Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Kayen da Buhari ya sha a kotu da korar shugaban NUT da malamai a Kaduna
Labaran siyasa ne ke ci gaba da mamaye tattaunawa da kuma kafofin yaɗa labarai a Najeriya.
Kamar kowane mako, mun duba wasu muhimmai daga cikinsu da suka faru a wannan makon.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta bayyana Biodun Abayomi Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti.
A daren da ya gabata ne hukumar INEC ta ce Mista Oyebanji ya samu kuri'u 178,057.
Hakan ya sanya jam'iyyar All Progressive Congress ta zamo wadda ta samu kuri'u mafi yawa a zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Yunin shekara ta 2022.
Dan takarar jam'iyyar Social Democratic Party, Olusegun Oni, shi ne ya zo na biyu a zaben inda ya samu kuri'u 82,211.
Sai jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) wadda ta zo ta uku, inda dan takararta Bisi Kolawole ya samu kuri'u 67,457.
Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar APC ce ta lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar, inda jam'iyyar PDP ta yi nasara a karamar hukuma daya tal.
Kama mai amfani da shafukan karya a intanet da 'yan sandan Kano suka yi
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta damƙe wani matashi a Kano wanda ake zargi da amfani da shafukan bogi a kafafen sada zumunta domin yaudarar jama'a.
Mai magana da yawun ƴan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook inda ya ce sun samu nasarar kama matashin mai suna Musa Lurwanu mai shekara 26 ne bayan tattara bayanan sirri da kuma bin diddiƙin lamarin.
Ya bayyana cewa tun da farko sun samu ƙorafe-ƙorafe ne tun a watan Afrilun bana kan yadda wani ya yi ƙaurin suna a kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da sunayen maza da mata da hotunansu domin buɗe shafuka a Facebook da Twitter da Whatsapp da dai sauransu domin yaudarar mutane.
A cewar ƴan sandan, har sun samu ƙorafi daga wata Zahra Mansur mai shekara 20 wadda ta ce abokanta da ƴan uwa na ta kiranta sakamakon wani na amfani da sunanta da hotonta da bidiyoyi wurin buɗe shafukan Facebook da kuma yaudarar jama'a.
Korar shugaban NUT da malamai fiye da 2000 da El-Rufa'i
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanar da korar malamai 2,356, da suka gaza cin jarrabawar gwaji da aka yi musu.
Hukumar da ke kula da ilimi matakin farko ta KADSUBEB ta sanar da matakin ranar Lahadi, wanda ya shafi har da shugaban kungiyar malamai ta kasa Audu Amba.
Mai magana da yawun KADSUBEB Hauwa Mohammed ta ce hukumar ta yi jarrabawar ne ga sama da malamai 30,000 a cikin watan Disamban 2021.
Ta ce sun kori malaman firamare 2,192 da suka hada da Shugaban kungiyar malamai ta kasa wato NUT, Audu Amba, saboda kin zana jarrabawar kwata-kwata.
Ta kara da cewa sun kori wasu malamai 165 daga 27,662 saboda gaza samun makin da ya dace.
Kotu ta hana INEC dakatar da rajistar katin zaɓe
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, babban birnin Najeriya, ta hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, dakatar da rajistar katin zaɓe.
Hukumar dai ta sanya ranar 30 ga watan Yunin 2022, a matsayin ranar da za ta dakatar da rajistar masu zaben.
Sai dai kotun karkashin jagorancin mai shari'a Mobolaji Olajuwon ta bayar da umarni na wucin gadi kan daina yin rajistar har zuwa ranar 29 ga watan Yuni da za ta sake zama domin sauraron karar.
Mai shari'a Olajuwon ta yanke wannan hukunci na wucin gadi ne bayan sauraren karar da Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta shigar da INEC.
SERAP da sauran wasu masu fafutuka 185 suna shigar da karar Hukumar zaben a farkon wannan wata, suna neman kotu ta bayyana wa'adin da INEC ta sanya a matsayin haramtacce da ya ci karo da kundin tsarin Mulki.
Tinubu ya ce ya koma ga Allah
Dan takarar shugaban kasa a Najeriya karkashin jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce ya koma ga Allah a lokacin da ya lura cewa wasu sun hada kai suna son ganin bai tsaya takarar shugaban kasa na jam'iyyar ba.
Tinubu ya ce ya fahimci cewa an shirya yi masa taron-dangi don ganin bayansa kan takarar shugaban kasa da yake son yi.
Gboyega Akosile, sakataren yada labarai na gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya ambato Tinubu na yin wadannan kalaman a lokacin da ya kai wa Oba na Lagos Rilwan Akiolu ziyara, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Tsohon gwamnan na Jihar Lagos ya doke mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; tsohon Ministan ma'aikatar Sufuri, Rotimi Amaechi; shugaban majaliasar dattawa Ahmad Lawan da wasu 'yan takara 10 a zaben fitar da gwani.
Buhari ya sha kaye a Kotun Koli a shari'a kan dokar zabe ta 2022
Kotun Koli a Najeriya ta yi watsi da karar da Shugaba Muhammadu Buhari da Babban lauyan gwamnati suka shigar, suna bukatar fashin baki kan sashe na 84 na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa garambawul.
Sashen ya haramata wa duk wani mai rike da mukami na siyasa, da aka nada a dukkan matakai, ya kada kuri'a a zaben fitar da gwani na duk wata jam'iyya.
Alkalan Kotun bakwai da suka yi zaman ranar Juma'a a karkashin jagorancin Mai Shari'a Musa Dattijo, dukansu sun amince cewa karar yunkurin wahalar da kotu ne kawai.
A hukuncin da Mai Shari'a Akomaye Agi ya karanto, Kotun Kolin ta ce ba zai yiwu Shugaba Buhari ya nemi a goge sashen na 84 da dokar zabe 2022, bayan da a baya ya aminta da shi.
An gurfanar da Sanatan Najeriya bisa zargin yunkurin cire sassan jikin mutum
An gurfanar da wani dan majalisar dattawan Najeriya a gaban kotu bisa zargin kai wani yaro kasar Birtaniya da zummar cire sannan jikinsa.
Ike Ekweremadu, mai shekara 60, da matarsa Beatrice Nwanneka Ekweremadu, mai shekara 55, sun gurfana a gaban kotun Majistiret ta yankin Uxbridge a Yammacin London ranar Alhamis.
An mika wa gidan kula da kananan yara yaron, mai shekara 15, da ake zargi an kai London domin cire sassan jikinsa. Rundunar 'yan sandan birnin London ta ce hukumomi suna yin bakin kokarinsu domin kulas da shi.
Kotun ta saurari karar da ke cewa Mr Ekweremadu, wanda dan siyasa ne kuma lauya, ya taba zama mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya.