Sani Garba SK: Rayuwar marigayi dan wasan kwaikwayon Hausa cikin hotuna

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A ranar Alhamis da safe ne aka yi jana'izar tauraron fina-finan Hausa Sani Garba SK a gidansa da ke unguwar Mandawari da ke birnin Kano a Najeriya.

Ya rasu ne ranar Laraba da maraice bayan ya yi fama da rashin lafiya.

"Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibiti," in ji wani furodusa Abdul Amart, a tattaunawarsa da BBC Hausa.

Mun zabo muku wasu daga cikin hotunan rayuwarsa: