Tukunyar gas ta sake fashewa a Kano, ta jikkata kusan mutum 70

.
An wallafa

Rahotanni daga Jihar Kano sun ce wata tukunyar gas ta sake fashewa a ranar Juma'a a unguwar Sharada 'yan tagwaye.

A safiyar ranar Juma'an an samu irin wannan fashewa a Unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso.

Tuni ma'aikatan NEMA da SEMA suka kai dauki wurin da abin ya faru, kamar yadda wakilin BBC ya shaida.

Ya zuwa yanzu dai babu rahoton rasa rai a yayin wannan hadari.

Rahotanni sun ce da misalin karfe uku na yammacin Juma'ar ne wasu masu aiki walda da suke kokarin fasa tukunyar gas ne suka fasa wata tukunya, abin da ya janyo fashewarta da ta wasu tukunyoyi da ke kusa.

Daga nan abin ya rika fantsama zuwa cikin gidajen mutane da wadanda suke wucewa a kan ababan hawa.

Wani wanda abin ya faru a kan idonsa da ake kira Ibrahim Muhammad ya ce "tukunyar gas takwas aka kawo wajen masu waldar da za su iya mayar da su na amfanin gwan-gwan, an yanka bakwai lafiya lau babu komai cikinsu, amma ta takwas din akwai sauran sinadarai a ciki, sai aka ce kada a yanka ta a hakura.

"Bayan tafiyar shugaban wurin sai matahsin da ke aikin ya nemi ya ci gaba da yankata, yana yankata sai sinadarin cikin mai launin ruwan dorawa ya fara feshi a sama, in ji Ibrahim.

Shugaban asibitin Murtala Husaini Muhammad ya ce "Tukunyar gas din da ake fasawa domin a yi gwan-gwan da ita ce ta fashe sai sinadaren da ke cikinta suka rika fantsama mutane na shaka".

"Wadannan kuma sinadaren na da cutarwa ga lafiyar dan adam, an ta kawo mana mutane da suke shakar numfashi da kyar kuma har ya zuwa yanzu muna karbar wasunsu," in ji Dr Husaini Muhammad.

BBC
Bayanan hoto, Wasu daga cikin marasa lafiya da suka shaki iskar gas din da aka fasa sun sami sauki amma sun ki komawa gida saboda fargarba

Ya kara da cewa a halin da ake ciki sun karbi fiye da mutum 70, wadanda suka zo da wannan matsala.

Kuma ya zuwa yanzu sama da mutum 65 sun dawo hayyacinsu.

Mafi yawan wadanda aka kai asibitin sai da aka sanya musu na'urar taimakawa numfashi aka kuma ba su maganin da zai bude kirjinsu, in ji Shugaban Asibitin.

Lamarin da ya faru a Sharada 'Yan twagwaye bayan gidan rodi amma ya fara fantsama zuwa unguwanin da ke makwabtaka irinsu Sabuwar Gandu da Kwarin barka.

Ko a safiay yau Juma'a sai da aka samu fashewa a shagon sayar da gas ɗin girki a wata unguwa da ke cikin garin Kano, lamarin da ya jikkata mutum 20 da ƙona shaguna da dama.

Wannan ya faru ne makwanni bayan samun irin wannan fashewar a titin Aba na kasuwar Sabon Gari a Kano, inda mutum 9 da suka mutu baya ga wadanda suka jikkata da dama.