Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda kungiyoyi suka barje gumi a wasannin Asabar

Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Da alama sauyin da Frank Lampard ya yi a Chelsea yayi masa yadda yake so. Kasanbcewar Kante a tawagar ya dace sosai musamman ganin yadda aka dakatar da Jorginho.

    Da babu Kante ba mu san yadda tsakiyar Chelesa za ta kasance ba a yau.

  2. Katin gargadi, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    An bai wa Wilfried Zaha katin gargadi bayan doke Willian da ya yi, Zaha bai ji dadi ba har ma ya yi wa alkalin wasa korafi.

  3. Bugun tazara ga Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Bugun tazara ne mai hadarin gaske Chelsea ta buga a kusa da yadi na 21. Mason Mount ya buga kuma kwallon ta daki bangon 'yan wasan Palace zuwa wajen fili.

  4. Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Chelsea kawai kwallo suke bukata, kwallon tana yi wa Frank Lampard yadda yake so.

  5. Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Chelsea na kara matsa lamba, Crystal Palace kamar ba ita ba manyan 'yan wasanta irin su Zaha sun bata a wasan

  6. Minti 18', Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Yanzu lokacin cin abincin rana ne, babu irin ihun da aka rika yi a filin wasan kamar wanda aka yi a tsakiyar mako a wasan Chsampions League tsakanin Chelsea da Ajax a tsakiyar makon da ya gabata.

    Ko Chelsea za ta nuna irin waccen bajinta a yau? Idan ta ci wasan dai za ta zama ta biyu a teburin na Premier.

  7. Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Willian ya bugo kwana cikin ragar Palace amma babu wani hadari, 'yan baya sun yi aikinsu.

  8. Pullisic ya kai hari, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Christain Pullisisc ya kai wani mummunan hari bayan ya yanke dan wasan baya guda daya sannan ya je daga shi sai gola. Sai dai golan ya kama ta bayan ya dada masa kwallon a cikin yadi na 16.

  9. Zaha da James, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Tuni aka fara fafatawa tsakanin Reece James, lamba 2 na Chelsea, da kuma Wilfried Zaha, dan wasan gaban Palace. Fafatawar za ta yi kyau sosai.

  10. Willian, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Willian na Chelsea ne kyaftin a yau, wanda shi ne wasan farko da dan wasan kasar Brazil din ke daura tsimman a hannunsa a wsan Premeir

  11. An take wasa, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    An take wasa. Mike Deen ne a;lkalin wasa.

    Ko sau nawa VAR za ta taka rawa a yau? Ma ji ma gani dai wai an binne tsohuwa da ranta!

  12. Crystal Palace, Chelsea vs Crystal Palace

    Roy Hodgson, kocin Palace, sauyi daya kacal ya yi a cikin tawagarsa da ta sha kashi a hannun Leicester City da ci 2-0 Lahadin da ta gabata.

    Andros Townsend ya dawo daga jinyar raunin da ya ji kuma ya karbi Jeffrey Schlupp.

    'Yan wasan: Guaita, Ward, Tomkins, Cahill, Van Aanholt, Milivojevic, Kouyate, McArthur, Townsend, Zaha, Ayew

    'Yan benci: Hennessey, Dann, Schlupp, Benteke, McCarthy, Kelly, Riedewald

  13. Tawagar Chelsea, Chelsea vs Crystal Palace

    Kocin Chelsea Frank Lampard ya yi sauyi uku a cikin tawagar da ta byi canjaras 4-4 da kungiyar Ajax a gasar Champions League a daren Talata. Ngol Kante da Reece James da Emerson dukkaninsu za su fara wasan, yayin da Jorginho da Marcos Alonso ba sa cikin tawagar. Sai kuma Cesar Azpilicueta da yake benci.

    'Yan wasan: Kepa, James, Tomori, Zouma, Emerson, Kante, Mount, Kovacic, Willian, Pulisic, Abraham

    'Yan benci: Caballero, Christensen, Giroud, Hudson-Odoi, Batshuayi, Azpilicueta, Gilmour.

  14. Chelsea vs Crystal Palace

    Masu bibiyarmu barkanku da rana, barkanku da sabon makon Premier Ingila na 12.

    Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge ne ke maku barka.

    Shin kun shirya ganin Chelsea ta zama ta biyu a teburi a yau? Kun shirya ganin Wilfred Zaha na Ivory Coast yana yin abin da ya saba? Kun shirya ganin Ngolo Kante a tsakiyar fili yana raba aiki?

    Ku biyo mu kawai a wannan shafi!