Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Abdussalam Muhammad, Baban Gwale

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale
An wallafa

An haifi Sheikh Abubakar Abdussalam Muhammad wanda aka fi sani da Baban Gwale ne a birnin Kano da ke arewacin Najeriya a shekarar 1982.

Ya shaida wa BBC a filinmu na Ku San Malamanku cewa tun gabani "a yaye" shi ya iya magana kuma hakan ne ya ba shi damar soma koyar sunayen Allah da Larabci daga wurin mahaifiyarsa.

Malamin ya kara da cewa bayan ya soma tafiya ne aka fara zuwa da shi makarantar allo ta marigayi Malam Maraya, inda daga bisani ya koma makarantar Alaramma Malam Inuwa, ko da yake a makarantar allo ta Malam Idi ya kammala saukar AlKur'ani.

"Daga baya ne na karasa satu sannan aka kai ni wajen Alaramma Malam Mu'azu a unguwar Gwammaja, sai kuma daga baya lokacin da na kai Suratul Nahli ina rubuta AlKur'ani na kammala sauka ta farko, sai aka mayar da ni makarantar Alaramma Malam Dahiru," in ji Malamin.

Sheikh Muhammad ya ce a makarantar Shababul-Kur'an ta Malam Abubakar Ramadan ya soma koyar tajwidi.

Ya kara da cewa ya shiga makarantar firamare ta Dangado Special Primary School a shekarar 1988, kuma bayan ya kammala ya shiga makarantar Sakandare mai suna Government Arabic College da ke Gwale.

Malamin ya ce ya kuma shiga makarantar zaure ta Malam Muhammad Kani Gwale inda ya koyi karantun Tauhidi da Luga da Usulul Fiqh da Adabi da sauransu.

Sheikh Abubakar Abdussalam Muhammad ya ce daga nan ya yi karatun Share fagen shiga Jami'a ko da yake ya kuma yi jarrabawar JAMB inda ya samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero da ke Kano domin karanta Aikin Jarida.

Sai dai ya sauya zuwa Fannin Shari'a sannan kuma daga bisani ya samu damar tafiya Sudan inda ya soma karatun Digiri.

Amma daga bisani ya samu gurbin karatu a Jami'ar Madina inda ya karancin Fannin Hadisi da Kimiyyarsa inda ya kammala a 2008/9.

Ya ce ya sake komawa Makkah inda ya yi karatun gaba da Digiri na farko a Tsangayar Horas da Limamai da Malamai a kan Da'awa.

Baban Gwale ya samu aiki a aiki a Kwalejin Shari'a da Addinin Musulunci mai suna Aminu College of Legal Studies da ke Kano.

Kana ya koma Sudan inda ya yi Digiri na biyu a fannin koyar da Hadisi da Kimiyyarsa. Daga bisani ya yi Digirin-Digirgir a kasar ta Sudan.

Malamin ya kara da cewa a zamansa na Madina ya hadu da manyan malamai, cikinsu har da 'yan Najeriya, wadanda suka koyar da shi matuka.

Surori masu wahala

Baban Gwale ya ce Suratu Nahl da Suratu An'am da Suratu Ankabuti da Suratu Ahqaf ne suka fi ba shi wahala.

Amma ya ce yana son Kur'ani kafatan, sai dai ya fi son Suratu Nisa'i da Furqan da Israi'i saboda "idan ina karanta su nakan shoga wani yanayi mai dadi."

Malam ya ce ranar da ya samu gurbin karatu a Jami'ar Madina ce ranar da ya fi farin ciki da ita a duniya.

Ya ce abu biyu ne na takaici da ba zai manta da su ba, wato kuskuren da aka samu a lokacin da ya samu gurbin karatu a karon farko a Jami'ar Bayero. Malam ya ce ya sha wahala sosai a lokacin.

Abu na biyu kuma lokacin da yake aji uku zai shiga na hudu a Madina a lokacin da ya je Kano hutu har fasfo ɗinsa da tikitinsa suka fadi.

"Na ga wulakanci sosai a ofishin fasfo da jami'an ofishin jakadancin Saudiyya a Kano, wannna abu ya jawo na rasa zango ɗaya na karatu a Jami'ar Madina."

Baban Gwale ya ce babban abin da ke faranta masa rai shi ne ya ga ana bautar Allah da Manzonsa, amma ya tsani zalunci da tauye hakki musamman na mata a gidajen aure.

Yana da mata biyu da ƴaƴa tara.