Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sakamakon zabukan Kenya na 2022 kai-tsaye
BBC tana amfani da bayanan da aka wallafa a shafin intanet na Hukumar Zabe da Kan Iyakoki (IEBC) domin kirga kuri'un zaben shugaban kasar na wucin-gadi. A yayin da hukumar take tantance kuri'un, za a iya samun jinkiri kan yadda BBC take sabunta bayanan. A bisa dokokin zaben Kenya, hukumar zaben ce kadai ke da alhakin bayyana sakamakon zaben.
A ranar Litinin 15 ga watan Agusta ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Kenya ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na 2022.
Hukumar ta ayyana mataimkain shugaban ƙasar mai ci, William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Al'ummar ƙasar Kenya ba su fita kaɗa ƙuri'a sosai ba a manyan zaɓukan ƙasar na 2022, inda mutum miliyan 12.2 ne kawai suka kada ƙuri'unsu a cikin miliyan 21 da ake sa ran za su yi hakan.
A ranar Talata 9 ga watan Agustan 2022 ne ƴan Kenya suka fita don zaɓar sabon shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki da na wakilai da gwamnaoni, waɗanda za su ja ragamar mulkin ƙasar na tsawon shekara biyar, sannan sai su fara dakon sakamako bayan rufe rumfunan zaɓen.
Ɗaya daga cikin tambayoyin da mutane ke yi ita ce zuwa yaushe za su san wanda ya lashe zaɓen?
Hukumar zaɓen Kenya mai zaman kanta (IEBC), ita ce ke da alhakin bayyana wadanda suka yi nasara, kuma za su sanar da sakamakon zaɓen ne a cikin kwana bakwai.
Za a yi hakan ne bayan hukumar zaɓen ta tattara, ta ware tare da ƙirga sakamakon da aka samu daga dukkan mazaɓun.
Sashen na 138 sakin layi na 10 na kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce, "Shugaban hukumar zaɓen zai sanar da sakamakon tare da bayar da bayanin yadda sakamakon yake a rubuce ga Babban Alkalin ƙasar da kuma shugaban mai barin gado Uhuru Kenyatta."
Sashe na 138 sakon layi na uku kuma ya ce bayan ƙirga ƙuri'un a mazaɓu, hukumar zaɓen za ta tattara, ta tantance ta kuma ayyana sakamakon.
Ga taswirorin sakamakon zaɓukan Kenya na 2022
Sakamakon zaɓukan ƴan majalisar dattijai na Kenya na 2022
Ga inda za ku duba don ganin sakamakon zaɓen gwamnoni na Kenya na 2022
Ga inda za ku ga sakamakon zaɓukan ƴan majalisar dokoki
Ga inda za ku duba don ganin sakamakon zaɓuka na gundumomi