Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda kungiyoyi suka barje gumi a wasannin Asabar

Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Aubameyang ya kusa tabukawa, Leicester City 0-0 Arsenal

    David Luiz ne ya hango Aubameyang a mashigar yadi na 18 din Leicester ya ba shi fasin a sama, inda shi kuma ya take ta amma sai dai 'yan baya sun kade ta zuwa bugun kwana.

    Da Aubameyang ya samu yadda yake so da tuni labari ya sha bamban.

  2. Leicester City ta yi canji, Leicester City 0-0 Arsenal

    Ayoze Perez ya fita Demarai Gray ya shigo

  3. Katin gargadi, Leicester City 0-0 Arsenal

    An bai wa Jonny Evans katin gargadi

  4. GOAL Bundesliga, Bayern Munich 2-0 Dortmund

    Gnabry ya kara kwallo ta biyu a ragar Dortmund a minti na 47.

    Lewandowski ne ya fara jefa kwallo a minti na 17.

  5. Ayyaaaa! Arsenal ta ci amma an hana, Leicester City 0-0 Arsenal

    Arsenal ta ci ikwallo ta kafar Aubameyang, sai dai ya yi satar gida..... alkalin wasa ya hana.

  6. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Bellerín ya kai hari mai matukar hadari sai dai ta yi sama ba ta shiga raga ba.

  7. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Da alama Ndidi ya fusata

  8. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Ricardo ya matukar kokarin ta yadda ya kutso kuma ya kawo wa Ndidi Kwallon... hari mafi hadari da aka kai a wasan kenan, ya zuwa yanzu.

  9. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Ndidi ya dako turke ... kuma an ci gaba da kaiwa Arsenal kora.

  10. An dawo wasa, Leicester City 0-0 Arsenal

    Babu wanda ya yi canji

  11. Bundesliga - hutun rabin lokaci, Bayern Munich 1-0 Dortmund

    Yanzu haka Bayern ita ce tana ta uku a teburin Bundesliga da maki 21, inda ita kuma Dortmund take ta biyar da maki 19.

  12. Hutun rabin lokaci: La Liga, Eibar 0 - 3 Real Madrid

    Idan Madrid ta samu nasara a wannan wasan, za ta zama ta daya a kan teburin La Ligar da maki 25.

    Idan Barcelona ta ci nata wasan anjima da Celta Vigo za ta hau saman teburin ita ma da maki 22.

  13. Hutun rabin lokaci, Leicester City 0-0 Arsenal

    Ba a kara ko minti daya ba.... saboda yadda ake buga wasan babu wani bata lokaci.... An tafi hutun rabin lokaci babu wanda ya samu nasarar zira kwallo tsakanin kungiyoyin biyu.

  14. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Kiris ya hana Maddison ya zira kwallo a bugun tazara.

  15. Bundesliga '41, Bayern Munich 1-0 Dortmund

    A wasan hamayyar Bundesliga na kasar Jamus Bayern Munich ce ke kan gaba a wasan da take karbar bakuncin Dortmund.

  16. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Bugun tazara.... Torreira ya yi keta....

  17. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Kwanar farko da Arsenal za ta buga.... caraf a hannun mai tsaron raga Schmeichel

  18. Arsenal ba ta fiya tashi ba tare da kwallo a ragarta ba, Leicester City 0-0 Arsenal

    Wasan waje biyu kacal Arsenal ta buga ba tare da an saka mata kwallo a raga ba a wasa 24 da ta buga na baya-bayan nan - dukkanin wasa biyun kwallo tdaya take ci kuma su ne: tsakaninta da Watford da kuma Newcastle

  19. Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal

    Kwana ta 2 da Leicester City za ta buga.... Tielemans ya dada ta amma ina ba ta shiga ba.

  20. GOAL La Liga '29, Eibar 0 - 3 Real Madrid

    Karim Benzema ya kara kwallo ta uku, kuma ta biyu da ya ciwa Madrid a yau, sai dai duka kwallon Benzema ta biyu da ta Ramos da Finareti aka cisu.