Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Kannywood na jimamin mutuwar Ladi Mutu-ka-raba
A ranar Asabar ne aka samu labarin rasuwar fitacciyar 'yar Kannywood din nan wato Ladi Mohammed wadda aka fi sani da Ladi Mutu-ka-raba.
An bayyana cewa jarumar dai ta rasu ne bayan ta yi fama da doguwar rashin lafiya.
Tuni jama'a da dama cikinsu har da 'yan Kannywood suka fara yin ta'aziyya dangane da rasuwarta.
Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso kenan ke ta'aziyyar mutuwar Ladi a shafinta na Instagram.
Shi ma Ali Nuhu wanda tauraro ne a Kannywood ya yi ta'aziyyar rasuwarta a shafin instagram.
Sani Danja ba a bar shi a baya ba wajen yin ta'aziyya kan rasuwar Marigayiya Ladi.
A bara ne dai bayan rashin lafiyar marigayiyar ta yi tsanani aka yi ta yawo da hotunanta a shafukan intanet inda ake cewa tana bukatar taimako.
Sai dai Marigayiyar ta fito ta kare kanta dangane da hakan inda ta ce masu son bata mata suna ne suka aikata hakan.
Tuni jama'a da dama cikinsu har da 'yan Kannywood suka fara yin ta'aziyya dangane da rasuwarta.
Fim din da ta yi na Mutu ka raba na daga cikin fina-finan da suka sa ta yi fice kamar yadda Ibrahim Sheme ya shaida wa BBC da muka tuntube shi bayan rasuwarta.