Kotun Kolin Najeriya ta sa ranar fara shari'ar zabe tsakanin Atiku da Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Bankwana

    Mun zo ƙarshen rahotonnin a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo muku wasu sababbi gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Bawa ne ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Najeriya ta fito ta bayyana matsayarta kan rikicin Gaza - NSCIA

    Majalisar Koli kan Harkokin Shari’ar Musulunci a Najeriya ta yi kira ga gwammnatin kasar da ta fito ta bayyana matsayarta kan rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da mayakan Falasdinawa.

    Wannan na zuwa ne yayin da ƙasashe da dama ciki har da na Afrika ke ci gaba da nuna matsayarsu game da rikicin.

    A wani taron manema labarai da ta yi yau a Abuja, majalisar ta kuma yi kira ga gwamnati da ɗaiɗaikun jama’a da su tattara kayan tallafi domin aika wa zuwa Gaza.

    Ibrahim Ado Kurawa wakili ne a majalisar ga kuma ƙarin bayanin da ya yi wa Haruna Shehu – Tangaza.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron tattaunawar
  3. Sunak ya buƙaci Saudiyya ta 'goyi bayan samun zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya'

    Sunak/MBS

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Birtaniya Rishi Sunak da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman sun amince a zaman da suka yi cewa rasa rayukan mutane da ba su ji ba ba su gani ba a Zirin Gaza da Isra'ila a cikin makonni biyu da suka gabata yana da ban tsoro, a cewar kakakin Firaministan.

    Sunak, wanda ya isa Riyadh tun da farko, ya karfafa wa Saudiyya gwiwa da ta yi amfani da tasirinta don "tallafawa zaman lafiya" a Gabas ta Tsakiya, a cewar sanarwar da kakakin Firaministan ya fitar.

    Sunak da bin Salman "sun jaddada wajibcin ƙaucewa fantsamar yaƙin" da kuma ɗaukar matakan da suka dace don cimma wannan buri.

    Sanarwar ta ƙara da cewa firaministan da Yarima mai jiran gado sun amince da buƙatar kai agajin a Gaza domin samar da ruwa da abinci da kuma magunguna.

  4. Babu ranar da ba a kashe mutane a Katsina - Radda

    Dikko Umaru Radda

    Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya ce babu ranar da za a wayi gari ba tare da samun labarin kisan mutane ba a faɗin jihar sanadiyyar matsalar tsaro.

    Gwamnan ya faɗi haka ne yau Alhamis lokacin wata tattaunawa da manema labaru a Abuja.

    Gwamnan ya ce matsalar tsaro ta yi wa jihar katutu, ta yadda ƴan fashi a kowace rana ke kai hare-hare a ƙauyukan jihar suna kisa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    A cewarsa “Babu ranar da zan tashi ba tare da samun labarin kisan mutane ba a jihata, har tsoron kunna wayata nake ji saboda na san labarin da zan samu ke nan.”

    Gwamnan ya ce a kan haka ne ya tara ƙwararru waɗanda suka zauna tare da fito da tsarin kafa yan sintiri na jiha, waɗanda za su taimaka wajen samar da tsaro a yankunansu.

    Katsina na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro ta ƴan fashin daji waɗanda suka kwashe shekaru suna kai hare-hare a ƙauyuka da garuruwan jihohin.

    Gwamnatin Tarayya dai ta kaddamar da shirye-shiryen soji da dama a yankin domin yaƙi da matsalar, sai dai har yanzu lamarin na ƙara kazancewa.

    Gwamnan na Katsina ya ce idan samar da tsaro ne kaɗai aikin da zai yi a tsawon wa’adin mulkinsa, ya shirya yin hakan.

    Ya bayyana cewa tun kafin zamansa gwamna, ya zagaya faɗin jihar inda ya ga yadda al’umma ke cikin uƙuba sanadiyyar rashin tsaro.

    Gwamnan ya kuma ce a yanzu an fara samun ingantuwar tsaro a jihar bayan kaddamar da rundunar ‘yan sintiri ta jihar.

    Ya ce “a yanzu bayan kaddamar da rundunar sintiri na yi kwana biyu ba tare da na samu labarin kisan mutane ba a Katsina.”

  5. Jordan da Masar sun yi Alla-wadai da 'hukunci kan kowa da kowa' a Gaza

    Shugaban ƙasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi, da Sarkin Jordan Abdullah, sun yi Alla-wadai da abin da suka kira 'hukunci kan kowa da kowa' da ake yi wa Falasɗinawa a Gaza, bayan wani zama da suka yi a Alkahira domin tattaunawa kan yaƙin.

    Waa sanarwa da Jordan ta fitar, ta kuma yi gargaɗin cewa faɗan na barazanar jefa ɗaukacin yankin cikin bala'i.

    Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama kan Gaza tun bayan kaddamar da wani kazamin hari kan Isra'ilar da Hamas ta yi a ranar 7 ga watan Oktoba.

    Isra'ila ta toshe hanyoyin kai abinci, ruwa, man fetur da kuma wutar lantarki zuwa Gaza bayan harin Hamas.

    Ta ce ba zata kawo karshe kofar rago da ta yi ba har sai Hamas ta saki ƴan ƙasar da tayi garkuwa da su.

    An sa ran al-Sisi da Sarki Abdullah za su tattauna da shugaban Amurka Joe Biden da kuma shugana Falasɗinawa Mahmoud Abbas a Jordan a wannan mako, sai dai Jordan ta soke zaman tattaunawar bayan kazamin fashewa a asibitin Al-Ahli Arab a ranar Talata.

    Masar da Jordan sun kasance ƙasashen Larabawa na farko da suka dawo da hulɗar dangantaka da Isra'ila kuma sun taka rawa a shiga tsakani a rikice-rikicen baya.

  6. Ambaliyar Ghana: ‘Ruwa ya cinye gida da gonata'

  7. Tinubu ya soke naɗin shugaban FERMA

    Imam Kashim Imam

    Asalin hoton, NTA Network News/Facebook

    Shugaba Bola Tinubu ya soke naɗin Injiniya Imam Kashim Imam a matsayin shugaban Hukumar kula da manyan tituna ta Najeriya (FERMA).

    Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar, ba ta faɗi dalilin da ya sa aka soke naɗin nasa ba.

    Naɗin nasa ya zo da ce-ce-ku-ce musamman ma a shafukan sada zumunta ganin ba a taɓa naɗa matashi mai ƙarancin shekaru a hukumar ta Ferma ba, wadda wasu ke ganin tana buƙatar shugabanci mai ɗimbin ƙwarewa da gogewa saboda muhimmancin aikinta.

  8. Za mu yi aiki tare don hana fantsamar rikicin Isra'ila da Gaza - Sunak

    @RishiSunak

    Asalin hoton, @RishiSunak

    Firaministan Birtaniya Rishi Sunak na ziyara Saudiyya, kuma ya wallafa wannan hoto a kafofin sada zumunta lokacin da ya isa.

    "A matsayinmu na al'ummar ƙasashen waje, ba za mu bar harin Hamas ya zama sanadin wata mummunar matsala a ayyukan jin-kai a Gaza ba", in ji Sunak a sakon da ya wallafa a shafin X.

    "Za mu yi aiki tare don tabbatar da cewa ɗorewar zaman lafiya a yankin da hana fantsamar rikicin", a cewar Firaministan na Birtaniya.

    Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani a kan ziyarar tasa da zarar mun samu.

  9. Tunzuri yana karuwa a Gaza yayin da mutane ke rububin samun ruwa da abinci, Tom Bateman daga birnin Kudus

    Muna samun ƙarin alkaluma a cikin sa'o'i 24 da suka gabata da ke nuna yadda matsalar agaji ke ƙaruwa a Gaza.

    Yayin da miliyoyin mutane suka tserewa gidajensu, "ɓacin-rai da takaici" na ƙaruwa cikin mutanen da yaƙin ya ɗaiɗaita waɗanda kuma ke ƙoƙarin ganin sun samu kayan agaji na ruwa, abinci, da kuma magani, a cewar ofishin kula da jin-kai n Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Ofishin ya ce sansanonin da MDD ta samar - wanda suka kasance a cikin makarantu - sun cika makil da mutane, da suka haɗa da yara, manya, masu buƙata ta musamman da kuma mata masu juna biyu.

    Tashohin samar da ruwa sun daina aiki, sannan babu man fetur domin samun damar tayar da injunan ba da ruwa. Don haka, buƙatar ruwan sha na ƙaruwa

    OCHA ya ce wuraren da suka rage na samun ruwa su ne na robobi waɗanda wasu ke sayarwa. Ofishin ya ce "iyalai da dama ba su da karfin samun ruwna roba".

    Gaza situation

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Falasɗinawa sun taru kusa da ɓaraguzan wani gini da harin Isra'ila ya lalata a birnin Khan Younis

    A ɓangaren kiwon lafiya, ɗaukacin tsarin na daf da durkushewa, a cewar hukumomin ba da agaji.

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce rashin man fetur na nufin cewa tawagogin lafiya na aiki cikin duhu, kuma sun daina amfani da gadajen kwantar da marasa lafiya.

    MDD ta ce asibitin Shifa da ke birnin Gaza ta cika da mutanen da suka jikkata bayan hari kan asibitin al-Ahli a ranar Talata.

    Ta ce an tilasta wa likitoci yin tiyata a ƙasa a cikin ɗakunan kwantar da marasa lafiya, ba tare da an yi musu alluran rage zafi ba lokacin tiyata.

    MDD ɗin ta ce rukunin gidaje kusan 100,000 aka lalata, inda ta ƙara da cewa gawawwakin da ke zagwanyewa na ƙaruwa karkashin gine-ginen da aka ruguza, inda ta ce hakan abin damuwa.

  10. Kotun Kolin Najeriya ta sa ranar fara shari'ar zabe tsakanin Atiku da Tinubu

    Atiku Abubakar Team

    Asalin hoton, Atiku Abubakar Team

    Kotun Koli ta sanya ranar Litinin 23 ga watan Oktoba, don fara sauraron karar da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, babbar mai adawa a Najeriya, ya daukaka a kan zaben 2023.

    Wata sanarwa da magatakardar kotun Zainab M Garba ta sanya wa hannu, ta zayyana hukumar zabe ta INEC da wasu, a matsayin wadanda ake kara.

    Atiku Abubakar dai ya yi alkawarin daukaka kara ne a kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe na ranar 6 ga watan Satumba da ya tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu.

    Jagoran adawar na Najeriya ya samo ƙarin shaida a kan karar da ya shiga yana kalubalantar cancantar Tinubu, inda yake fatan Kotun Kolin za ta ba shi damar gabatar da ita, yayin da take sauraron shari'arsa.

    Hukumar zabe ta INEC ta ayyana cewa Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya samu kuri'a 8,794,726, yayin da ta ce Atiku Abubakar ya samu kuri'a 6,984,520.

    Sai dai a karar da ya daukaka gaban Kotun Kolin, Atiku ya shigar da hujjoji guda 35, wadanda yake cewa bisa la'akari da su, kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a karkashin Mai shari'a Haruna Tsammani ta "tafka babban kuskure".

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a takardar daukakar da babban lauyan dan takarar na PDP, Chris Uche ya shigar, Atiku Abubakar ya roki kotun ta jingine duk abubuwan da kotun zaben shugaban kasa ta gano da kuma matsayar da ta cimma.

  11. Gaza na buƙatar agaji da gaggawa - MDD

    Antonio Gutteres

    Asalin hoton, Reuters

    Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce Gaza na buƙatar agaji cikin gaggawa.

    Da yake jawabi ranar Alhamis, a wani taron manema labarai a birnin Alkahira, tare da ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shoukry, Gutteres ya ƙara da cewa ya zama tilas a samar da kafa ta kai kayan agaji ga al'ummar Gaza miliyan 2.2.

    Gutteres ya nanata a jawabinsa cewa, "ya kamata a bai wa masu kai kayan agaji hanya, domin shiga Gaza da kuma raba agajin lami lafiya."

  12. Saudiyya na son ɗaukar nauyin Kofin Duniya na mata 2035

  13. Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin hukumomin yaɗa labarai

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/Twitter

    Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, ya amince da naɗin Lanre Issa-Onilu a matsayin shugaban Hukumar Wayar da kai ta Ƙasa (NOA).

    Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ya fitar, ta ce cikin waɗanda aka naɗan sun haɗa:

    • Mal Salihu Abdulhamid Dembos - shugaban Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA)
    • Dakta Muhammed Bulama - shugaban Gidan Rediyon Tarayya (FRCN)
    • Mr. Charles Ebuebu - shugaban Hukumar Kula da Kafofin Yaɗa Labarai na Rediyo da Talabijin
    • Mr. Jibrin Baba Ndace - shugaban Gidan Rediyon Muryar Najeriya (VON)
    • Dr. Lekan Fadolapo - shugaban Hukumar Kula da Tallace-Tallace
    • Mr. Ali Muhammed Ali - shugaban Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN)
    • Mr. Dili Ezughah - shugaban Hukumar Kula da Gidajen Jarida

    Sanarwar ta ce naɗin nasu na nan take ne.

  14. An kashe shugabannin Hamas a Gaza

    Kafar yada labarai mai alaka da kungiyar Hamas ta ce an kashe shugaban dakarun tsaron Hamas a Gaza.

    Haka zalika, an ba da rahoton cewa an kuma kashe iyalan Jehad Mheisen.

    An kuma ba da rahoton kashe matar mutumin da ya kafa kungiyar Hamas, Abdel Aziz al-Rantisi cikin tsakiyar dare.

    Su ne manyan kusoshin Hamas na baya-bayan nan da suka mutu a abin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana da yaki na tsawon lokaci da kasarsa ta kaddamar a kan Hamas.

    A ranar Laraba ne, kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kashe Jamila Al-Shantee, mace ta farko da aka zaba a kan mukamin siyasa na Hamas a wani hari da Isra'ila ta kai.

    Tun farkon wannan mako, rundunar sojojin Isra'ila ta wallafa a shafin X cewa an kashe Ayman Nofal wanda ta bayyana da "babban jami'in Hamas".

  15. 'Mutum 6 ne suka mutu sakamakon arangama da sojojin Isra'ila a Yammacin Kogin Jordan'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Mutum 6 ne suka mutu sakamakon arangama da sojojin Isra'ila a yanki yamma da gaɓar kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa.

    Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun shiga sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams da ke birnin Tulkarm tun da farko kuma ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin su da 'yan bindigar Falasɗinawa.

    Sojojin Isra'ila sun ce tun da farko sun kama mutane sama da 80 da ake zargi, ciki har da "ma'aikatan ta'addancin Hamas 63", a wani samame da suka kai cikin dare a yankin yamma da gaɓar kogin Jordan.

    Ta ce ta kama mutane biyar da ake zargi a Nur Shams sannan ta ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukansu a sansanin domin daƙile ayyukan ta’addanci.

    Yankin Yamma da gaɓar Kogin Jordan da Isra'ila ke mamaya ya bambanta da Zirin Gaza.

    Hukumomin Falasɗinawa ne ke tafiyar da sassanta, yayin da Gaza ke karkashin Hamas.

  16. Sunak ya nufi Saudiyya a wani abu mai kama da bayan harin 11 ga Satumba, Daga Frank Gardner Wakilin BBC kan sha'anin tsaro

    Sunak

    Asalin hoton, NUMBER 10

    An shiga wani yanayi irin wanda aka taba gani yayin da haka bagatatan ake ganin shugabannin Kasashen Yamma suna rige-rigen zuwa kasashen Gabas ta Tsakiya.

    Kamar yadda Firaministan Birtaniya na wancan lokacin Tony Blair ya rika kai gwauro, yana kai mari daga wannan babban birni zuwa wancan bayan hare-haren 11 ga watan Satumba a kan Amurka a shekarar 2001, a wannan mako ma mun ga shugabannin Amurka da na Birtaniya da na Jamus na garzayawa zuwa yankin don nuna goyon bayansu ga Isra'ila da kuma kokarin hana rincabewar rikicin.

    Yayin da aka tura sakataren harkokin wajen Birtaniya zuwa Masar da Turkiyya da Qatar - kasashen da dukkansu ke da wani tasiri ga Hamas - Rishi Sunak ya kai ziyara zuwa Isra'ila da kuma Saudiyya.

    Ta baya-bayan dai tana da matukar muhimmanci. A matsayin gawurtacciya, hamshakiya a yankin na kasashen Larabawa, da dumbin arzikin man fetur da tarin dukiyar da ta kusa dala tirliya guda a asusunta na zuba jari, kasar Saudiyya na da tasiri.

    Mako biyu da ya wuce tana kan hanyar daidaita alaka da Isra'ila. Yanzu an dakatar da tattaunawar da ake yi bayan Saudiyya ta bayyana goyon bayanta ga matsayin al'ummar Falasdinawa kuma ta zuba ido tana kallo a harzuke yayin da fusatattun masu zanga-zanga suka fantsama kan tituna a fadin yankin.

    Birtaniya na kallon Saudiyya a matsayin wata muhimmiyar abokiyar kawance, duk da zargin rawar da Yarima Mai jiran Gado Mohammed Bn Salman ya taka a shekara ta 2018 wajen kisan gillar da aka yi wa bijirarren dan kasar Saudiyyan nan Jamal Khashoggi.

    A wannan wata ya kamata ya kai ziyara Birtaniya, sai dai a yau fadar firaminista ta ce zuwa yanzu ba a sa takamaiman lokaci ba tukunna.

  17. Firaministan Birtaniya ya nufi Saudiyya

    Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya bar Isra'ila inda ya nufi Saudiyya domin gana wa da Yarima Mohammed bin Salman.

    Ku kasance da mu, za mu kawo muku ƙarin bayani kan ziyarar tasa da zarar ya isa.

  18. An harba ƙarin rokoki zuwa Isra'ila daga Lebanon

    Isra'ila - Lebanon

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, An ga hayaki na tashi bayan da sojojin Isra'ila suka harba rokoki zuwa Lebanon yayin fargaba ke ƙaruwa a kan iyakar

    Ana ci gaba da samun tarzoma a kan iyakar Isra'ila da kuma kudancin Lebanon.

    Sojojin Isra'ila sun ce an harba rokoki 20 daga Lebanon zuwa yammacin yankin Galilee da ke arewacin Isra'ila.

    Rundunar tsaron Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki, a cewar mai magana da yawunta Avichay Adraee.

    Mayakan Hamas da ke Lebanon sun ɗauki alhakin kai harin, inda suka ce sun harba makamai masu linzami 30.

    An ruwaito jikkatar wani mutum mai shekara 70.

    Wannan shi ne sabon hari a kan iyaka tsakanin Isra'ila da mayaka a Lebanon.

    Tun da farko, an harba makamai masu linzami biyu a faɗin iyakar daga Lebanon, amma a wurare daban-daban - can nesa da gabashin yankin kibbutz Manara na Isra'ila.

  19. Dole a nuna jin-ƙai a rikicin Isra'ila da Falasɗinu - Mo Salah

  20. Za a yi wa Neymar tiyata a gwiwarsa