Bola Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na APC

Asalin hoton, Tinubu Facebook
Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.
Ya lashe zaɓen ne da ƙuri'a 1,271, kuma dama tun da fari shi ne ƴar manuniya ta nuna ya fi yawan ƙuri'u.
Bisa alƙaluma da aka sanar a bainar jama'a, ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu ƙuri'a 316, yayin da Yemi Osinbajo ya samu ƙuri'a 235.
Shugaban majalisar dattijan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ya samu ƙuri'a 152.
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu ƙuri'a 47, shi kuwa tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha bai samu ƙuri'a ko ɗaya ba.
Shi kuwa gwamnan jihar Cross River Ben Ayade ya samu ƙuri'a 37, yayin da gwamnan Ebonyi Dave Umahi ya samu ƙuri'a 38, shi kuwa tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yariman Bakura ya samu ƙuri'a hudu.
Tsohon gwamnan jihar Legas din dai ya mamaye muhawarar shafukan sa da zumuntar a Najeriya kusan mako guda tun kafin zaɓen.
Zaben dai ya ɗauki hankali ƴan Najeriya sosai a ciki da wajen ƙasar, musamman bayan da ƴan takara kusan bakwai suka ce sun janyewa Tinubun.









