Isra'ila ta ce tana fadada mamaye ta kasa da matsanancin luguden bam

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Sojojin Isra'ila sun ce Hamas na amfani da asibitoci a Gaza don 'kaddamar da yaki'

    IDF

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Daniel Hagari ya ce Hamas tana shirya hare-harenta ta hanyar amfani da wasu hanyoyin karkashin kasa da ke karkashin asibitoci kamar Al Shifa

    Mun saurari wani jawabi daga mai magana da yawun rundunar tsaro ta sojojin Isra'ila (IDF), Daniel Hagari.

    Ya ce Hamas "na kaddamar da yaki daga cikin asibitoci" a Gaza ta hanyar amfani da irin wadannan wurare a matsayin "cibiyoyin ajiye kayan ta'addanci".

    Ya yi magana takamaimai a kan asibitin Al Shifa, mafi girma a Zirin Gaza. Ya bayyana wata gagarumar hanyar karkashin kasa mai sarkakiya a kasan ginin wanda ke birnin Gaza, wanda daga wurin ya ce ana iya shirya yadda za a kai hare-hare.

    Daniel Hagari ya ce "daruruwan 'yan ta'adda suna tserewa cikin asibitin don buya a can" bayan hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba, kuma ya ce Isra'ila na da bayanan sirri da ke nuna cewa "akwai man fetur a asibitocin Gaza, sannan Hamas tana amfani da shi don harkokin ta'addancinta".

    Ya kara da cewa Hamas ta yi haka ne saboda, a cewarsa, rundunar sojojin tsaron Isra'ila tana rarrabewa tsakanin "'yan ta'adda da fararen hula" a hare-harenta. Sabanin haka, a cewarsa Hamas tana cutar da 'yan Isra'ila da kuma fararen hulan Gaza.

    • Yadda mutane ke dogon layin karɓar gurasa a Gaza
    • Iyalan 'yan Isra'ila da Hamas ta kama sun yi zanga-zangar neman sakinsu
  2. Gwamnati ba za ta tsoma baki a zaɓukan Bayelsa da Imo da Kogi ba - Ribadu

    NSA

    Asalin hoton, X/Nuhu Ribado

    Bayanan hoto, Mallam Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro

    Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta yi katsalandan a zaɓukan jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo ba, da ke tafe cikin watan Nuwamba.

    Ribadu, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a lokacin wani taro da shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Mahmood Yakubu, tare da sauran kwamishinonin zaɓen da sauran masu ruwa da tsaki a sabgar zaɓen.

    Ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu na cike da fatan gudanar da sahihin zaɓe a waɗannan jihohi.

    “Wannan zaɓuka za su kasance mafiya tsafta fiye da na baya. za su gudana ba tare da rigima ba, za su kasance sahihan zaɓukan da babu katsalandan a cikinsu,” in ji Ribadu.

    Ya kuma ce shugaban ƙasa a shirye yake ya goyi bayan hukumar don samun nasarar hakan.

    An gudanar da taron ne a ofishinsa a wani ɓangare na tuntuɓa da hukumar ke yi gabanin zaɓukan da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

    Tun da farko INEC ta nuna fargabar tsaro gabanin zaɓukan, a wani taro da ta gudanar da jam'iyyun siyasa.

    A nasa ɓangare shugaban INEC, ya bayyana fargabarsa kan tsaron lafiyar masu kaɗa ƙuri'a da tsaron kayayyakin zaɓe masu muhimmanci, tare da tsaron cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

    Ya yi kira ga jami'an tsaro su yi maganin duk wanda ya yi yunƙurin tayar da zaune-tsaye a ranar zaɓen.

  3. Rikicin Sudan: RSF ta ƙwace iko da birnin Nyala a yankin Darfur

    .

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar dakarun tsaro masu sanye da kayan karki na RSF a Sudan ta ƙwace iko da birnin Nyala, birni na biyu mafi girma a ƙasar .

    RSF ta ƙwace iko da birnin daga hannun dakarun sojin ƙasar bayan shafe watanni ana gwabza yaƙi, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa BBC.

    Wani shaida a yankin ya ce mazauna birnin na cike da murna, saboda suna fatan hakan zai kawo ƙarshen rikicin yankin.

    Rikicin ya tilasta wa fiye da mutum 670,000 barin gidajensu.

    An lalata asibitocin birnin, inda rohotonni ke cewa an yi ta ganin gawarwaki zube a kan titunan birnin.

    Ƙwace birnin da RSF suka yi na zawa ne, yayin da ɓangarorin da ke faɗa da juna ke shirin komawa teburin sulhu a ƙasar Saudiyya.

    Kawo yanzu rundunar sojin ƙasar ba ta ce komai ba game da cin galabarta a birnin Nyala.

    Nyala - wanda shi ne babban birnin jihar Darfur ta Kudu - shi ne birnin da ke kan iyakar Sudan da ƙasar Jamhuriyar tsakiyar Afirka.

    RSF ta samo asali ne daga Darfur, inda aka zarge ta da laifukan cin zarafin ƙungiyoyin da ba na Larabawa ba a yankin, lokacin yaƙin na wannan yaƙin.

    A 'yan makonnin da suka gabata ne aka kashe manyan sojoji a birnin ciki har da shugaban rundunar sojin ƙasar a birnin.

    • Hanyoyi uku da za a iya kawo ƙarshen rikicin Sudan
    • Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikicin Sudan
  4. Bidiyo ya nuna barnar da hari ya yi wa ginin Tel Aviv

    Wani jami'i a Tel Aviv ya ce an jikkata mutum hudu bayan wani harin roka da ya fada a kan wani gini mai hawa hudu a birnin.

    Dany Geva, mataimakin kwamandan na rundunar tsaron cikin gida ta Tel Aviv, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutum sun ji matsakaitan raunuka, sai biyu da suka ji 'yan kananan raunuka sanadin makamin roka.

    Ya ce an harbo makamin ne daga Zirin Gaza, nisan kimanin kilomita 64.

    "Dalilin da ya sa ba mu sanu wani da ya mutu ba, a iya fahimtata ga wannan lamari, shi ne saboda mutane sun yi abin da aka umarce su. Sun saurari jiniya... sun sauka kasan bene kuma an kubutar da rayuka."

    Dubi bidiyo na baya-bayan nan daga wurin da abin ya faru a nan kasa:

  5. Ƙungiyoyin ƴan tawayen ƙabilu uku sun kai hare-hare arewacin Myanmar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyoyin ƴan tawaye na ƙabilu uku a Myanmar sun ce sun ƙaddamar da hare-hare kan sojojin da ke mulki a arewacin ƙasar.

    Rahotanni sun ce 'yan tawayen sun kwace iko da wani sansanin soji a garin Chin Shwe Haw da ke kusa da kan iyaka da China a jihar Shan.

    Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar 'yan tawayen suka mamaye wata cibiyar gwamnati tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2021.

    Kungiyar ta ce manufarta ita ce ta gurgunta ikon da sojojin ke yi na kai hare-hare ta sama a yankin da kuma hana aikawa da ƙarin sojoji.

    A baya-bayan nan dai masu tada ƙayar bayan sun yi watsi da gayyatar da gwamnatin sojin ƙasar ta yi musu na tsagaita wuta.

  6. An zaɓi Sultan Ibrahim a matsayin sabon sarkin Malesiya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Malaysia ta zaɓi Sultan Ibrahim na jihar Johor da ke kudancin ƙasar a matsayin sabon sarkinta.

    Sarakunan ƙasar tara ne suka zaɓi Sultan Ibrahim a taron sarakunan ƙasar da aka yi ranar Juma’a kuma za a naɗa shi a ranar 31 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.

    Sultan Ibrahim ya yi fice da bayyana ra’ayinsa kan siyasa kuma yana da kyakkyawar alaƙa da Firaminista Anwar Ibrahim.

    Bugu da ƙari, yana jagorantar wasu dakaru masu zaman kansu kuma ɗan kasuwa ne a ɓangaren gine-gine da ma'adanai

    An zaɓi sarkin - wanda shi ne shugaban ƙasa a tsarin dimokuraɗiyyar majalisar dokokin Malaysia - a cikin wani tsari na musamman da shugabannin iyalan gidan sarautar ƙasar waɗanda ke kan gaba wajen zama sarki na tsawon shekaru biyar.

  7. Neuer na shirin dawowa bayan jinyar wata 10

  8. Amurka ta ce harin da ta kai a Syria bai da alaƙa da yakin Isra'ila da Gaza

    Amurka ta ce hare-haren da ta kai ta sama a kan wasu wurare a Syria da ke da alaƙa da dakarun kare jagoran addini na Iran ba shi da alaƙa da rikicin Isra'ila da Hamas.

    Sakataren tsaro Lloyd Austin ya ce Amurka na mayar da martani ne kan hare-haren da kungiyoyin mayaka masu samun goyon bayan Iran suka kai wa dakarunta a Iraƙi da Siriya.

    Ya ce Washington ba ta da sha'awar shiga wani tashin hankali don haka ya buƙaci dukkan sojojin jihohi da su guji ɗaukar matakin da zai iya rikidewa zuwa wani babban rikici na yanki.

  9. 'Mutum uku sun jikkata a harin da aka kai Tel Aviv'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa mutum uku sun jikkata a wani hari da aka kai Tel Aviv, babban birnin Isra'ila.

    Reuters ya ce mutanen sun jikkata sakamakon wani harin roka da ya faɗa kudancin birnin.

    Za mu kawo muku cikakkun bayanai game da harin, da zarar mun same su.

  10. Messi na iya lashe lambar yabo a MLS

  11. Ƙungiyar masu kiwon kaji a Kano ta ƙara farashin ƙwai

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin kwai sakamakon tashin gwauron zabin da abincin kajin ya yi.

    Ƙungiyar ta ce bayan nazari da lissafin da mambobinta suka yi kan yadda suke tafiyar da sana'ar tasu, sun cimma matsayar sanar da sabon farashi inda ta ƙara da cewa abincin kaji mai iganci a yanzu ya haura naira 11,000 a kan ko wanne buhu.

    Shugaban ƙungiyar, dakta Usman ya ce idan ba su ƙara farashin ƙwan ba, babu riba.

    Ya kuma jadadda cewa sabon farashin shawara ce da suka bai wa junansu, ba umarni ba.

    Masu kiwon kajin sun ce babban abin da ake hada abincin kajin da shi, wato masara ta yi tsada, lamarin da ya sa wasu ma ke dakatar da aiki.

    Za ku iya sauraron rahoton Zahraddeen Lawan daga kano kan wannan batu.

    • Sauyin yanayi: Labarin tsuntsayen da suka jinkirta yin kwai da mako uku
    • Abin da ya kamata ku sani kan ƙirƙirar kazar da za ta dinga haifar kaza zalla
    Bayanan sautiLatsa hoton sama don sauraron cikakken rahoto
  12. 'Sama da kashi 40 na waɗanda aka kashe a Gaza yara ne'

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da rahoton mutuwar mutum 7,028, yayin da sama da kashi 40 cikin 100 yara ne a Gaza.

    Sun kuma rubuta raunuka 18,482, gami da adadi mai yawa na yara ne.

    Yawancin asibitoci suna aiki a wani bangare, kuma rashin man fetur na janareta yana kawo cikas ga mahimmancin kula da lafiya ga marasa lafiya gami da masu buƙatar wankin ƙoda da jariran da ba su kai haihuwa ba da suke cikin kwalbar incubator da kuma masu ciwon daji.

    • Yadda gawawwaki suka mamaye asibitocin Gaza
    • Iyayen 'yan Isra'ila da ke hannun Hamas sun yi roko ga al'ummar duniya
  13. Wasu ƙarin motoci 10 dauke da kayan agaji sun shiga Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    An bai wa wasu ƙarin ayarin motocin da ke dauke da muhimman kayayyaki kamar ruwa da abinci da magunguna damar shiga Gaza.

    Rahotanni kamfanin dillancin labarai na Reuters wanda wani jami'in kan iyakar Falasɗinawa ya fara bayyanawa sun nuna cewa wannan ayarin da suka hada da motocin agaji guda goma, na tare da tawagar likitoci.

    Jami'in ya bayyana cewa, a safiyar yau Juma'a, tawagar likitocin da ta kunshi likitoci 10 na kasashen waje sun shiga, baya ga manyan motoci 10 da suka shiga yankin Zirin Gaza ta mashigar Rafah, dauke da ruwa da abinci da kuma magunguna, wanda ya kawo jimillar manyan motocin tun daga lokacin farkon yakin zuwa manyan motoci 84 kawai."

    Duk da cewa an ba da izinin shiga yankin a makon da ya gabata, ƙungiyoyin agaji sun sha nanata buƙatar gaggawa na neman ƙarin taimako domin tunkarar mummunan halin jin kai a Gaza.

    • Za a shigar da kayan agaji zuwa Gaza
    • Malaman cocin da suka ce yaƙi ba zai sanya su guje wa Gaza ba
  14. Rana ta 20 na yaƙin Isra'ila da Gaza

    Ga wasu hotuna daga Isra'ila da Gaza, yayin da rikicin da ake fama da shi a yankunan ya kusa cika makwanni uku.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Matan Falasɗinawa na jimamin mutuwar ‘yan uwansu a asibitin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A Gaza, ma’aikatan agajin gaggawa na duba cikin ɓaraguzan gidaje suna neman gawarwaki
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Tankokin sojin Isra'ila sun shiga wani atisaye a kusa da iyakar kasar da Lebanon
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wasu ayarin motocin dakon kaya dauke da kayan agaji domin shiga yankin zirin Gaza daga Masar ta kan iyakar Rafah.
  15. Kalaman mawaki Rarara sun tayar da kura a Najeriya

    Dauda Kahutu Rarara

    Asalin hoton, Dauda Kahutu Rarara/Facebook

    Kalaman fitaccen mawakin siyasar nan a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara na ci gaba da tayar da kura a cikin ƙasar bayan da ya fito ya soki irin salon mulkin da tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi.

    Wani bidiyon mawakin da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuno shi yana cewa sai da "Buhari ya kashe ƙasar kafin miƙa ga shugaba Tinubu."

    Ya ce ya yi da-nasanin gudummawa da ya bai wa tsohon shugaban ƙasar.

    "Na yi da-na-sani saboda kyakkawan zaton da na yi wa Buhari na kawo gyara a Najeriya. Amma ba mu ga haka ba har ya gama mulki," in ji Rarara.

    Ya ce Buhari ya kashe kowanne fanni a ƙasar kafin ya miƙa mulki ga gwamnatin da ke kai a yanzu.

    "Duk wata ma'aikata ko hukuma gwamnatin Buhari ta kasheta, sai an motsa ta take motsi," a cewar mawakin.

    Ya kuma ce kwana 100 na gwamnatin Tinubu, ta fi ta shekara takwas ɗin mulkin Buhari.

    Dangane da batun naɗa ministoci a gwmanatin Tinubu kuwa, Rarara ya ce kafin naɗa su ya kamata a nemi shawararsa.

    "Idan har ba a ba ni muƙamin minista ba, to ya kamata a ce an kira ni an zauna da ni, sannan an zaɓi waɗanda za a bai wa mukaman ministoci da ni," in ji Rarara.

    "Ni na wuce a ba ni muƙami ɗaya sai dai muƙamai. Ni ba wanda za a yi gefe da ni ba ne, dole a dama da ni," in ji shi.

    Sai dai kalaman na Rarara sun haifar da martani daga angarori da dama.

    Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan kafafen yaɗa labaru na zamani, Malam Bashir Ahmad, ya kwatanta kalaman mawakin a matsayin "marasa kan-gado".

    "Maganganunsa sun saɓa hankali da tunani. Babu hikima a cikinsu ko kaɗan."

    Game da wakokin da ya yi wa Buhari, Bashir ya ce Rarara bai taɓa yi wa tsohon shugaban ƙasar waka kyauta ba, ba tare da an biya shi hakkinsa ba.

    Dauda Kahutu ɗaya ne daga cikin mawaƙan arewacin Najeriya waɗanda suka yi fice a harkar siyasa.

    Kuma a cikin shekarun nan ya kan alaƙanta kansa da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.

    Ya rera waƙoƙi na goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari waɗanda suka yi tashe, sannan ya rera wa shugaban ƙasar mai ci, Bola Ahmed Tinubu waƙoƙi na nuna goyon baya tun lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma bayan samun nasara.

    • Dauda Kahutu Rarara: Ba zan sake yi wa Buhari waƙa ba sai talakawa sun ba ni naira dubu ɗai-ɗai
    • 'Yan Kannywood na mayar da martani kan hana su amfani da kayan 'yan-sanda
  16. Dakarun Isra'ila sun ce sun kai hari sama da 250 a cikin sa'o'i 24

    A halin yanzu dai wani karin bayani daga Dakarun tsaron Isra'ila ya nuna cewa sun kai hari sama da 250 a Zirin Gaza a cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

    Dakarun sun bayyana hakan ne a dandalin sada zumunta ta X inda suka ƙara da cewa hare-haren sun hada da ramuka da dama na mayaƙan Hamas da hedkwatar aikinsu da kuma wuraren harba jiragen yaƙi.

    • Me ya sa alaƙar Iran da Hamas ke da ƙarfi?
    • Rikicin Gaza na rura wutar tunzuri a manyan makarantun Amurka
  17. Ƙungiyoyi a Nijar za su maka Tinubu a kotu

    ...

    Asalin hoton, BOLA TINUBU/FACEBOOK

    Wasu kawancen ƙungiyoyin fararen hula a Jamhuriyyar Nijar sun bayyana aniyar kai karar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kotun tarayyar Afirka da kuma wasu shugabannin kasashen Ecowas kan takunkuman da aka kakaba wa Nijar.

    Kungiyoyin farar hular sun kuma nemi al'umma ƙasar su kai masu rahoto kan duk wani nasu da ya rasa ransa ta dalilin takunkunmin kungiyoyin ECOWAS bayan juyin milkin da sojoji suka yi.

    Za ku iya sauraron rahoton Tchima Illa Issoufou kan wannan labarin.

    • Shin Ecowas ta fara ba da kai ga sojojin Nijar ne?
    • Bola Tinubu: Yabo da suka bayan kwana 100
    Bayanan sautiLatsa hoton sama don sauraron rahoto
  18. Kotu ta haramta neman jinsi guda tsakanin sojojin Koriya ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun tsarin mulkin kasar Koriya ta Kudu ta amince da wata doka da ta haramta neman jinsi daya a tsakanin sojoji, a wani mataki da masu fafutuka suka kira koma baya ga 'yancin ƴan luwaɗi da maɗigo

    Kotun ta ce dangantakar da ke tsakanin neman jinsi ɗaya na iya cutar da shirye-shiryen yaki da kuma lalata tarbiya.

    Aikin soja wajibi ne a Koriya ta Kudu, kuma ana buƙatar dukan maza masu shekaru tsakanin 18 zuwa 28 su yi aiki na kusan watanni 20.

    Masu fafutuka suna jayayya cewa wannan hukuncin yana ci gaba da cin zarafi da nuna wariya ga sojojin ƴan luwadi.

    Kotun a hukuncin da ta yanke ta goyi bayan sashe na 92-6 na dokar sojin ƙasar.

    Dokar bata fito ƙarara ta ce an haramta saduwa tsakanin masu jinsi guda ba amma ta ce luwaɗi da duk wani aikin rashin ɗa'a haramun ne ga aɗanda suke aikin soji.

    Wannan dai shi ne karo na hudu tun shekara ta 2002 da kotun ta amince da wannan doka, wadda ta shafi zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu.

    Ba a san auren jinsi ɗaya ba kuma ana ganin luwaɗi a wasu lokuta a matsayin naƙasa ko ma rashin lafiya a Koriya ta Kudu.

    • Manyan malaman addinai sun yi kira a haramta sauya ‘yan luwadi da madigo
    • Yadda aka yi wa ɗan luwadi rukiyya don sauya daɓi’arsa
  19. Mun gode wa jam'iyyun hamayya da suka kai mu kotu – Ganduje

    ..

    Jam`iyyar APC mai mulkin a Najeriya, ta ce nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a Kotun Koli nasara ce ga dimokuraɗiyya da kuma al`ummar Najeriya.

    Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje shi ya bayyana haka a hira da BBC.

    Ya ce wannan nasara ce ga Najeriya ba APC ko sauran jam'iyyu kaɗai ba.

    "Ƴan siyasa sun yarda a koma ɓangaren shari'a domin bin kadinsu maimakon a tayar da yamutsi. Dole mu gode wa ƴan hamayya da kuma kowa da kowa," in ji Ganduje.

    Shugaban jam'iyyar ta APC ya ce da ma sun san nasara tasu ce saboda sun ga alamun haka tun da farko.

    "Mun ƙara samun ƙwarin gwiwa da wannan nasara da muka yi a Kotun Koli," in ji shi.

    Ya ce gwamnatinsu za ta ci gaba da ayyukan raya ƙasa da ta faro ba kama hannun yaro.

    Ya yi kira ga sauran jam'iyyu da ƴan takara da cewa su zo a haɗa kai wajen ciyar da ƙasa gaba.

    A jiya Alhamis ne Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron korafin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke cewa Bola Tinubu ne ya samu nasara a zaɓen shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.

    • Wanne zaɓi ya rage wa Abba Kabir Yusuf a Kano?
    • Manyan ƙalubale huɗu da ke gaban Ganduje
  20. Yawan ƴan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su sun kai 226

    ...

    Hukumomin Isra'ila sun fitar da sabbin bayanai wadanda suka nuna cewa mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza sun kai 226 tun lokacin da aka kama su a ranar 7 ga watan Oktoba.

    Daniel Hagari, kakakin rundunar tsaron Isra'ila ne ya sanar da hakan.

    Kawo yanzu kungiyar Hamas ta saki wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su.

    • Mutanen da ƙungiyar Hamas ke garkuwa da su tsawon shekaru
    • Yadda sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa