Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske Bala Kaura ya koma takarar gwamna, Tambuwal ya koma ta sanata?
Bayan da wasu jiga-jigan 'yan siyasa suka gaza kai bantensu a neman takarar shugaban ƙasa musamman a jam'iyyar PDP a Najeriya, yanzu haka sun koma neman wasu kujerun da ba su kai waccar daraja ba.
Cikin irin waɗannan 'yan siyasa akwai gwamnan jihar Bauchi, wanda a yanzu ya koma neman takarar kujerar da yake kai, bayan wanda ya samu takarar gwamman jihar ya janye aniyarsa.
A yanzu haka Gwamna Bala yana wa'adinsa ne na farko, kasancewar an zabe shi karo na farko a shekarar 2019.
A jihar Sokoto ma da akwai irin wannan magana, inda gwamnan jihar da ya nemi takarar shugaban kasa zai koma neman kujerar sanata.
Tambuwal zai kammala wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan Sokoto a 2023.
Alhaji Yayanuwa Sarki Zainabari shi ne jami'in watsa labarai na jam'iyar PDP jihar Bauchi ya kuma shaida wa BBC Hausa dalilin da ya sa Gwamna Bala ya koma takararsa ta gwamnan jihar Bauchi.
"Saboda shi wanda muka zaba a matsayin dan takarar gwamna Barista Kashim Ibrahim, ya ajiye wannan matsayi don kashin kansa. Hakan ya sa dole sai jam'iyya ta sake neman dan takara.
"A bayyane bai gaya mana dalilan da ya sa ya ajiye ba amma dai don kashin kansa ya ajiye takarar.
Zainabari ya kara da cewa duba da sha'anin aiki na al'umma, tun da don raɗin kansa ya ajiye bai kamata su tursasa sai ya bayyana dalilansa ba.
A baya dai rahotanni sun yi ta yawo a Najeriya cewar yarjejniya ce aka yi tsakanin Gwamna Bala da Kashim Ibrahim, cewa idan gwamnan ya yi nasara a zaben fitar da gwani na PDP na shugaban kasa, to Barista Kashim zai ci gaba da takarar gwamna.
Idan kuma bai yi nasara ba, to zai koma ya karɓi takararsa daga wajen Shatima, sai dai mai magana da yawun PDP ɗin ya ce ba haka abin yake ba.
"Dama wanda yake daga waje zai faɗi duk abin da yake so ne, amma mu mun san cewa al'ummar Bauchi da Najeriya sun nemi gwamnanmu na yau ya tafi takarar shugaban ƙasa kuma ya amsa.
"Ya tafi wannan takara ba da niyyar ya dawo ya yi gwamna ba. Amma yanzu kasancewar bai yi nasara a waccar ba, sai al'ummar jihar Bauchi da jam'iyya su suke so ya dawo ya ci gaba da takarar gwamnan nan."
Sai dai Alhaji Zainabari bai bayar da bayanin ko gwamnan shi kaɗai yake takarar ba a yanzu ko akwai wasu ƴan takarar a PDP.
"A matsayina na jami'in watsa labarai ba zan iya cewa shi kadai ba ne, amma na san al'ummar jihar Bauchi da ita kanta jam'iyya shi suke ta kira ya tsaya," in ji shi.
A jihar Sokoto ma haka lamarin ke shirin kasancewa, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai nemi takarar ɗan majalisar dattijai bayan da ya rasa ta takarar shugaban ƙasa.
Ko da yake ba faɗuwa ya yi ba, ya sanar da janyewarsa daga takarar ne jim kaɗan kafin a fara kaɗa ƙuri'a a wajen taron.
Abdullahi Yusif Hausawa shi ne mai magana da yawun jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ya ce ba sabon abu ba ne don mutum ya nemi takarar sanata bayan sauka daga gwamna.
"Har yanzu bai ce yana da buƙata ba tukunna, amma idan ya zo da buƙatar ba wani abu ba ne wanda yake nema zai iya janye masa, ba wani sabon abu ba ne kuma ba abu ne mai wahala ba, jam'iyyar PDP a Sokoto uwa ɗaya uba ɗaya ne.
"Kuma shi shugaba ne kuma mu masu biyayya ne a gare shi. Idan ya ce yana da buƙata to wanda yake nema zai janye ya ba shi."
Sai dai ya musanta cewa shiri ne aka yi wajen tsayar da ƴan takarar tun farko.