gaza
  2. Rashin iskar Gas ya haifar da katsewar wutar lantarki a Ghana

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yawancin sassan Ghana na fuskantar matsalar rashin wutar lantarki sakamakon ƙarancin iskar gas da ake buƙata domin samar da injinan samar da wutar lantarki.

    Kamfanin Ghana Grid Company Limited (GRIDCo) ya ba da rahoton wani gagarumin giɓin samar da wutar lantarki na megawatt 550 a cikin sa'o'i mafi yawa a tashar wutar lantarki ta Tema da ke kusa da babban birnin kasar, Accra.

    An fara wannan babbar katsewar wutar lantarkin ne da yammacin ranar Alhamis.

    A halin yanzu Ghana na fama da matsalar tattalin arziki mafi muni a baya-bayan nan, wanda ya ta'azzara saboda yanayin samar da makamashi.

    Wani bincike da aka gudanar a watan Yuni ya bayyana irin mawuyacin halin da ake ciki na samar da wutar lantarki a kasar, lamarin da ke nuni da cewa ana fuskantar matsalar wutar lantarki.

    A cikin watan Yuli, masu samar da wutar lantarki masu zaman kansu a Ghana sun yi barazanar daina aiki saboda rashin biyan basussukan da kamfanin wutar lantarki na kasar ke bin gwamnati.

    Kamfanin samar da wutar lantarki na GRIDCo, ya fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa za a takaita samar da wutar lantarki ga masu amfani da shi a wasu yankuna na kasar saboda karancin iskar gas ga tashar samar da wutar lantarki ta Tema.

    • Abin da ya sa kamfanin dillancin wutar lantarki na Najeriya ya tafi yajin aiki
    • Ana kukan tsadar kaya a Ghana da Najeriya saboda rufe iyakokin Nijar
  3. Amurka ta kai hari cikin Syria

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Amirka sun ce sun kai hare-hare ta sama wurare biyu da sojin juyin-juya-hali na Iran ke amfani da su a Syria.

    A wata sanarwa da sakataren tsaron Amirka ya fitar Lloyd Austin, ya bayyana hare-haren na tsantsar kare kai.

    Sama da mako guda da rabi kenan da sojin Amirka ke zafafa kai hare-hare kan kungiyar masu dauke da makamai da Iran ke marawa baya.

    Sun ce martani ne kan hare-haren da suke addabar sojin Amirka da ke Iraqi da Syria hare-hare.

    Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce an kai wa kawancen da Amirka ke jagoranta a Iraqi da Syria hari sama da sau 16 cikin wannan watan, daidai lokacin da ake zaman dar-dar a yankin gabas ta tsakiya saboda yakin Isra'ila a Gaza.

    • Amurka ta kai hari kan mayakan Iran a Iraki da Syria
    • Ta waɗanne hanyoyi Iran za ta iya shiga yaƙin Isra'ila da Gaza?
  4. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu, barkan mu da safiyar Juma'a

    Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi na kai tsaye, BBC Hausa domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntarmu domin yin muhawara kan labaran da muka wallafa

    Ku biyo ni.