Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda kungiyoyi suka barje gumi a wasannin Asabar

Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Crystal Palace ta yi canji, Chelsea 1-0 Crystal Palace

    Jeffrey Schlupp ya sauya James McArthur

  2. Reece James, Chelsea 1-0 Crystal Palace

    Reece James ya hana Zaha taka rawar da ta dace a wasan.

  3. Chelsea, Chelsea 1-0 Crystal Palace

    Chelsea ta na kara kaimi, domin ganin ta kara kwallo, kar ta yi wasa da damarta ta zama ta biyu a tebutin Premier,

  4. Tammy Abraham, Chelsea 1-0 Crystal Palace

    Da farko kamar Abraham ya yi satar gida amma daga baya alkalin wasa ya karbi kwallon.

    Tammy Abraham dan shekaru 22 da kwana 38 shi ne matashin dan wasa mafi karancin shekaru kuma na biyu da ya ci wa Chelsea kwallo sama da 10 a Premier bayan Arjen Robben.

  5. GOAL '52, Chelsea 1-0 Crystal Palace

    Tammy Abraham ya jefa kwallo

  6. Chelsea 0-0 Crystal Palace, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Babu karsashi daga magoya bayan kungiyoyin, saboda karancin hare-hare a wasan.

  7. Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    kamar minti 45 din farko Chelsea na ci gaba da rike kwallo sama da Crystal Palace.

  8. An ci gaba da wasa, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Kowanne bangare ya dawo da karsashi

  9. Katin gargadi, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Katin gargadi 4 aka bayar a wasan - 3 a bangaren Chelsea, 1 a bangaren Crystal Palace.

  10. Crystal Palace, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Ba a samu dama da yawa ba a wasan, dole kuma a yaba wa Crystal Palace sabo da yadda suka hana Chelsea shiga yadi na 18 dinta.

  11. Tammy Abraham, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    'Yan wasa irin su Tammy Abraham da Wilfred Zaha ba su tabuka wani abin arziki ba zuwa yanzu.

    Ko da yake dai hantsi mya fara duban ludayi, amma anya kuwa sa shiga fili ba tare da sun ci abinci ba.

    Buhari ya ka kalli fallen wasan na farko ne?

  12. Rawar da kowacce kungiya taka, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Rawar da kowacce kungiya taka a minti 45 na farko

  13. Hutun rabin lokaci, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Minti 45 din farko ya kare, babu kwallo ko daya da aka ci.

    Chelsea ce ta mamaye wasan da yawan rike kwallo da kuma yawan hare-hare.

  14. Williaaaaan, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Willian ya kai wani mummunan hari mafi kyau a cikin mintunan karshe tun bayan wanda Pullisic ya kai.

    ya buga kwallon a cikin yadi na 18 din Palace bayan Mount ya bai wa James, inda shi kuma ya bugo ta cikin raga daga gefen dama.

    Ba don tsohon dan wasan Chelsea ba Gary Cahill da Willian ya jefa kwallon farko a wasan, mummunan hari daga bangaren Chelsea.

  15. Karin lokaci, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    An kara minti 4 a karshen minti 45 na farko da aka buga.

  16. Palace ta yi canji, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Martin Kelly na Palace ya shigo wasan, inda ya karbi Joel Ward a minti na 44.

  17. Crystal Palace 43, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Har yanzu Crystal Palace ba ta kai wani hari mai hadari ba hasali ma ko shot daya ba ta yi ba. Zaha kana ina ne? Ko sai magoya baya sun fara rera sunanka ne.

    Har yanzu babu ci tsakanin kungiyoyin biyu.

  18. Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Samun nasara ga Chelsea wata dama ce ta zama a matsayi na biyu a teburin Premier kafin Manchester City ta yi wasa gobe da shugabannin teburin wato Liverpool.

  19. Chelsea, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Chelsea na da kashi 75% na yawan rike kwallo, sai dai duka a tsakiyar fili, akwai bukatar kara matsa lambar da zai kai ga cin kwallo.

  20. Katin gargadi, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    An bai wa Emerson katin gargadi bayan ya yi wa Andros Townsend keta.