Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nura Mustapha Waye: 'Yan Kannywood na jimanin rasuwar daraktan 'Izzar So'
A ranar Lahadi ne aka yi jana'izar Nura Mustapha Waye, daraktan shirin nan mai dogon zango na 'Izzar So', wanda ake nunawa a dandalin YouTube.
Tun bayan rasuwarsa, jama'a da dama musamman abokan sana'arsa ta fim, suke ta yin alhini a shafukan sada zumunta.
Sanarwar rasuwarsa dai ta bai wa mutane da dama mamaki ganin cewa ba a san shi da wata rashin lafiya ba, kuma lafiya kalau aka rabu da shi kwana guda kafin rasuwarsa, kamar yadda makusantansa suka bayyana.
An gudanar da jana'izarsa a unguwarsu ta Goron Dutse da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.
Yadda Ƴan Kannywood ke alhinin rasuwar Nura Mustapha
Furodusan shirin Izzar So, Lawan Ahmed, ya bayyana Nura a matsayin mutumin kirki sannan ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma yafe kurakuransa.
Ita ma Aisha Najamu wadda aka fi sani da Aisha Izzar So ta yi masa addu'ar Allah jikansa da gafara.
Jarumi a masana'antar Kannywood Ali Nuhu shi ma ya saka hotonsa da ya ɗauka tare da marigayin inda ya roƙi Allah ya kyautata makwancinsa.
Darakta a masana'antar Kannywood, Malam Aminu Saira, shi ma ya wallafa hoton marigayin a shafinsa na Instagram inda ya yi masa addu'ar Allah ya jikansa da rahama kuma ya saka shi Aljanna Firdausi.
Ita ma Khadijah Yobe, wadda aka fi sani da Karima a shirin Izzar So, ba a bar ta a baya ba wurin wannan ta'aziyya inda ta roki Allah ya sa Aljanna ce makoma ga darakta Nura.