Shugaba Biden zai kai ziyarar ta'aziyyar kisan 'yan makaranta

An wallafa

A ranar Lahadin nan ne Shugaba Biden na Amurka zai kai ziyara birnin Uvalde, bayan da wani matashin dan bindiga-dadi ya shiga makarantar furamare ta Robb a makon da ya gabata ya kashe yara tara da malamai biyu.

Bayan wannan mummunan hari, shugaban ya bukaci hadin kan 'yan jam'iyyarsa ta Democrat da kuma 'yan hamayya, Republicans a kan yin dokokin da za su takaita mallakar bindiga da sauran matakan da za su kare kai hari a makarantu a nan gaba.

Ya yi kiran ne yayin da babbar kungiyar masu goyon bayan mallakar bindiga a Amurkar ke taronsu na shekara-shekara a Texas, inda ma har suka yi watsi da duk wani matki na neman tsaurara dokokin mallakar bindigar a Amurka.

Shugaba Biden na fuskantar kalubale wajen cimma matsaya ta tsaka-tsaki a birnin na Uvalde. A ka'ida dai zai je can ne domin ya gabtar da ta'aziyyarsa da jajanta wa iyayen wadanda harin ya shafa.

A matsayinsa na wanda ya rasa 'ya'ya shi ma, zai tausaya musu sosai kan wannan rashi.

Sai dai kuma wasu daga cikin iyaye da 'yan uwan da ke cikin wannan hali na jimami ba za su so su gan shi ba, ko kuma ma wani dan siyasa, saboda fargabar cewa, za a shigar da damuwa da jimamin da suke ciki, cikin babban batun siyasar da ake yi na tsaurara matakan mallakar bindiga.

Kafin ya tashi zuwa birnin na Uvalde, Mista Biden ya gaya wa wasu dalibai a Delaware cewa har yanzu ba a makara ba, za a iya raba Amurka da hare-hare.

To amma yayin da yake neman hadin kan dukkanin 'yan siyasa na jam'iyyarsa da kuma 'yan hamayya a kan yadda za a tsaurara matakn mallakar bindiga, zai ci karo da manyan 'yan Republican wadanda ke dora alhakin matsalar a kan batun tsaro a makarantu da kuma, lafiyar kwakwalwa, amma ba mallakar bindiga ba.

Saboda haka abu ne mai wuyar gaske samun hadin kai na bangarorin jam'iyyun biyu.

Sai dai kil kawai a dan dakata da batun tsawon wasu 'yan sa'o'i a birnin na Uvalde, yayin da shugaban ke ta'aziyyar mutum 21 da aka harbe, a wannan hari da ya kasance daya daga cikin mafiya muni a makaranta a tarihin Amurka.