Isra'ila ta ce tana fadada mamaye ta kasa da matsanancin luguden bam

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa Kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman kan rikicin Isra'ila da Hamas.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa.

    Mukhtar Adamu Bawa tare da Abdullahi Bello Diginza, ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Ma'aikaciyar agaji ta ce asibitoci na dab da komawa hanyar 'gargajiya'

    Kungiyar Agaji ta Red Crescent ta Falasɗinawa, ta jaddada wa BBC cewa an katse hanyoyin sadarwa a Gaza.

    Yayin ya take magana daga Ramalla, da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, mai magana da yawun ƙungiyar, Nebal Farsakh, ta ce "Muna cike da fargabar halin da abokan aikinmu ke ciki a Gaza, sakamakon ci gaba da kai hare-hare bom".

    Misis Farsakh, ta ce kula da marasa lafiya zai koma hanyar "gargajiya".

    "Muna fuskantar rasa man fetur cikin sa'o'i masu zuwa, ba za mu samu damar duba marasa lafiya a Gaza ba, sakamakon rashin man fetur da motocin ɗaukar marasa lafiya za su yi amfani da shi,'' in ji ta.

    Ta yi gargaɗin cewa mutanen da ke rayuwa ta hanyar taimakon iskar oxygen "za su rasa rayukansu", saboda na'urorin da ke bayar da iskar za su daina aiki sakamakon rashin wutar lantarki.

  3. 'Yan sanda sun kama matashi kan zargin kashe wata mata mai 'ya'ya takwas a Gombe

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi mai shekara 18, bisa zargin kashe wata uwa mai 'ya'ya takwas.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar , ASP Mahid Abubakar, ya ce sun samu rahoto daga wani mutum mai suna Muhammad Abdullahi, mai shekara 45, da ya ce wani mutum ya kashe mahaifiyarsa da wuƙa

    ASP Abubakar, ya ce rundunar 'yan sandan ta tura jami'anta da ke Pantami, inda lamarin ya faru, inda aka samu matar mai shekara 58 kwance cikin jini.

    Daga nan aka garzaya da matar, mai suna Aishatu Abdullahi babban asibitin koyarwa na jami'ar Gombe, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta

    Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da jami'an tsaron ke tuhumarsa.

    ''Ya bayyana yadda ya lallaɓa ya shiga ɗakin matar domin neman sifanarsa da ya ce ta ƙwace masa. bayan da ta shiga ɗakin ta same shi, sai ta tambaye shi dalilin shigarsa ɗakinta, amma ya ƙi ficewa daga ɗakin, a maimakon haka sai ya far mata, ya shaƙe ta tare da kashe ta da wuƙa, daga nan ya yi ficewarsa, ya bar wuƙar da rigarsa da jini ya taɓa, amma kuma ya fita da sifanar", kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan ya bayyana.

    ASP Abubakar, ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin ne da taimakaon wani matashi mai shekara 17.

    Wanda shi ma rundunar ta kama shi, amma kuma ya musanta hannu a aikata laifin.

  4. Bidiyon da ake dauka kai tsaye ya nuna karin fashe-fashen bam da dama a Gaza

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an samu karin fashe-fashen bam a wurare da dama na Gaza.

    Ga abin da zuwa yanzu muka gani:

    Bayanan bidiyo, Bidiyo ya nuna karin fashe-fashen bam wurare da dama a Gaza
  5. Labarai da dumi-dumi, Babban Zauren MDD ya kada kuri'ar neman tsagaita wuta nan take a Gaza

    Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince – da gagarumin rinjaye – ga wani kuduri da ke neman tsagaita wuta nan take bisa muradan ayyukan jin kai a Gaza.

    Kudurin – wanda kasar Jordan ta gabatar a madadin rukunin kasashen Larabawa – ya kuma yi alla-wadai da dukkan wasu ayyukan tarzoma a kan fararen hula na Falasdinawa da Isra'ila ciki har da dukkan "hare-haren ta'addanci da kuma hare-haren ba-ji-ba-gani".

    Kudurin ya yi kira a bai wa fararen hula kariya sannan a shigar da kayan agaji ba tare da iyaka ba.

    An kada kuri'a 120 ta amincewa, sai kasashen duniya 14 da suka ki nuna goyon baya, yayin da 45 suka kaurace.

    Kudurorin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ba lallai ba ne bisa doka a yi aiki da su, amma suna dauke da alhakin sanin ya kamata ga daukacin mambobin Majalisar.

  6. 'A yi wa masu raunin harbin bindiga magani ba tare da rahoton 'yan sanda ba'

    .

    Asalin hoton, Facebook/Nigerian Police

    Bayanan hoto, Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun

    Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya bayar da umarnin wajibcin yi wa masu raunin harbin bindiga aiki, ba tare da jiran rahoton 'yan sanda ba.

    Cikin wata sanarwar da rundunar ta aike wa manya da ƙananan mataimakn sifeton 'yan sandan da kwamishinonin 'yan sanda da shugabanin kwalejojin 'yan sanda na ƙasar.

    Egbetokun, ya ce umarnin ya zama wajibi la'akari da dokar aikin 'yan sanda ta 2017 da ta wajabta yi wa masu raunin harbin bindiga aiki.

    Dokar, wadda ta fara aiki a shekarar 2018, ta wajabta wa duka cibiyoyin lafiya karɓar masu raunin harbin bindiga domin gaggauta yi musu aiki, ba tare da rahoton 'yan sanda ba.

    “Babban Sifeton 'yan sanda ya bayar da umarnin tattaunawa a kan wannan batu, tare da yaɗa shi ga sauran al'umma, domin su samu masaniya kan yadda muke bin doka,' kamar yadda sanarwar ta bayyana.

  7. Shugaban MDD ya ce "wannan lokaci ne na fadar gaskiya' kuma ya yi kira a tsagaita wuta

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gueterres ya wallafa a shafin X dazu, inda yake kira a tsagaita wuta, yana cewa "wannan lokaci ne na fadar gaskiya".

  8. Amurka za ta goyi bayan dakatar da fada don fitar da mutanen da ake garkuwa da su - Kirby

    Mai magana da yawun harkokin tsaron kasa a Amurka John Kirby ya ce Amurka za ta goyi bayan sassauta fada don taimakawa wajen fitar da mutanen da ake garkuwa da su a Gaza - kuma a bar karin kayan agaji su shiga.

    "Za mu ba da goyon baya ga dakatar da fada don shigar da kayan agaji, da kuma fitar da mutane daga cikin zirin, kuma a ciki har da tura man fetur don ya shiga ciki da kuma dawo da wutar lantarki," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

  9. Hare-haren na ƙara zafafa a Gaza da maraice

    Rahotonnin da ke fitowa daga Gaza na cewa Isra'ila ta ci gaba da zafafa kai hare-haren boma-bomai ta sama a Gaza, yayin da layukan intanet da na wayoyin sadarwa suka katse a yankin.

    Kawo yanzu babu wani bayani karara a kan ko wannan wani matakin share fage ne ga wasu hare-haren kasa, ko kuma a'a; rahotannin farko-farko sun nuna cewa ana ci gaba da samun tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta mai alaka da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

  10. Bidiyo na nuna yadda ake ci gaba da harba rokoki daga Gaza

    Dazu-dazun nan, wani bidiyo da ake dauka kai tsaye ya nuna rokokin da ake harbawa daga Birnin Gaza. Mun kuma ga gagaruman fashe-fashe a dai wannan bidiyo.

    Bayanan bidiyo, Ana nuna yadda ake harba rokoki daga Zirin Gaza

    Hamas tana ci gaba da kai hare-haren rokoki kan wurare a Isra'ila yayin da rundunar sojin Isra'ila ta kaddamar da luguden bama-bamanta a Gaza, tun bayan hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba.

    Kamar yadda muke kawo rahoto, Isra'ila ta ce tana fadada hare-haren mamaye ta kasa a daren nan.

  11. EFCC ta tsare Emefiele bayan DSS ta sake shi

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Yaƙi da yi wa Tatalin Arzikin Najeriya Ta'annati (EFCC) ta tsare tsohon gwamnan Babban Bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

    EFCC ta kama Emefiele ranar Alhamis da daddare, ƙasa da sa'a guda bayan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake shi.

    Rahotonni ne cewa EFCC na ci gaba da yi wa tsohon gwamnan na CBN tambayoyi, a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

    EFCC na tuhumar Emefiele kan zarge-zargen saɓa ƙa'idar aiki a lokacin da yake gwamnan CBN.

    Cikin watan Yuni ne dai hukumar DSS ta kama Emefiele jim-kaɗan bayan shugaban ƙasar Bola Tinubu ya dakatar da shi daga aiki.

  12. Isra'ila ta ce dakarunta na ƙasa za su 'faɗaɗa hare-hare cikin dare'

    Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari, ya ce dakarunta sojin ƙasa na kasar, za su faɗaɗa kai hare-hare ta sama cikin dare.

    Cikin jawabin da ya yi a wani taron manema labarai da ya gabatar , Mista Hagari ya buƙaci mazauna birnin Gaza da su fice zuwa kudancin birnin.

    Ya kara da cewa dakarun ƙasarsa sun faɗaɗa hare-haren da suka kai wa a Gaza.

  13. Kotun ƙararrakin zaɓe ta tabbatar da nasarar Wamakko

    .

    Asalin hoton, Wamako/Facebook

    Bayanan hoto, Sanata Wamako

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a Sokoto ta tabbatar da nasarar sanata Aliyu Wamakko na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen sanatan Sokoto ta Arewa.

    Babban abokin hamayyarsa a zaɓen, Manir Mohammed Dan’Iya, na jam'iyyar PDP ne ya shigar da ƙara gaban kotun, yana ƙalubalantar nasarar Wamakko, kan zargin amfani da takardun bogi, da rashin takardun shaidar karatu.

    Cikin hukuncin da alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Josephine Oyefeso suka yanke, sun yi watsi da ƙarar, kan rashin gamsassun hujjoji daga ɓangaren mai ƙara.

    A ranar Alhamis ne dai kotun ta tabbatar da nasarar Sanata Aminu Waziri Tambuwal na PDP, a matsayin sanatan Sokoto ta Kudu.

  14. Bidiyon da ke nuna gagarumar fashewa a Zirin Gaza

    Bayanan bidiyo, An shaida fashe-fashe mafi karfi a Zirin Gaza

    Rundunar sojojin Isra'ila ta fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tana "ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza".

    Wani rukunin ma'aikatan BBC a Ashkelon da ke kudancin Isra'ila, wanda ke da nisan kilomita goma daga Gaza, ya ce ya jiyo rugugin fashe-fashen abubuwa.

    Rukunin ya ce fashewar ita ce mafi karfi idan an kwatanta da hare-haren da aka saba ji da maryace a baya kuma ya bayyana lamarin a matsayin "wani luguden wuta mai karfi kuma akasari ta sama".

  15. Dole ne Ivanka Trump ta ba da shaida a shari'ar almundahana da ake yi wa mahaifinta

    Ivanka Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Lauyoyin Ivanka a baya sun ce babu wajabcin bayyanarta a gaban kotu kan shari'ar neman hakki ta birnin New York

    Ivanka Trump za ta bayar da shaida a shari'ar almundahanar kasuwanci a kan mahaifinta da 'yan'uwanta, kamar yadda wani alkalin New York ya yanke hukunci.

    A baya ta nemi ba za ta tsaya a gaban kotu ba, inda ta ce ba ta cikin birnin kuma ta sauka daga mukaminta na Rukunin Kamfanonin Trump.

    Sai dai alkali Arthur Engoron ya ce har yanzu tana da alaka da harkokin kasuwancin Trump da kuma rukunin gidajensa na New York.

    Tuni dai ya yanke hukuncin cewa Donald Trump ya zuzuta darajar kadarorinsa don ya samu basuka a mataki mafifici.

    Shari'ar na mayar da hankali ne a kan sauran ikirari guda shida da aka yi a cikin karar, ciki har da kantara karya cikin bayanan kasuwanci da tafka almunhadanar inshora da kuma shirya makarkashiya.

    Wadanda ake kara sun musanta zarge-zargen.

    Masu shigar da kara sun yi musun cewa Ivanka Trump na da muhimman bayanai da za ta iya bayarwa game da shari'ar.

    A hukuncin da ya yanke ranar Juma'a, Mai shari'a Engoron ya amince da bahasin masu shigar da karar, inda ya rubuta cewa: "Misis Trump a bayyane take karara, ta gabatarwa da kanta alfarmar gudanar da harkokin kasuwanci a New York."

    Ya kafa hujja da takardun da ke nuna cewa har yanzu tana mallaka ko kuma tana da alaka da shugabanci kan wasu harkokin kasuwanci a New York, kuma har yanzu tana mallakar dogon benen Manhattan.

    Lauyoyin Ivanka sun yi musun cewa babu wajabcin shari'a a kanta na bayar da shaida, don kuwa ta sauka daga mukami a rukunin kamfanonin Trump a 2017, kuma tun daga nan ta koma Florida.

  16. Hamas ta musanta amfani da asibitoci don ƙaddamar da hare-hare

    ƙungiyar Hamas ta musanta batun da rundunar sojin Isra'ila ta yi cewa ƙungiyar na amfani da asibitoci a Zirin Gaza a matsayin sansanoni domin shirya hare-hare.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani mamban ƙungiyar na cewa Isra'ila ta yi wannan zargi ne domin ''fakewa da shi don ƙaddamar da sabbin hare-haren kisan kiyashi kan mutane".

  17. Tsohon firimiyan China da Shugaba Xi ya mayar da shi gefe ya rasu

    Li Keqiang

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon firimiyan China, Li Keqiang ya mutu sakamakon bugun zunciya.

    Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce Mista Li, mai shekara 68, ya mutu ne da tsakar daren Juma'a.

    Mista Li ya taɓa yunƙurin zama shugaban ƙasar, to amma ya sha kaye a hannun shugaban ƙasar na yanzu Xi Jinpin.

    Fitattcen ɗan kasuwar, ya taɓa zama mutum na biyu mafi girman muƙami a China, to sai dai a shekarun baya-bayan nan manyan shugabannin ƙasar sun mayar da shi saniyar ware.

    Ya kasance mutum ɗaya tilo daga cikin manyan jami'an gwamnatin, da ba ya cikin magoya bayan Mista Xi.

    "Mutuwar Li na nufin rasa wani babban ƙusan da ke kare muradun masu matsakaicin ra'ayi a cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar gurguzu ta CCP, gurbin da zai yi wahalar cikewa," Kamar yadda Ian Chong, malami a Jami'ar Carnegie, ya shaida wa BBC.

  18. Falasɗinawa da dama za su mutu saboda ƙarancin kayan agaji - MDD

    Majalisar Dinki Duniya ta yi gargadin cewa mutane da dama za su iya mutuwa a Gaza sakamakon karancin kayan agaji da kuma mamayar da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankin.

    Majalisar ta ce hanyar da za a hana hakan faruwa ita ce a yi gaggawar shigar da karin kayan agaji a Gaza.

    Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa na Majalisar Dinkin Duniya, Philippe Lazzarini, ya ce hukumarsu na sanya idanu domin tabbatar da kayan agajin bai faɗa hannun Hamas ba.

    Manyan motocin goma dauke da kayan agaji da jami'an lafiya ne suka shiga Gaza sai dai har yanzu ba a cimma yarjejeniya kan fetur ba.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana yi wa marasa lafiya tiyata ba ta tare da anyi masu allurar kashe zafi ba, yayin da mutane ke kwance a ko'ina a asibitocin yankin.

    Ofishin kare hakkin ɗan'adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya gargaɗi Isra'ila cewa hana shigar da abinci da fetur da katse wutar lantarki ka iya zama laifukan yaƙi.

  19. Arsenal za ta yi rashin Gabriel Jesus saboda rauni

  20. Newcastle ta shiga tsaka mai wuya kan Tonali