Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hikayata 2023: Yadda za ki shiga gasar
Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai (Latsa nan domin aikewa da labari) wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa.
Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo.
Mata biyu na iya haɗa gwiwa su shigar da labari guda amma ka da su haura mata biyu, kuma labari ɗaya kacal mace za ta iya shigarwa.
Gasar dai ta mata zalla ce wadanda shekarunsu ba su gaza 18 ba sannan kuma ba su wuce 35 ba ya zuwa ranar 20 ga watan Agustan 2023.
Za a rufe gasar da karfe 23:59 na ranar 20 ga watan Agustan 2023. Latsa nan domin shiga gasar
Ku tabbatar kun karanta ka'idojin gasar da dokokin bayanan sirri na BBC kafin ku shiga gasar.
Wata tawagar alƙalai waɗanda ba ma'aikatan BBC ba ne, bisa jagorancin ma'aikacin BBC za su zaɓi gwarzuwa ɗaya da labarinta ya yi nasarar yin na ɗaya sannan za su zaɓi ta biyu da ta uku.
Kafin tura wa alƙalan labaran don tantancewa za a cire duk wani bayani dangane da mai shiga gasa kuma ba za a aika masu ko wane irin bayani kan masu shiga gasar ba.
Waɗanda su ka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan daya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu dari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu dari biyar) ga wadda ta zo ta uku.
BBC za ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa.
Za a sanar da mutum ukun da suka zamo zakaru a yayin wani bikin karramawa a Abuja, babban birnin Najeriya.
BBC za ta sanar da lokacin bikin ta hanyar wallafa bayanin a shafukanta na intanet da na social midiya.