Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Binta Kofar Soro: 'Yan Kannywood na jimamin rasuwarta
Jama'a da dama na ci gaba da ta'aziyya tun bayan rasuwar fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood din nan wato Hajiya Binta Kofar Soro.
Hajiya Binta ta rasu ne a ranar Asabar, 4 watan Mayu a garin Katsina a gidanta da ke unguwar Filin Samji.
Tun bayan rasuwar jarumar, manya-manya daga cikin taurarin Kannywood kamar su Ali Nuhu da Rahama Sadau ta Sani Danja suka yi ta'aziyyar rasuwarta a shafukan su na sada zumunta.
Rahotanni sun bayyana cewa, kafin rasuwarta ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
Ba ma jaruman fina-finai kadai ba, harda sauran jama'a ma sun yi ta'aziyya da nuna alhininsu game da rashin da Kannywood ta yi.
Tuni dai aka yi jana'izar marigayiyar kamar yadda addinin musulunci ya tanadar
Sai dai kafin rasuwar jarumar, ta wallafa a shafinta na Instagram inda ta bukaci al'ummar Musulmi da su yafe mata duk wanda ta yi wa laifi da wanda bata yi masa ba.