Sakamakon zabukan Kenya na 2022 kai-tsaye

Kenya Election 2022 live results updates

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

BBC tana amfani da bayanan da aka wallafa a shafin intanet na Hukumar Zabe da Kan Iyakoki (IEBC) domin kirga kuri'un zaben shugaban kasar na wucin-gadi. A yayin da hukumar take tantance kuri'un, za a iya samun jinkiri kan yadda BBC take sabunta bayanan. A bisa dokokin zaben Kenya, hukumar zaben ce kadai ke da alhakin bayyana sakamakon zaben.

A ranar Litinin 15 ga watan Agusta ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Kenya ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na 2022.

Hukumar ta ayyana mataimkain shugaban ƙasar mai ci, William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Al'ummar ƙasar Kenya ba su fita kaɗa ƙuri'a sosai ba a manyan zaɓukan ƙasar na 2022, inda mutum miliyan 12.2 ne kawai suka kada ƙuri'unsu a cikin miliyan 21 da ake sa ran za su yi hakan.

A ranar Talata 9 ga watan Agustan 2022 ne ƴan Kenya suka fita don zaɓar sabon shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki da na wakilai da gwamnaoni, waɗanda za su ja ragamar mulkin ƙasar na tsawon shekara biyar, sannan sai su fara dakon sakamako bayan rufe rumfunan zaɓen.

Ɗaya daga cikin tambayoyin da mutane ke yi ita ce zuwa yaushe za su san wanda ya lashe zaɓen?

Hukumar zaɓen Kenya mai zaman kanta (IEBC), ita ce ke da alhakin bayyana wadanda suka yi nasara, kuma za su sanar da sakamakon zaɓen ne a cikin kwana bakwai.

Za a yi hakan ne bayan hukumar zaɓen ta tattara, ta ware tare da ƙirga sakamakon da aka samu daga dukkan mazaɓun.

Sashen na 138 sakin layi na 10 na kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce, "Shugaban hukumar zaɓen zai sanar da sakamakon tare da bayar da bayanin yadda sakamakon yake a rubuce ga Babban Alkalin ƙasar da kuma shugaban mai barin gado Uhuru Kenyatta."

Sashe na 138 sakon layi na uku kuma ya ce bayan ƙirga ƙuri'un a mazaɓu, hukumar zaɓen za ta tattara, ta tantance ta kuma ayyana sakamakon.

Ga taswirorin sakamakon zaɓukan Kenya na 2022

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kenya na 2022

Dole ne ɗan takara ya samu kashi 50% na ƙuri'un da aka kaɗa a cikin a ƙalla kashi 25% na yawan ƙuri'un a cikin gunduma 24 cikin 47 na ƙasar.


Lokaci na ƙarshe da aka sabunta: 15/08/2022, 18:59:31 EAT

Final results from IEBC

Ƴan takara Ƙuri'u
William Ruto
50%
50.5%
7,176,141
William Ruto
7,176,141
Gamayyar Kenya Kwanza
Ƙuri'u 7,176,141
A ƙalla kashi 25% na al'ummar gundumar sun kada ƙuri'a 39/47
Raila Odinga
48.8%
6,942,930
Raila Odinga 6,942,930
Gamayyar Azimo la Umoja
Ƙuri'u 6,942,930
A ƙalla kashi 25% na al'ummar gundumar sun kada ƙuri'a 34/47
George Wajackoyah
0.4%
61,969
George Wajackoyah 61,969
Jam'iyyar Roots
Ƙuri'u 61,969
A ƙalla kashi 25% na al'ummar gundumar sun kada ƙuri'a 0/47
David Mwaure
0.2%
31,987
David Mwaure 31,987
Jam'iyyar Agano
Ƙuri'u 31,987
A ƙalla kashi 25% na al'ummar gundumar sun kada ƙuri'a 0/47
Sauran 'yan takara
0.6%
93,956
Sauran 'yan takara 93,956

Sakamakon zaɓukan ƴan majalisar dattijai na Kenya na 2022

Wace jam'iyya ko gamayya ce take da iko da majalisar dokoki?

Lokaci na ƙarshe da aka sabunta: 16/09/2022, 10:50:59 EAT

Taswirar bayanan sakamakon zaɓen a teburin da ke ƙasa, da ke nuna kowace kujera ta majalisar dokoki a matsayin ɗigo da launi a jiki.
Jam'iyya Kujeru
Gamayyar Azimio la Umoja 168
Kenya Kwanza 167
Jam'iyyu ƴan ba ruwanmu/Ƴan majalisa marasa jam'iyya 14
Wadanda ba a bayyana ba 0
Bayanai daga: Hukumar zaɓe ai zaman kanta

Ga inda za ku duba don ganin sakamakon zaɓen gwamnoni na Kenya na 2022

Ga inda za ku ga sakamakon zaɓukan ƴan majalisar dokoki

Ga inda za ku duba don ganin sakamakon zaɓuka na gundumomi