Labarai da dumi-dumi, An fara sanar da sakamakon zaɓen gwamna a Lagos
Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta fara karɓar sakamakon zaɓen gwamna daga ƙananan hukumomin jihar Legas
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan sakamakon zaɓen gwamnoni da aka gudanar a Najeriya
Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Yusuf Yakasai, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge
Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta fara karɓar sakamakon zaɓen gwamna daga ƙananan hukumomin jihar Legas

Hukumar zaɓen najeriya na ci gaba da karbar sakamakon zaɓen gwamna a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Kawo yanzu an gabatar da sakamakon ƙarain ƙananan hukumomi 14, bayan biyun da muka fara kawo muku a baya.
An dai karɓar sakamakon zaɓen ne a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamna da ke birnin Katsina.
Ga yadda sakamakon sauran ƙananan hukumomin 14 ya kasance.
Karamar hukumar Baure:
ADC - 06
ADP - 50
APC - 32,802
NNPP - 62
PDP - 17,888
PRP -12
SDP - 01
ZLP - 02
Karamar hukumar Batagarawa
APC - 26,326
LP - 17
NNPP - 212
PDP - 13,510
PRP - 81
SDP - 25
ZLP - 08
Karamar hukumar Ingawa
ADC - 37
APC - 22,08
LP - 13
NNPP - 209
PDP - 12,255
PRP - 217
SDP - 01
ZLP - 04
Karamar hukumar Dandume
APC - 23,710
PDP - 14,792
NNPP - 220
PRP - 146
Karamar hukumar Dutsi
ADC - 4
APC - 15,631
NNPP - 10
NRM - 11
PDP - 8,419
PRP - 10
SDP - 202
ZLP -03
Karamar hukumar Bindawa
ADC - 26
ADP - 52
APC - 28,997
LP - 21
NNPP - 957
PDP - 12,165
PRP - 47
SDP - 6
ZLP - 3
Karamar hukumar Kaita
ADC - 21
ADP - 70
APC - 24,121
LP - 16
NNPP - 53
PDP - 9,824
PRP - 20
SDP - 04
ZLP - 10
Karamar hukumar Mai'adua
ADC - 08
ADP - 52
APC - 28,436
LP - 01
NNPP - 68
PDP - 11,506
PRP - 10
SDP - 03
ZLP - 01
Karamar hukumar Zango
ADC - 10
ADP - 40
APC - 19,757
NNPP - 04
PDP - 10,477
PRP - 14
SDP - 04
Karamar hukumar Rimi
APC - 28,202
LP - 13
NNPP - 397
NRM - 22
PDP - 13,823
PRP - 37
SDP - 10
ZLP - 02
Karamar hukumar Kusada
APC - 13,750
LP - 04
NNPP - 05
PDP - 11,151
PRP - 17
SDP - 02
ZLP - 02
Karamar hukumar Mani
APC - 29,678
LP - 16
NNPP - 231
NRM - 26
PDP - 16,180
PRP - 28
SDP - 10
ZLP - 03
Karamar hukumar Safana
ADC - 15
ADP - 21
APC - 15,417
BP - 05
LP - 02
NNPP - 09
NRM - 14
PDP - 10,450
PRP - 53
SDP - 143
Karamar hukumar Funtua
AA - 07
ADC - 53
ADP - 120
APC - 31,924
BP - 13 LP - 39
NNPP - 314
NRM - 49
PDP - 19,849
PRP - 218
ZLP - 08
Karamar hukumar Daura
A - 09
AA - 03
ADC - 44
ADP - 106
APC - 26,548
BP - 14
LP - 08
NNPP - 78
NRM - 12
PDP - 10,689
PRP - 27
SDP - 08
ZLP - 03
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fara karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar.
Kawo yanzu dai an karɓi sakamakon ƙananan hukumomi biyu - daga cikin ƙananna hukumomin jihar 23 aka sanar da sakamakonsu.
Manyan jam'iyyu biyu a jihar su ne PDP da APC.
Ga yadda sakamakon ƙananna hukumomin da aka gabatar ya kasance:
Karamar hukumar Binji
APC - 13,410
PDP - 11,078
Karamar hukumar Wurno
APC - 17,350
PDP -13,099

Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta ta fara karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kawo yanzu dai an karɓi sakamakon ƙananan hukumomi tarar - daga cikin ƙananna hukumomin jihar 21 -da ake gudanarwa a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke birnin Yola.
Manyan 'yan takara biyu ne dai ke kan gaba a zaɓen jihar, waɗanda suka haɗar da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri na jam'iyyar PDP, wanda ke neman wa'adi na biyu, da kuma Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani ta jam'iyar APC.
Ga yadda sakamakon ƙananna hukumomin da aka gabatar ya kasance:
Karamar hukumar Jada
ADC - 112
APC - 20899
PDP - 22933
SDP - 753
Karamar hukumar Gombi
ADC - 148
APC - 19665
PDP - 19866
SDP - 59
Karamar hukumar Guyuk
ADC - 55
APC - 14172
PDP - 18427
SDP - 422
Karamar hukumar Shelleng
ADC - 24
APC - 12589
PDP - 14867
SDP - 1136
Karamar hukumar Ganye
ADC - 80
APC - 21605
PDP - 17883
SDP - 69
Karamar hukumar Demsa
ADC - 255
APC - 11798
PDP - 22958
SDP - 146

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya na ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwaman da aka gudanar a jihar.
Kawo yanzu an gabatar da sakamakon kananan hukumomi takwas a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke birnin Minna.
Manyan 'yan takara biyu a jihar su ne Umar Muhammad Bago na jam'iyyar APC, sai kuma Isah Liman Kantigi na jam'iyyar PDP.
Ga yadda sakamakon kananan hukumomin da aka gabatar ya kasance:
1. Karamar hukumar Gurara
Umar Muhammad Bago, APC - 14, 520
Isah Liman Kantigi, PDP - 11, 505
2. Karamar hukumar Tafa
Umar Muhammad Bago, APC - 12, 520
Isah Liman Kantigi, PDP - 12, 082
3. Karamar hukumar Paikoro
Umar Muhammad Bago, APC - 21, 855
Isah Liman Kantigi, PDP - 15, 780
4.Karamar hukumar Munya
Umar Muhammad Bago, APC - 8, 644
Isah Liman Kantigi, PDP - 10, 208
5. Karamar hukumar Bosso
Umar Muhammad Bago, APC -24, 794
Isah Liman Kantigi, PDP - 20, 251
6. Karamar hukumar Suleja
Umar Muhammad Bago, APC - 18, 261
Isah Liman Kantigi, PDP - 15, 551
7. Karamar hukumar Katcha
Umar Muhammad Bago, APC - 17, 037
Isah Liman Kantigi, PDP - 16, 495
8.Karamar hukumar Edati
Umar Muhammad Bago, APC -9, 925
Isah Liman Kantigi, PDP - 16, 559

Hukumar zaɓen Najeriya na shirye-shiryen fara karɓar sakamakon zaɓen gwamnoni a wasu jihohin Najeriya da aka gudanar ranar Asabar.
A jihohin Adamawa da Bauchi hukumar zaɓen ta shirya tsaf domin fara karɓar sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomin.

Can kuma a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar tuni hukumar ta INEC ta fara karɓar sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomin jihar.

To sai daia jihohin Kano da Kaduna hukumar zaɓen ta ce sai nan gaba ne za ta fara karɓar sakamakon zaɓen.

A yau lahadi an ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamna da na 'yan majalisaun dokokin jihohi a mazaɓar VGC a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Hukumar zaɓen ƙasar ce ta ce za a gudanar da zaɓen ne a yau kasancewar ba a samu gudanar da zaɓen a irin waɗannan mazaɓu ba.

A sanarwar da hukumar INEC ta fitar ta ce ba a samu gudanar da zaɓen a wannan mazaɓa ba kasancewar masu kaɗa ƙuri'a sun turje wa ma'aikatan da aka tura.

Hukumar zaben Najeriya a jihohin Kano da Kaduna sun bayyana cewa sai karfe biyu na rana za su soma sanar da sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jiya Asabar.

Hukumar zabe a Najeriya ta soma tattara sakamakon zaben gwamna a jihar Katsina.
Akwai kananan hukumomi 34 a jihar Katsina.
Sakamakon farko shi ne daga karamar hukumar Musawa. Ga yadda aka sanar da alkaluman da kowace jam'iyya ta samu.
Karamar Hukumar Musawa:
Karamar Hukumar Sandamu:

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla mutum shida ne suka mutu da yawa suka jikkata a rigingimun da suka shafi zaɓen gwamnoni da aka gudanar a faɗin Najeriya ranar Asabar.
Jami'an tsaro sun kama mutum 154 bisa laifukan da suka shafi tayar da hargitsi a lokacin zaɓen a jihohin ƙasar da dama, inda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka bayar da rahotonnin sace akwatunan zaɓe.
Rahotonni sun ce mutum shida ne suka mutu a jihohin Delta da Benue yayin da mutane da dama suka jikkata.
Jaridar Vanguard a ƙasar ta ce mutum uku aka kashe a ƙaramar hukumar Ethiope ta Yamma da ke jihar Delta a wata arangama da ake zargin samu tskanin jami'an tsaro da wasu matasa.
Shafin yanar gizo na kafar yaɗa labarai ta Daily Post ya ce sojojin Najeriya sun hallaka wasu mutum uku waɗanda suka yi yunƙurin tayar da hargitsi a yankin ƙaramar hukumar Gboko da ke kudu maso gabashin jihar Benue.
Sannan a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar rahotonni sun ce wasu matasa sun yi yunƙurin sace akwatunan zaɓe da na'urorin BVAS.
Haka kuma 'yan daba sun raunata jami'an zaɓe 16 a ƙaramar hukumar Onitsha ta Kudu a jihar ta Anambra kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Haka a wasu sassan jihohin arewacin ƙasar an samu rahotonnin rigingimun zaben a jihohin Sokoto da Jigawa da Kano da sauransu.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce nan gaba kaɗan ne za ta buɗe cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar.
Wakilinmu na Kaduna Yusuf Tijjani ya ce a yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen a matakan ƙananan hukumomi kafin nan gaba a fara ƙarbarsa a cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamna da ke birnin Kaduna.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da za su samu sabon gwamna, yayin da Malam Nasir El-Rufai ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu a jihar.

An buɗe rumfar zaɓe ta rukunin gidajen Victoria Garden City da ke Ikko, ɗaya daga cikin wuraren da za a gudanar da zaɓen gwamna da na majalisar dokokin jiha a yau Lahadi.
An kasa gudanar da zaɓe a rumfar a jiya Asabar bayan da masu kaɗa ƙuri'a suka turje kasancewar masu aikin zaɓe sun kafa rumfarsu ne a wuri na daban, ba inda aka saba yi ba a baya.
An kasa samun jituwa tsakanin masu kaɗa ƙuria'ar da masu aikin zaɓe, lamarin da ya sa aka ɗage zaɓen zuwa yau Lahadi.




Asalin hoton, Twitter/ICPC
Hukumar yaƙi da cin-hanci da almundahanar kuɗaɗe ta Najeriya ICPC ta ce jami'anta sun kama mutum huɗu bisa zargin sayen ƙuri'a a jihohin Sokoto da Katsina.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama mutanen ne ranar Asabar a lokacin da ake gudanar da zaɓen gwamna da na 'yan majalisar dokokin jihohi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Haka kuma hukumar ta ce an kai wa jami'anta hari tare da raunata mutum guda a jihar Sokoto.
ICPC ta ce an kai wa jami'an nata harin ne a daidai lokacin da ta kama mutum uku masu sayen ƙuri'a a zaɓen da aka gudanar jiya Asabar.

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar rajin kawo ci gaba ta YIAGA, ta ce bayanan da ta tattara sun nuna yadda ƴan siyasa suka rinƙa amfani da abubuwa daban-daban wajen sayen ƙuri’a a zaɓen gwamnonin Najeriya.
Jami’in ƙungiyar, Paul James, ya ce sun samu rahotannin sayen ƙuri’u a jihohi da dama, ciki har da irin su Bauchi da Benue.
Ya ce a Makurdi, babban birnin jihar Benue, an rinƙa saya wa mutane barasa domin su kaɗa ma wasu 'yan takara ƙuri’a.
Haka nan a cewarsa an yi amfani da kuɗi sosai a lokacin zaɓen na gwamnoni wanda ya gudana a ranar Asabar.
A tattaunawar da ya yi da BBC a safiyar yau Lahadi, James ya ce babban abin takaicin shi ne yadda wakilan jam’iyyu suka rinƙa kaɗa wa mutane ƙuri’a bayan sun biya su kuɗi.
Ya kuma ƙara da cewa sun samu rahotannin wasu wuraren da aka ƙona ƙuri’u bayan kai farmaki a rumfunan zaɓe.

Asalin hoton, OTHER
Hukumar zaɓen Najeriya da ke jihar Legas ta sanar da cewa za ta buɗe cibiyar tattara sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar.
Hukumar ta ce da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar wannan rana ta Lahadi ne za ta buɗe cibiyar domin fara karɓar sakamakon zaɓen.
Jihar Legas dai na da yawan masu rajistar zaɓe sama da miliyan bakwai.
Gwamnan jihar mai ci Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC na neman wa'adin mulkin jihar na biyu.
Sauran masu ƙalubalantar sa su ne Gbadebo Rhodes-Vivour na jam'iyyar LP, sai Dr. Olajide Adediran, Jandor na jam'iyyar PDP.

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u a zaɓen gwamnoni a jihohi 28 da na ƴan majalisar dokokin jihohi da aka gudanar a faɗin Najeriya, ranar Asabar.
An samu rahotannin tayar da hargitsi a yankuna daban-daban lokacin zaɓen.
A wani yanki na jihar Legas, wasu sun yi yunƙurin satar akwatin zaɓe, sai dai ba su samu nasara ba, inda aka bi su aka ƙwace akwatin.
An samu rahotannin kai farmaki kan rumfunan zaɓe a Sokoto da Kano da kuma Port Harcort.
Sai dai da alama na’urar BVAS ta yi aiki fiye da lokacin zaɓen shugaban ƙasa, inda bayanai ke cewa an samu nasarar tura sakamako ta na’urar a wurare da dama.
Masu bin mu barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi inda za mu ci gaba da kawo muku labaran yadda sakamakon zaɓen gwamna ke fitowa daga hukumar zaɓen Najeriya.
Kar ku manta da shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan irin labaran da muke sabuntawa a kodayaushe a shafukan namu.
Haruna Ibrahim Kakanki tare da Abdullahi Bello Diginza ne tare da ku a daidai wannan lokaci