Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cutar kyandar biri ta bulla a Najeriya, ta kashe mutum daya
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce mutum daya ya mutu yayin da cutar kyandar biri ta bulla a wasu sassan kasar.
NCDC ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a karshen mako.
Shekarar 2019 ne karo na karshe da aka samu bullar cutar a Najeriya gabanin wannan lokaci.
Sanarwar da NCDC ta ce ya zuwa ranar 28 ga watan Mayu na shekarar 2022, an tabbatar da bullar cutar kyandar biri 21 a jihohi tara na kasar da kuma Abuja, babban birnin kasar.
Hukumar ta kara da cewa ta kama mutum biyar a Adamawa, mutun hudu a Lagos, mutum biyu a Bayelsa, biyu a Delta, biyu a Cross River.
Kazalika mutum biyu sun kamu da cutar a Abuja, biyu a Kano, daya a Imo da kuma mutum daya a Rivers.
NCDC ta kara da cewa mutum daya, wani maras lafiya mai shekara 40, ya mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Ta kara da cewa ta sanya ma'aikatanta cikin shirin ko-ta-kwana kuma suna aiki tukuru domin dakile cutar.
Mene ne alamun cutar kyandar biri?
Alamun farko-farko sun haɗa da masassara da ciwon kai da kumburi da ciwon baya da ciwon gaɓɓai.
Da zarar an fara zazzaɓi sai ƙuraje su feso wa mutum, su kan fara fesowa ne a fuska, daga nan sai su yaɗu a sauran sassan jiki, musamman tafin hannu da hannu da ƙafa.
Ƙurajen, waɗanda sukan yi ƙaiƙayi sosai, da sukan sauya ne mataki-mataki, har sai sun yi saɓa, sannan a warke. Amma sukan bar wa mutum tabo a jiki.
Cutar kan ɗauki tsawon kwana 14 zuwa 21 kafin ta warke.
Ta yaya ake kamuwa da ita?
Cutar ƙyandar biri na yaɗuwa ne idan wani ya yi alaƙa da mai cutar. Ƙwayar cutar kan shiga jiki ne ta fatar jiki, da wuraren shaƙar numfashi da kuma ta ido da hanci da baki.
Har yanzu ba a bayyana ta a matsayin wadda ake kamuwa da ita ta hanyar jima'i ba, amma ana iya yaɗa ta kai tsaye ta wajen jima'in.
Sannan kuma tana iya yaɗuwa idan aka yi mu'amala da dabbobi kamar su biri da ɓera da kurege, ko kuma wani abu da mai cutar ya yi amfani da su kamar kayan sakawa ko gadon kwanciya.
Mene ne maganinta?
Babu wani takamaiman magani na cutar, amma ana iya shawo kan ɓarkewarta.
Sannan an tabbatar cewa allurar riga-kafin farankama na yin aikin kare ta da kashi 85 cikin 100, kuma a wasu lokutan ana amfani da ita.