Ku san Malaman ku tare da Sheikh Muhammad Abubakar Madu Bulamari
An haifi Malam Muhmmad Abubakar da aka fi sani da suna Madu Bulamari a kauyen Nariku a karamar hukumar Bama, ranar 1-1-1959.
Kasancewar inda aka haife shi, a kusa da Jamhuriyar Kamaru ne, wanda Kogi ne kadai ya raba su,
sai aka mika shi hannun wani shahararren malami, Goni Madu Yachammaye, amma kafin wannan lokacin sai da ya fara karatu a hannun kakanshi, da ya kai shekara bakwai zuwa takwas ne aka mika shi hannun Goni.
''Nan na yi karatu har na kai lokacin da zan kula da almajirai da jan ragamarsu, mu ne har kauyukan Banki, sai Bama da Maiduguri.
Malam Madu Bulamari ya fara ba ni gudummawa ciki har da karatun Ahlari da Ishmawi da sauransu.
Daga nan sai na kai ga munzalin fara yawo cikin kauyukan kasar Banki inda nake koyarwa, muka shiga Bama da Maiduguri,'' in ji Malamin.
Malamin farko da ya fara ba shi gudummawa a cikin Maiduguri, shi ne Sheikh Muhammad Abba Ari, malami na uku kuma shi ne Malam Madu Fakarawi, dukkansu a nan Maiduguri suke.
Wani amininsa shi ne ya ba shi wayewar hada ilimin boko da na Muhammadiyya, sun ba shi shawarar ya rubuta jarrabawar kammala makarantar Sakandare.
Allah cikin ikonsa na rubuta WAEC na samu maki mai kyau a darussan Arabiyya da Hausa da kuma Ilimin addini.
Malamin ya kara da cewa: ''Daga nan sai na tsunduma na yi karatun Difloma, da ita na yi amfani na kai ga shiga jami'a aka ajiye ni a matakin shekara ta biyu na karatun digiri.
Gab da za mu fara jarrabawa sai Allah cikin ikonsa sai wata harkar kasuwanci ta taso, shawarar magabata na bar karatun na koma kasuwanci kuma ban kara komawa karatun jami'a ba''.
Malamin ya ce ingantaccen, karatun allo da ya samu, ya yi babban tasiri gare shi, sakamakon shi ne mabudi ko wani haske mai saukakawa mutum karatun Al-Kur'ani mai girma, da sauran littafan addini.
Malamin ya ce ya fi sha'awar fannin Fiqhu, na addinin Musulunci. Mutane sun fi son karatun tafsiri, amma da zarar ka san Fiqhu, zai sanya ka fahimci ainahin Al-Kur'ani.
Abu mafi soyuwa a gare shi, shi ne yadda mahaifiyarsa ta kama hannunsa a ranar da ya sauke Al-Kur'ani mai girma, wannan rana ce mafi soyuwa a gare shi.
''Lokacin da ba ya karbo min wani abu, yana fita bam ya tashi a nan cikin Maiduguri, yana cikin wadanda suka rasu,'' in ji Malamin.
Ya ce zaman lafiya shi ne abu mafi soyuwa a gare shi, babu tashin hankali ko tsangwamar juna. Allah ya albarkaci Malamin da mata daya da kuma 'ya'ya goma sha takwas.










