APC na kan gaba a sakamakon farko na zaɓen gwamnan jihar Borno

Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fara bayyana sakamakon zaɓen gwamna na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, da aka gudanar ranar Asabar.
Hukumar zaɓen ta fara karɓar sakamakon ne da yammacin Lahadi.
Fafatawar dai ta fi zafi ne tsakanin jam'iyyar APC mai mulkin jihar da kuma jam'iyyar PDP babbar mai hamayya.
Sakamakon da ya fara fitowa zuwa yanzu dai ya nuna cewa jam'iyyar APC ce ke kan gaba.
Jihar Borno na da ƙananan hukumomi 27.
Ga yadda sakamakon ya ke zuwa yanzu.
Ƙaramar hukumar Kaga
PDP - 1091
APC - 9523
LP - 2
Ƙaramar hukumar Magumeri
APC - 10428
PDP - 151
LP - 3
Ƙaramar hukumar Mafa
APC - 23,615
PDP - 83
LP - 2
Ƙaramar hukumar Dikwa
APC - 17,294
PDP - 765
LP - 12
Ƙaramar hukumar Jere
APC - 45,247
PDP - 2785
LP - 79
Ƙaramar hukumar Nganzai
APC - 8,078
PDP - 69
LP - 1
Ƙaramar hukumar Guzamala
APC - 18,341
PDP - 200
LP - 2













