Kotun Kolin Najeriya ta sa ranar fara shari'ar zabe tsakanin Atiku da Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Hotunan Zirin Gaza bayan hare-haren da Isra'ila ta kai

    Sojojin Isra'ila sun ce a safiyar yau suna "ci gaba da kai hare-hare" a wuraren da ke Zirin Gaza.

    Rundunar sojin ta ce tana kai hari ne kan kayayyakin more rayuwa na Hamas.

    Waɗannan hotuna na ranar Alhamis sun nuna sakamakon wasu hare-haren da aka kai ta sama a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  2. Gwamnatin Kaduna ta ware naira biliyan 3.1 don biyan fansho da garatuti

    s

    Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya amince da ware naira biliyan 3.1 domin biyan garatuti ga ma'aikatan da suka yi ritaya da kuma iyalan ma'aikatan da suka mutu.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya ce hakan na daga cikin manufofin gwamnan na rage wahalhalun da tsoffin ma'aikatan ke fuskanta, waɗanda ke cikin mutanen da suka fi shan wahalar rayuwa a jihar.

    Sanarwar ta ce gwamnan na son tabbatar da cewa tsoffin ma'aikatan jihar sun samu haƙƙoƙinsu kamar yadda doka ta tanadar.

    ''Gwamnatin jihar Kaduna ta hanyar hukumar biyan Fansho ta jihar za ta tabbatar da ci gaba da biyan kuɗaɗen fanshon ga tsoffin ma'aikata da kuma iyalan ma'aikatan da suka mutu a faɗin jihar'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Gwamnatin Kaduna ta ce waɗannan kuɗaɗe za su taimaka wajen warware wa mutane matsalolin matsin tattalin arziki da suke ciki, musamman tsoffin mutanen da suka bar aiki.

  3. 'Yan sandan sa-kai ba jami'an 'yan sanda ba ne amma doka ta amince da su'

    ...

    Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta Najeriya (PSC) ta ce ƴan sandan sa-kai na musamman da rudunar ƴan sandan jihar Kano ta ƙaddamar Laraba ba jami'an 'yan sanda ba ne, kuma gwamnati da rundunar 'yan sandan ba ta ɗauke su a matsayin 'yan sanda ba, amma hukumar ta ce doka ta amince da su.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an ja hankalinta game da ayyukan 'yan sandan sa-kan a Kano musamman ɗaukar tubabbun 'yan daba cikin rundunar 'yan sandan sa-kan.

    Sanarwar ta ambato hukumar na cewa dokar aikin ɗan sanda ta amince da ayyukan 'yan sandan sa-kan, kuma a yanzu ne ya kamata a yi amfani da dokar a ƙasar duba da halin rashin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar domin yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a ƙasar.

    Hukumar kula da aikin 'yan sandan ta ce ta amince da irin rawar da ƴan sandan sa-kai ke takawa wajen tallafa wa 'yan sanda don samar da tsaro a ƙasar.

    PSC ta ce tana tattaunawa da rundunar ‘yan sandan jihar Kano, wadda ke amfani da ƴan sandan sa-kai wajen ƙarfafa tsaro na cikin gida, tare da ba su damar magance masu aikata miyagun laifuka da ke aiki a cikin al’ummarsu yadda ya kamata.

    Dokta Solomon Arase, Shugaban Hukumar kuma tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, ya jaddada ƙudirin hada kai da ‘yan sanda domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a Najeriya.

    Arase ya bayyana cewa za a ɗauki matakan bambance rigar ƴan sandan sa-kai a fili da na rundunar ‘yan sandan Najeriya domin kauce wa ruɗani da kuma ayyana takamammen ayyukansu a cikin tsarin tsaron ƙasar.

  4. 'An aikata kisan ƙare-dangi a Darfur'

  5. Ramaphosa da Zelensky sun tattauna kan farfaɗo da yarjejeniyar hatsi

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky sun tabbatar da burinsu na ganin an warware rikicin Rasha da Ukraine cikin lumana.

    A ranar Talata ne shugabannin biyu suka tattauna bisa buƙatar shugaban Ukraine kamar yadda fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta faɗa a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

    Sanarwar ta ce Ramaphosa ya yi marhabin da matakin Zelensky na farfaɗo da shirin noman hatsi a tekun Bahar Aswad kuma shugabannin biyu sun yi alƙawarin ci gaba da yin aiki tare a kan hakan.

    Rasha ta fice daga yerjajeniyar fitar da hatsi da Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya suka ƙulla a watan Yulin 2022 wadda ta ba da damar fitar da hatsi daga tashar jiragen ruwa na Ukraine zuwa kasuwannin duniya.

    Tuni dai Ukraine ta ba da shawarar kafa rumbunan ajiye hatsi a tasoshin jiragen ruwa na Afirka.

    A watan da ya gabata ne shugaban kasar Kenya William Ruto ya ce, Ukraine ta amince da kafa rumbunan ajiye hatsi a tashar ruwan Mombasa domin wadata yankin gabashin Afirka.

    Ƙasashen Habasha da Somaliya da kuma Sudan na daga cikin ƙasashen da suka ci gajiyar yarjejeniyar hatsin Bahar Aswad

    A yayin tattaunawar, Ramaphosa ya kuma jaddada aniyar ƙasarsa na ci gaba da tattauna shirin samar da zaman lafiya a Afirka wanda shugabannin Afirka bakwai suka gabatar a farkon wannan shekarar a matsayin tushen samar da zaman lafiya.

  6. Za a rufe tasoshin motar da ba sa kan ƙa'ida a Abuja saboda ƙaruwar fashi

    ...

    Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce za ta rufe duka tasoshin motar da ke aiki ba bisa ƙa'ida ba, a wani mataki na yaƙi da masu fakewa a matsayin direbobi domin yi wa fasinjoji fashi a mota da aka fi sani da 'One -Chance'.

    Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai.

    An samu rahotannin yin fashi da garkuwa da mutane a Abuja tsawon makonni, inda mazauna birnin ke cikin fargaba kan ayyukan ’yan ta’addan da ke fakewa da sana'ar haya don kai hari da kuma yi wa mutane fashi.

    Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa Wike ya ce hukumar FCTA ta kafa rundunar hadin gwiwa kan laifukan da suka shafi kan iyakoki, tare da mai da hankali kan magance ‘yan fashi da makami.

    Ministan ya danganta ƙaruwar aikata laifukan da tasoshin motan da ke aiki ba bisa ka’ida ba da kuma gine-ginen da ba a kammala ba waɗanda ke zama mafakar ɓata-garin.

    Ya ƙara da cewa, babban birnin tarayya Abuja a tsakiyar jahohin Neja da Kogi da Nasarawa da kuma Kaduna, inda ake fama da matsalar ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

    Mista Wike ya ce, akwai buƙatar rushe gine-ginen da ba a kammala ba da masu laifi ke amfani da su, domin fatattakar ɓata-garin.

    Ministan ya jaddada muhimmancin yin la’akari da illolin tsaro a yayin da ake magance matsalolin da suka shafi tasoshin mota ba bisa ka’ida ba.

    • Yadda Wike ya tayar da ƙura bayan naɗa shi ministan Abuja
    • Yadda rusau ke ƙara jefa mutane cikin fargaba a Kano
  7. Sama da mutum 3,700 aka kashe a Gaza - jami'an kiwon lafiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu sabbin alƙaluma daga ma’aikatar lafiya a Gaza sun ce akalla Falasɗinawa 3,785 aka kashe a Gaza tun lokacin da Hamas ta kai wa Isra’ila hari a ranar 7 ga Oktoba.

    Daga cikin waɗanda aka kashe, 1,524 yara ne, 1,000 mata ne, yayin da kuma 120 tsofaffi ne.

    Jami'an kiwon lafiyar sun kara da cewa mutum 12,493 ne suka jikkata.

    • Kalaman ƙarshe na yaron da aka caka wa wuƙa saboda zargin ƙin jinin Musulmai
    • Me ya sa hankalin duniya ya karkata kan Zirin Gaza?
  8. Chadi ta tabbatar da mutuwar mutum guda sakamakon zazzaɓin Dengue

    ...

    Ƙasar Chadi ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya sakamakon ɓarkewar zazzabin Dengue tare da sama da mutum 1,342 ake zargin sun kamu da cutar ya zuwa yanzu, ciki har da 41 da aka tabbatar.

    Waɗannan alƙalumman sun kasance har zuwa farkon watan Oktoba wanda ya ƙunshi tun lokacin da ƙasar ta ayyana ɓullar zazzabin Dengue a cikin watan Agusta, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

    A halin yanzu ma'aikatar lafiya ta ƙasar tana mayar da martani dangane da ɓarkewar zazzaɓin a daidai lokacin da ake fargabar ta ƙara yaɗuwa saboda ƙarancin ƙarfin sa ido da kuma mayar da martani.

    Gundumar lafiya ta Abéché, da ke kudu maso gabashin lardin Ouaddai, ita ce cibiyar ɓarkewar zazzaɓin a halin yanzu.

    Ana kamuwa da zazzaɓin Dengue ta hanyar cizon sauro kuma sau da yawa yana haifar da alamu masu kama da mura, ba tare da takamaiman magani ba.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta dauki barkewar zazzaɓin Dengue a matsayin babban hatsari a ƙasar saboda yadda sauro suke yaɗuwa sosai a ƙasar da kuma matsalar ƴan gudun hijira da ake fama da ita a yankin sanadiyar rikicin da ake fama da ita a Sudan.

    • Wasu cututtuka da sauro ke jawowa baya ga maleriya
    • Ranar Maleriya ta Duniya: Yadda sauyin-yanayi da rigakafi suke shafar yaki da zazzabin cizon sauro
  9. Sunak ya gana da Netanyahu

    Hoto daga gwamnatin Birtaniya, na Firayim Minista Rishi Sunak na ganawa da Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

    ...

    Asalin hoton, UK government

  10. Sunak ya buƙaci Isra'ila da ta kai agaji zuwa Gaza

    ...

    Asalin hoton, No 10 Downing Street

    Mai magana da yawun fofishin firaministan Birtaniya ya bayar da cikakken bayani kan ganawar da firaministan ƙasar, Rishi Sunak ya yi da shugaban Isra'ila Isaac Herzog a cikin wata sanarwa.

    Sunak ya sake nanata cewa Birtaniya na goyon bayan Isra'ila kuma "ta yi imani da 'yancin ƙasar na kare kai daidai da dokokin ƙasashen duniya".

    Sanarwar ta ce Sunak da Herzog "sun amince da mahimmancin samun tallafin jin ƙai na gaggawa ga Falasɗinawa, talakawan Gaza waɗanda suma ke fama da wahala".

    • Ko sauran ƙasashe za su iya shiga yaƙin Gaza da Isra'ila?
    • Babban asibitin Gaza na cikin mayuwacin hali sakamakon katsewar lantarki
  11. Amurka ta sassauta takunkuman da ta sanya wa Venezuela

    ...

    Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES

    Bayanan hoto, ...

    Amurka na sassauta takunkumin da ta kakabawa Venezuela kan abubuwan da suka shafi man fetur da iskar gas da zinare.

    Matakin na zuwa ne bayan gwamnati da 'yan adawa sun amince a gudanar da zaɓe a shekara mai zuwa.

    Washington ta yi gargaɗin cewa za a iya sauya hukuncin idan yarjejeniyar zaɓen ta ruguje.

    Har yanzu Amurka ba ta amince da shugaba Nicolas Maduro a matsayin halastaccen shugaban ƙasar ba saboda tana kallon zaɓen da ya sake lashewa na 2018 a matsayin shirirta.

    • Takunkumin Amurka a kan Iran ya soma aiki
    • Amurka ta sanya wa wasu 'yan Najeriya takunkumi
  12. Likitoci sun bayar da shawarar yanke ƙafar ɗan wasan fim, Mista Ibu

    Mista Ibu

    Asalin hoton, @REALMRIBU/INSTAGRAM

    Ɗan wasan fim ɗin barkwanci na Najeriya, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu na fama da rashin lafiya.

    A wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, an ga Ibu na neman tallafi daga masoyansa.

    Ɗan wasan ya ce ya kwashe tsawon lokaci kwance a asibiti sanadiyyar “wata cuta mai sarƙaƙiya” da ke damun shi.

    Ya kuma ce a yanzu likitoci sun bayar da shawarar yanke ƙafafunsa.

    “Yanz haka da nake magana ina kwance ne a asibiti, shugaban asibitin ya ce idan har abin da yake tunanin za a yi yanzu bai yi nasara ba to abin da ya fi shi ne a yanke ƙafar.” In ji Mista Ibu wanda ke kwance a asibiti.

    Daga nan sai Mista Ibu ya roƙi masoyansa da su taya shi roƙon Allah domin ganin ba a yanke masa ƙafa ba.

    A ranar Talatar da ta gabata ne ɗan wasan fim ɗin barkwancin ya yi bikin cikar sa shekara 62 da haihuwa, yayin da yake kwance a asibiti.

    A cikin bidiyon na Mr Ibu, wanda aka wallafa a shafin instgaram, za a iya ganin yadda ƙafafu da hannuwan tsohon tauraron fim ɗin ke rawa.

    Yayin da wasu daga cikin iyalai da ƴan’uwansa ke a kusa da shi..

    • Wasu ƴan wasan fina-finan da aka sauya ana tsaka da ɗaukar shiri
    • An nemi ɗauki bayan ƙudajen zuma miliyan biyar sun faɗo daga mota
  13. Dakarun Isra'ila fiye 300 ne suka mutu tun bayan harin Hamas

    ...

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    A wata sabuwa kuma, rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe aƙalla sojojinta 306 tun ranar 7 ga watan Oktoba.

    A jiya ne firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce sama da 'yan Isra'ila dubu 1,400 ne Hamas ta kashe.

    Shi ma kakakin rundunar tsaron Isra'ila Daniel Hagari ya ce ba zai iya kawar da yiwuwar har yanzu mayaƙan Falasɗinawa na ci gaba da zama a yankin Isra'ila ba bayan harin farko na Hamas.

    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
    • Fargaba na ƙaruwa yayin da Isra'ila ke jibge dakarunta a kan iyakar Gaza
  14. Sunak ya gana da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su

    ...

    Asalin hoton, No 10 Downing Street

    Firayim Ministan Birtaniya, Rishi Sunak ya riga ya gana da shugaban Isra'ila Isaac Herzog kuma hotuna na shigowa yanzu da ke nuna yana ganawa da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Daga baya zai gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

    Yayin da ya isa, Sunak ya yi alkawarin tsayawa tare da Isra'ila kuma ya ce Isra'ilawa sun fuskanci "mummunan aikin ta'addanci".

    Ana kuma sa ran zai yi amfani da wannan tafiya wajen matsa kaimi kan kai agajin jin ƙai a Gaza.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Dalilai huɗu da suka sa Hamas ta kai wa Isra'ila hari
  15. Shugaban mulkin sojin Gabon ya yafe albashinsa

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban sojojin ƙasar Gabon, Janar Brice Oligui Nguema, ya ɗauki wasu matakai da nufin tsuke bakin aljuhun gwamnati a mummunan halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.

    Ya yanke shawarar yafe albashinsa a matsayinsa na "Shugaban ƙasar", kuma zai karbi albashi ne kawai a matsayinsa na shugaban rundunar tsaron ƙasar, muƙaminsa na da kafin ya hamɓarar da Ali Bongo.

    Mai magana da yawun kakakin gwamnatin rikon kwarya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a gidan talabijin na kasar a daren jiya, Larabar.

    Rundunar sojin ta kuma sanar da rage alawus-alawus ɗin ‘yan majalisar, da dai sauran matakan da aka dauka na haɗa kuɗaden jama’a da kuma rage kudaden da jihar ke kashewa.

    • Abin da ƴan Gabon ke cewa kan naɗa soja a matsayin sabon shugaban ƙasa
    • Juyin mulkin Sojoji ba zai kawo karshen mulkin iyalin Bongo ba in ji wata majiya a fadar shugaban kasa
  16. Firaministan Birtaniya na ziyara a Isra'ila

    d

    Asalin hoton, EPA

    Rishi Sunak ya isa Tel Aviv bayan ya tashi zuwa Cyprus a daren jiya.

    Ana sa ran zai je birnin Kudus domin ganawa da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban kasar Isaac Herzog.

    Da isarsa Isra'ila, Sunak ya yi Allah wadai da harin Hamas da aka kai a ranar 7 ga watan Oktoba a matsayin "aikin ta'addanci maras misaltuwa" tare da jaddada goyon bayan Birtaniya ga Isra'ila.

    Ya bayyana fatan ganawar da zai yi da shugabannin Isra'ila.

    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
    • Sunak ya jaddada goyon bayan sa ga Ukraine kan mamayar Rasha
  17. 'Badaƙalar kwangila ta janyo wa Najeriya asarar tiriliyan 2.9 cikin shekara uku'

    ...

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    Sabon shugaban Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa a Najeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce ƙasar ta yi asarar naira tiriliyan 2.9 ta hanyar rashin gaskiya a harkar kwangiloli da zamba wajen sayan kayayyakin gwamnati a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga Sanatoci a yayin tantance shi domin tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC ranar Laraba.

    Ya ce adadin kuɗin ya isa a biya kuɗin gina tituna na aƙalla kilomita 1,000, da gina manyan makarantu kusan 200, da kuma ilimantar da yara kusan 6,000 daga matakin firamare har zuwa jami'a a kan Naira miliyan 16 ga kowane yaro.

    Da yake ƙarin haske game da hurumin binciken hukumar, Olukoyede - da Majalisar Dattawan ta tabbatar bayan tantancewar - ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban EFCC yana da ‘yancin gudanar da bincike ga kowa a ƙasar.

    Ya kuma yi alƙawarin rashin saɓa ƙa'ida a gudanar da aikinsa, yayin da ya sha alwashin yin aiki da al’ummar Najeriya tare da tabbatar da gaskiya da kuma ɗaukar matakan kariya don rage ƙararrakin da aka daɗe ana yi.

    • EFFC za ta binciki Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje da Makamashi kan badaƙalar N4.5bn
    • Ya kamata a binciki shugaban EFCC — Matawalle
  18. 'An kashe mace ɗaya tilo a cikin jigogin Hamas'

    Al-Shanti na daga cikin daɗaɗɗun ƴan ƙungiyar Hamas

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Al-Shanti na daga cikin daɗaɗɗun ƴan ƙungiyar Hamas

    Kafofin yaɗa labaran Falasɗinawa na cewa an kashe mace ta farko kuma ɗaya tilo a ofishin kula da harkokin siyasa na Hamas a wani harin da aka kai ta sama.

    Ofishin kula da harkokin siyasar shi ne mataki mafi girma na yanke shawara kan lamurran ƙungiyar.

    Jamila al-Shanti, matar wanda ya kafa ƙungiyar Hamas Abdel Aziz al-Rantisi, ita ce ta kafa ƙungiyar mata a Hamas kuma ta zama mace ta farko da aka zaɓa a ofishin kula da harkokin siyasa a shekarar 2021.

    Babu cikakken bayani kan inda aka kai harin ta sama a cikin rahotannin.

    • Me ya sa mashigar Rafah a Gaza ke da muhimmanci
    • Za a shigar da kayan agaji zuwa Gaza
  19. An mayar da wutar lantarki a babban birnin Guinea-Bissau

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Kamfanin Karpowership na Turkiyya ya maido da wutar lantarki a babban birnin kasar Guinea-Bissau bayan ya dakatar da samar da wutar na kusan kwanaki biyu.

    Kamfanin ya katse wutar lantarki ga Bissau da safiyar ranar Talata saboda rashin biyan kuɗin da ake bin su na aƙalla dala miliyan 15, lamarin da ya jefa birnin cikin duhu.

    Mai magana da yawun kamfanin Karpowership ya shaida wa BBC cewa kamfanin ya samu damar komawa aiki bayan da gwamnati ta biya.

    Kakakin ya ce "Muna godiya da ƙoƙarin gwamnati na warware kuɗaden da ake muke bin su wanda ya ba mu damar sake fara aiki cikin sauri da kuma ci gaba da samarwa mutanen Guinea-Bissau wutar lantarki."

    Ministan makamashi Isuf Baldé ya ce an biya dala miliyan 6 daga cikin dala miliyan 15.

    • Abin da ya sa kamfanin dillancin wutar lantarki na Najeriya ya tafi yajin aiki
    • Guinea-Bissau: Ana fargabar juyin mulki yayin da aka ji karar harbe-harbe a fadar shugaban kasar
  20. Akalla mutum 203 aka yi garkuwa da su a Gaza

    Yayin da aka sanar da mutuwar Carmela da Noya Dan, sojojin Isra'ila sun bayyana adadin mutanen da aka yi garkuwa da su a hare-haren Hamas na ranar 7 ga Oktoba.

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari ya ce sojoji sun sanar da iyalan mutane 203 da aka yi garkuwa da su a Gaza.

    • Musulmai da Yahudawan Birtaniya na fargabar alaƙarsu saboda yaƙin Gaza
    • Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'