Kotun Kolin Najeriya ta sa ranar fara shari'ar zabe tsakanin Atiku da Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. An ƙara samun musayar wuta tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan Hezbollah

    ...

    Asalin hoton, AFP

    An ƙara samun musayar wuta ta kan iyaka tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan Hezbollah a kudancin ƙasar Lebanon.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki da makami mai linzami zuwa Isra'ila.

    Ta ce ta mayar da martani ne da harba tankokin yaƙi da kuma wani harin da jirgin mara matuki ya kai.

    Hezbollah - wacce ke samun goyon bayan Iran -- ta ce an kashe mayaƙanta biyu a ranar Laraba sannan wani ya samu rauni.

    Rikicin kan iyaka ya haifar da fargaba a Isra'ila cewa Hezbollah za ta iya raba hankalin Isra'ila.

    Shugaba Biden ya musanta rahotannin da ke cewa Amurka ta faɗawa Isra'ila cewa za ta shiga yaƙin, idan Hezbollah ta kai wani gagarumin hari.

    • Rikicin Gaza na rura wutar tunzuri a manyan makarantun Amurka
    • Za a shigar da kayan agaji zuwa Gaza
  2. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Aisha Babangida

    Ku kasance da mu domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da kuma faɗin duniya, musamman ma yaƙin Isra'ila da Falasɗinu.